NAMIJI BAYA KA'DAN
Page 1
Z aune suke a parlour cikin hiran jin dad'idan yau gidan a cikin nishad'i yake, Mahmud da yanzu ya shigo cikin miskilanci ya zauna gefen Mamin shi tare da tabe fuska yana ta huci, ya kalli khadija dake gefe rik'e da woya tana magana daga dukkan alamu da mutumin da ya kora yanzu ne take magana,Tana katse kiran ta juyo cikin zuurawa Mahmud ido da alamun tuhuma, Shima idon ya tsura mata tare da katseta cikin hade fuska yace,"Wallahi ni kunya kike bani ji irin mutanen da suke zuwa suna buga mana layi a kofar gida sai kace sun samu gidan mai, Duk gayyan taru kucen banza".
Ita kuwa harara ta watsa mai cikin bacin rai ta juya ta kalli Mami da Anty dake wurin tace." Wallahi Mami kuywa yaron nan fad'a ya fita daga idona fisa bilillahi duk Wanda yazo guna sai yai ta koransu ko ni Sa'ar sace ni wallahi ban son raini haka jiya yayiwa Sulaiman rashin mutun ci yau kuma ya kori Alhaji Bashir tome yakeso dani? .Shima fuskar ya had'e yana "Kai da Allah kiyi ta tara tsoffi bayan ba iya rik'e da gaskiya zasuyi ba ko sun aureki"
Mami ce ta kallesu cikin kosawa da hali irin nasu dan inda sabon sun saba yanzu suita Sa,insa anjima ajisu suna hira. Shiyasa ta mike tana "yes kai Mahmud meyasa kake kore mata bakinta kai wanne irin kanine wannan".
Anuty ma mi k'ewa tai tana "ke Khadija ya kikeyi har yasan da bak'in naki har ya samu damar koransu"? Baki ta tura cikin nunashi da yasa tana" Wallahi Khadija yaron nan ya cika Sa ido ne yaro kamar may.
Bata kai da rufe bakinta ba ya taso cikin fushi ya tsaya gaban ta yana nunata da yatsa har jikinsa Na bari a fili ake ganin bacin ransa murya Na rawa yace "Wallahi ina gaya miki daina cemin yaro wallahi ki kiyayeni waye yaron sai kace wata kanwar uwata kiyi tace min yaro" a fili bacin ransa ke bayyana."yes ancema yaron shekara nawa ne tsaka ninmu ko ka manta Na tunama kana dai sane Nike shiryaku lokacin da kuke zuwa primary ko" Hade fuska yayi tare da matsowa kusa da ita cikin yin kasa da murya tare da dan tsura mata ido yana mai lumshesu dayin piki dasu yace " Khadija wallahi shi namiji baya kadan ki dena cemin yaro ko Wai nayi kadan ni nasan nayi miki yawane ba kadan ba in kuwa shakku kike Na miki alk'awari gaba zaki gane.
Dariya ta danyi cikin rashin daukar kala manshi da komai tace "Wani ba Amman ba kai bakam Dan kana sane ni Aunty kace Amman Dan ka rainani sai kake cemin wani Khadija kai tsaye wallahi sai Na hadaka da Abba tukun zaka gane".Murmushi ya danyi tare da cewa " ai inna ce miki Aunty wallahi Na watsa burin raina d'en zan jawowa muradina nak'asu".Mikewa tayi tana d'an takawa a hankali hips dinta Na juyawa cikin rausayawan tace "wallahi kai Mahmud ka feye son girma".
Shi kuwa ido ya tsurawa bayan ta tare da sauke ajiyar zuciya yana mai lasan lips d'inshi da tuni sun fara bushewa cikin wata iriyar murya yace" dazu naga wata mai kama dake a bakin to titi komai naku iri daya "Juyowa tayi cikin hade fuska tace Mai kiba ko fara mai hips da yawa ko? Ido ya dan lumshe cikin daga mata gira daya yace"Ya akayi kika san haka take? " ai nasan da anga mai irin tsuffata sai ace muna kama ni wallahi ban son kibar nan" .Shima mikewa yayi ya dan tako ya matsota cikin rada yace ke wallahi mace mai kiba tayi a rayuwata ni banson mace siririya mai zanyi da ramarta mace kam ka samu ko ina ka taba bul kamar yadda kiken nan ai yafi ko? Ni Sam ban Sha'awar ramammiyiyar mace Yar duma-duma dai tafi wallahi.
Matsawa tayi cikin ranta ko mmk take yadda kanin nata Mahmud bai jin kunyar saki mata irin zantu kannan yaron da magana ma tsada take mai ko yaushe bai da abokin hira sai littata fanshi da karatu qur'an. Shi kuwa cikin sanyi yace "Bacci kike jine"? Kai ta Dan gyada mai alamar a'a, Ajiyar hrt ya sauke tare da cewa Ki hau online akwai labarin da zan baki "Karbar phone din yayi ya bude mata data cikin sanyi yace "bari Na tafi dakinmu Baby in baki labari "yana fita tana binshi a baya ya tana cewa "Waye baby kuma.
Shi dai tafiya yayi yana shakar kamshinta. Ita kuwa cewa take " ji yaro da son girma Wai nice baby lallai ma kuwa Mahmud ka isa".Shi kuwa yana zuwa dakin toilet ya fada wonka yayi ya zira rigar baccinsa sannan ya kwanta, yana mai jawo woyarshi Kaninshi Sulaiman ne ya kalleshi cikin tsokona yace."Sai chart da Aunty Khadija kuma ko wallahi Mahmud ka debo da zafi zan ga ta yadda abinga zai kasance, kai kace babbar mace kakeso ita kuma Aunty Khadija kullum cewa take ita matar manya ce saurayi ko sadaka ta yafe bare kuma kai K'anin bayan ta".dariya ya danyi cikin sanyi yace rebu da ita, ita bata San cewa namiji bayyin kad'an ko me take so wallahi ni Na yadda da kaina Na san zan isar mata nifa ba lusarin na miji bane".Shi dai Sulaiman ido kawai ya tsura mai yana mamakin yadda Allah ya jarrabi zuciyar dan uwan nashi da son Yayarta su.
Shiko cikin jin dadi ya tsurawa picture dinta na kan dap din ta ido yayi ta piki piki da idon cikin hikima ya fara yi mata magana. Salam yace da ita tare da cewa "da forko dai ki cire pic inki Na kan dap din ki in ba so kike muyi fadaba". Itako wanga ta tura mai tare da cewa "Nifa Aunty kace sai ka rinka abu kamar Kaine babba harda ko mu bata to mu bata din mana "dariya yayi tare da cewa "ai ina sonki baby bazan iya batawa da keba"Yes tace dashi shi kuwa cikin kuzari da kaifin basira irin nasu Na maza yace."Kinsan Ku mata kala kala ne kuna nan tamkar lemun zaki".cikin dariya da daukar abin as A shi haka yake mai son raha ne tace "to yaro ya muke? Cikin jin zafin Kalmar da take cemai Wai yaro ya dago woyar ya kirata Itako tana gani ta daga dan tasan ta cinnashi bai son tace mai yaro.
Yana dagawa sai jinshi tayi cikin sanyi ya busa mata iska a kunne tare da jan numfashi yace." Dan Allah ki daina cemin yaro ni wallahi har ga Allah kina kona min rai tunda nasan ni ba yaro bane "Tabe fuska tayi tace " yes me labarin da zaka gaya min? Jin haka ya sashi kara narkewa jikin pillows a ranshi yakeji inama ace a jikinta yake ace gashi gata wallahi da sai ya tabbata mata da cewa namiji baya karanta fili kuwa cewa yayi" ko kinsan Ku mata tamkar lemun kuke Wani lemun zaki ganshi baba a man cikinsa ba komai sai dusa wani kuma ki ganshi karami Amman cikinsa sai ruwa sai dai kuma sai a samu ruwan ba zaki wani kuma ki ganshi gashi a cike ga ken fata Amman ba ruwa bare zakin Wani kuma zaki ganshi ga kyauwun jiki ga ruwa ga zaki ga dan dano ga kauda kishi da k'ara lafiya da Sa kuzari".
Sai kuma yayi shiru ita kuma tunda ya fara mgnar ta tafi tunanin yes haka nefa wallahi maganar sa gaskiya ce a ranta take cewa wato su maza mu sannan masu ilimin fikkiwu komai Na mata sun sanshi.
Maganarsa ce ta katseta cikin kasala yace."Toh ke irin wannan lemunne Na karshe da na kwatan ta miki" cikin jin zafin furucin nashi tace "In kana hasa shenka ka daina sani a ciki yaro Sam baka da kunya".Murya a dakile kamar zai kuka yace "Dan Allah ki dena cemin yaro wallahi zakisa duk randa Na iso gareki Na zalum ceki dan kawar da wannan sunan"Ita dai bata gane me ya fadiba bare ta gane ma,anar zancen. Cikin sanyi dan ta fara jin bacci tace"Mahmud zanyi bacci" Ajiyar zuciya ya sauke jin dad'i yadda ta kirashi cikin sanyi yace Toh tashi kike kiyi alwala kizo muyi Addu'ar konciya bacci".Cikin bacci baccin "tace ai nayi ni tun dazu "Cikin rashin sanin zancen zai fito yace "ai nasan kinyi Amman dai alwalan ya warware yanzu kam.
Ita kuwa cikin baccin da kosawa da surtunshi tace " Yauwa dama gobe ina so ka kani Geere" Tes yace tare da cewa ni bari Na sake alwala sai da safe ko "To tace tare da katsa kiran. Shi kuma Mahmud kogin tunani ya fada yana kitsima yadda zai kasance shine miji kuma shugaba a gun Aunty Khadijan tasu A fili yake cewa bana jin tsoron komai sai k'iyeyta daga gareta Idanshi ya lumshe yana tuni surarta shi dai yasan ba matar da zata iya dashi sai itan itanma yana tausaya mata in ta iso gareshi. A haka bacci yayi awon gaba dashi yana mai muradin malla karta...?
Page 2
Wannan shafi nakune Jannart lamido, Zahra Muhammad Mahmud, Nana Diso, Rufaida Yusuf Fati Azlad Anty khadjia Aisha mazoji Sadnaf Halima Auwal sis Ummi Garkuwa, Suwaye Khadija da Mahmud? Alhaji Ibrahim da Alhaji Sani yan uwan junane uwa daya uba daya sai k'anwarsu mace Zahra, Yan Asalin Fulanin Adamawa Yola suna cikin Yola sulum, Alhali Ibrahim shine babba matansa 2 uwar gida mama yayanta 3 Sani sai Usman sai Autarsu Khadija sai Anty Zee mai yara biyu Fadil da Fadila.
Sai Alh Sani shima matansa 2 Uwar gida Mami yaran ta 4 Auwal shine babba sai Rayhana sai Fatima sannan Mahmoud sai autanta Amira sai Aunty Amarya wace take kanwa ga uwar gidan Allahji Ibrahim yaranta 4 Aysha itace baba sai Sulaiman sai Ibrahim takwaran bappanshi kenan sannan Autarta Nabila, Ita Khadija tun sanda Alhaji Sani ya auro Anty kanwar matar yayanshi sai suka dauko Khadija so ita Khadija gidan bappanta take k'anin mahaifinta sannan gaban ummarta kanwar mahaifi yarta. Sai Goggo Zahra yaran ta biyu babban danta Ahmad sai kanwarsa Maryam.
So Khadija da Rayhana da Fatima da Aysha kusan tare sukayi karatu sai dai Dan fifiko da yake tsaka ninsu kadan, Shakuwa ce sosai tsakanin yaran sannan iyayensu kuwa zaman lafiya ne mai tarin yawa a tsaka ninsu. Mahmoud da Khadija sunyi wani shakuwa na daban wanda ake ganin sabo ne kawai da shakuwa irin na yan uwan taka duk da Khadija ta girmi Mahmoud dan ko a maka ranta Khadija da Fatima da Aysha suna SS 3 yayin da shi kuwa Mahmoud yake jss 3 Rayhana ko a lkcin ta gama har tayi Aure tana cigaba a gidanta ya Auwal ko ya Dade da hade digiri dinshi har ya fara aikinshi sannan yayi Aurenshi.
Mahmoud da Khadija sabone mai tarin yawa a tsaka ninsu wanda ake ganin kawai iskarsu ce tazo daya dan Mahmoud shi ba mai yawan mgn bane sannan yana da halin ko in kula zai ganka sau goma Amman bazai sheida kamannin kaba ko yaushe kanshi a kasa, bai da yawan surutu sai in da Khadija ne zakajishi hira harda dry sam baison raini sannan yana da son girma over sam bai lamunci raini ba ita kuwa Khadija ta kasance ta kowace duk taron da suke a family din su muddin bata nan basa jin abin yayi armashi ita kowa nata ne tana da faram-faram da Jama'a ta kasance so popular.
Khadija farace tas mai direrren jiki tana da sura ta ban Sha,awa da tafi ya da hankali duk wani da namiji lafiyye sannan tana da korjini ga cikar haiba komai na jikinta das kullum ka ganta sai kayi zaton yar 18 ce ga tsafta da kula da kai Khadija dai kekkyewa ce ta ajin forko kuma haka Allah yayi ta da farin jini bata fita nan da nan ba tare da wani ya biyota ba.
Shi kuwa Mahmoud Yaro ne mai kwalisa da son girma yana da cikar zati da haiba yana yin shi yasa ko manyan mutanen ke bashi girma dan tako ina ya kasance mai haiba farine tas shima yana da tsawo dan duk yafi yayunshi matan tsawo sannan yana da fad'in girji gashi mutunne shi mai halittar gashi a jikinsa hatta hannu shi da sharaban kafafunshi suna cike da gashi maitaushi da sheki yana konce luf a jikinsa gashin giransa ko irin Na Khadija sak wanda har ya kusa hadewa hancishi zata har baki girjinshi ma rufe yake luf da suma so halittarsa takan sawa yana jin kanshi yes shifa namiji ne Haka kuwa Allah ya jarabci zuciyarsa da son Khadija shi tun yana yaro ya gane yana sonta so kuma na Aure bawai so Na yan uwan taka ba, Domain ko lokacin da zai kasance ya gama balaga da mafarkin Khadija balagarsa ta zauna gareshi.
Yayinda ita kuwa Khadija take mai so irin Na yan uwanta ka takuma daukeshi abokin shawara, Masu karatu zakiyi mmk ko wasu Suji takaici innace muku Khadija bazawara ce. Amman a suna take bazawara a zahiri da badiri budur wace, Domain Aurenta Na fari a deren da aka kaita Gidan Angonta Sulaiman mahaifiyarshi tace bata yace koda d'akin ya shi gaba kuma tace muddin bai saketaba zata tsine mai dole a Daren ya saketa abinda ya kona ran yan kuwa yayinda shiko yake ganin rebonshi ke bibiyarta, lokaci daya kuma Alhaji bashir ya fito shi kam Mahmoud baiji komai ba sai Aurenta yaji yayi kukan takaici da bakin ciki ba iyaka a lokacin yawa kanshi kukan takaici da kunci Khadija da Alhaji Bashir sun zauna zaman shekara 3 Amman ba wani Abu da ya taba giftawa tsaka ninsu a dalilin matan shi da suka shuka mai tsiya dan kishi duk ran girkinta dashi da mace basu da banbanci, Shi da kanshi yana tausaya mata yakuwa yi yunkurin sakinta tun tuni ita kuwa tace zata iya zama dashi a haka Dan inya sake ta bata San me mutanen zasu ce da itaba Shi da kanshi yaga dai yana cutar da ita dole ya saketa, Bayan shi ta kuma Aure da Adam Wanda ko tarewa basuyi ba ya saketa so daga nan tace ita ta hak'ura da Aure.
Kuma duk yan uwa ba wanda yasan cewa Khadija Na tare da budur cinta sai ita sai Mahaliccinta.Yayinda shiko yake sonta a matsayin bazawarar shi kam Mahmud ya sa aranshi Khadija matarsa ce rebonsa ke juyawa da ita zata dawo kanshi ya kuma yiwa kanshi alkawari a yan kwana kinsan zai Aureta ya tabbata tarwa kanshi shi zai iya rik'eta, Wannan kenan! Kashe gari da safe yana tashi ya shirya tsaf cikin riga da wondo na galila kalar pink ya amshesa ras ya fito cikin kuriciyarsa da zafin jini sai kamshi yake zubawa, 11 dai-dai ya Sakai cikin dakin Anty ita kuwa dai-dai lokacin tana tsaye gaban mirror atampa ce a jikinta riga da siket siket din ya zauna ras a jikinta kugunta ya fito fes a cikin hips dinta kamar sunyi magana ga rigar itama ta wani lafe a jikinta gashinta take ta kiciniyar tubkewa, Cikin bugawar zuciya da tsinkewar jini ya matsota a ranshi yake cewa "Wayyo zata karya min Azumi"
Matsota yayi yasa hannu ya karbi ribbon din cikin kamo gashin yana mai tsurawa kirjinta ido ta jikin madubin ita kuwa kara matsoshi tai da nufin ya tufke matan, cikin rashin Sani hips dinta ya gogi jikinsa, Cikin wani irin daukewar numfashi ya......?
page 3
Janye jikinshi yayi da sauri ya juya ya fito parlor ya zauna kan 1 Nabila dake gefenshi ta kalleshi cikin doki tace Ya Mahmoud nima zanje gidan ya Auwal ko Kai ya gyada mata dan in yace zai magana muryarshi rawa zatakeyi ita kuwa tana gamawa ta fito sai k'amshi take Cikin harara tace"Yau kuma su Mahmoud dinne a kusa ba magana sai tsune ido da kauda kai".Shi dai bayyi magana ba sai mikewa yayi ya fita ita ko hannun Nabila taja suka fito d'akin Mami suka shiga bayan sun gaisa tace "Mami bari muje gidan ya Auwal dan jiya ya kirani yace inje akwai maganar da zamuyi dashi.
Cikin kula tace "yes ki gaishesu Amman ki dawo da wuri" yes ta amsa tare da fita ta yafa kyalenta a kafada sannan ta kama hannun Nabila Suka fita a cikin matar ta sameshi zaune ya kife kanshi kan sister ga gate an bude mai Cikin tsokana ta ajiye Nabila a baya sannan ta bude gaba ta shiga cikin tabe baki tace"Yanzu karfe 11:20 Am shine har azumi ya fara juya ma kai gaskiya Mahmoud akwai ka da ragwanta" Cikin sanyi ya dago kanshi yayi motar key sannan ya harba cikin sanyi ga sanyi Air conditions ga kamshi turarukan jikinsu Har saida suka hau babban titin da zai sadasu da jimeta sannan ta kuma kallonshi tace." nifa ba dole in zuwanne baka so"Juyowa yayi ya tsura mata ido dai-dai lokacin da ya karya kona ya hau kan titin hayin gada Momy sosai tayi ganin fararen inda nunshi sunyi jazir sun kuma kankance cikin kula tace"Brother ko dai baka da lafiya ne"? Kai ya jinjina da ker ya bude baki yace " ahhahh lafiya ta lau kawai haka Na tsinci kaina" ido ta tsura mai cikin mmkin jin yadda voice nashi ke fita gashi yaki ya kuma magana sai. Ita shirun tayi har suka gaggara kasan gadan sannan, yace "Khadija me zakiyi a gidan ya Auwal naga satincan ma kinje" nima ban saniba ya dai ce naje".
Yace sannan yaci gaba da tafiya, 12 dai-dai suka isa cikin jere suna isa aka bude musu gate suka shiga yana tsayuwa Nabila ta bude mota ta fita a guje tayi cikin gida. Itama Khadija hannu tasa zata bude sai kuma taji ya rufe motar, Cikin tabbaya ta juyo sai kuma tayi sauri kauda kanta ganin shima gaba daya ya juyo ya sata a gaba ya tsura mata ido, Bata kulashi ba dan tasan fitina yake ji yanzu zai tsareta da wa, azi Cikin sanyi kamar mai rada taji yace "Khadija" Sai kuma ya danyi shiru sai ido da ya kafeta dasu cikin dan dakilewar voice yaci gaba da cewa" Na rasa yadda zan fahimtar dake illar irin wannan shiga da kike yi ke baki san irin fitina da kike hada sawa ba nace miki ki dena Sa gele amman bakya jin magana ta "ya karisa magana cikin sigar fada da isa, Ita kuwa dan sunkuyowa tayi ta dannan pin din da ya rufe kofar aiko ta kifa kirjinta kan cinyarsa, shi kam gaba daya jikinsa ya rinka sakewa yana macewa jikin sit ya koma ya jingina ya lumshe idanshi cikin fizgar numfashi.
Ita kuma tana budewa ta fita kai tsaye tayi cikin gida shiko hips dinta yabi da ido harda baki yana mai jin tsoron abinda zai mishi katanka da ita gaba daya yaji jikinshi ya mace bazai iya tukin ba. Ita kuwa tana shiga Anty Salma ta fito suka zauna a parlon sai hira suke dan Salma mace mai son Jama, a bayan sun gaisa ta kalleta cikin fara, a tace "ke Khadija ina Mahmoud din bazai shigo bane"?
Cikin mmk tace "kai Anty ya akayi kika san shi ya kamo mu" Dariya tayi tace " ai nasan Mahmoud din ke kawoki "dariya tayi sannan sukayi ta hiransu. Suna cikin hiran ya Auwal ya fito parlon shi cikin fara,a ya amsa gaisuwar ta sannan yace "dama akwai wani abokina Nasir shine ya ganki kuma ya nace yana son Ku hadu so tun last week kullum sai yazo yau dai nave bari in hadaku, ki isa yana parlor na"Rau rau tayi da ido lokaci daya kuma sai hawaye cikin sanyi tace "ya Auwal Aure kuma? Ya Auwal me Na samu a auren bare nayi sha'awar sakewa wallahi ni tsoron maza nakeji samida kowa da bak'in niyanshi a ranshi"
tana maganar ne da iya gaskiyarta lokaci daya fuska ta ta sauya, Shi kuwa Mahmoud sai yanzu ya dan dai-dai ta nitsuwarshi sannan ya samu ya fito ya shiga cikin gidan cikin salam ya shiga, Cikin mamaki ya rinka binsu da ido a ranshi kuwa cewa yake daga zuwa sai kuma a sata kuka, a fili kuwa gefenta yaje ya zauna cikin sanyi yace," Khadika me ya faru? me aka miki? Me ya same ki?" Haka ya jera mata tambbayoyin tun kafin ya gaisa da mutan gidan.
dariya Anty Salma tayi cikin wasa tace "ka tambaya kam Mahmoud ashe Aure Na zama abin tsoro ga dan Adam ji yadda take zubda kollah Dan ance ana sonta".Wani dum durum yaji a ransa a take ya hade fuska cikin had'e rai yace " shike nan bazan kubar yarinya ta hutaba aurena tunda anyi daya ba Sa'a an kuma Na biyu ba canji an kuma Na uku kazalika sai k'unci ase bai isa a barta ba sannan wayema mai cewa yana sonta dan naci da mayta ai naga sai a barta ta huta ko"?
Ido kawai ya Auwal da Salma suka zuba mai abin har tsoro ya bawa Ya Auwal din dan ganin kishi karara a fuskar kanin nashi. Ita kuwa cikin jin dadi zancen tace ni kamma ba Aure zanyi ba. Ganin zasu raina mai wayyo yasa cikin hade fuska ya ce "Ke tashi kike yana parlor na jiranki, ji yarinya da shirme ke a zatonki barinki zamuyi ki zauna ba Aure "Mike tayi cikin sanyi ta nufi parlon nashi, Shi kuwa Mahmoud tukuru ya rink'a fad'a kamar shine baba kan Auwal din, Abin ya basu mmk ganin haka yasa yace"Kai Mahmud ko dai sonta kake ne.
Cikin wata iriyar murya yace" yez sonta nake ya Auwal kuma sonta da Aure nake ni zan Aureta wlh itace burin raina".Cikin mmk Auwal ya bishi da ido itako Salma ba mmk a fuskar ta dan ta dade da gane Mahmoud son Khadija yake. Cikin hade fuska ya kalleshi yace lallai baka da hankali Mahmoud na yarda yarinta ke cika inaba hakaba ina kai ina Aure Wai shin yaushema ka gama rik'a "Mikewa yayi cikin murtuke fuska Wai shi sai aitacemai yarinta yarinta Fuska a hade yace "Wallahi ni dai nasan ni ba yaro bane kuma nasan zan iya rike ko mata 4 zan kuma iya wodatar musu sannan da kuke cewa yarinta Ina dai Amira kanwar tace Shekara nawa nake bata.
Kuma ina yanzu saura 9 days Aurenta wato ita ba yirinya bace saini? A harzuke yace,"can matsa daga nan ita mace kai namiji". Mikewa yayi yana " sai kuma akace namiji bai da rai ko ba zuciya ne daniba "Ganin fadan zai nisa yasa ya matsoshi cikin dariya yace "Haba Mahmoud ka bari ko digiri dinka ka hada mana tukunyanzu kai kama san yadda zaka iya kula da mace ne"?dariya yayi ta irin kumma rainani Cikin ko in kula yace." tsaf zan iya kula da ita har nai mata ciki ta Haihu "yes mgnar fa ta girmama ganin haka Auwal ya bishi da ido shiko Phone dinshi ya zaro ya kirata tana dagawa yace Khadija ki fito mu tafi ina da abin yi".fita yayi batare daya sallah mesu ba, Ita kuwa tana samun haka ta dan juyo ta kalleshi cikin sanyi tace "Kai hakura zamu tafi Mahmoud na jirana kuma Azumi yakeyi".ajiyar zuciya ya sauke tare da jin dadi voice nata yace. "Ba matsala gimbiya sai kuma nazo gida ko" Yes kawai tace ta mike ta fita shima binta yayi suka fito tare shi sai ya tsaya tare da Auwal ita kuma hannun Nabila takama suka yi musu sallah ma suka fita. Suna shiga mota ya figi motar a guje suna fita ya juyo cikin hade fuska yace."Kina sonshi ne? Tabe fuska tayi cikin gyatsine tace " me zanyi dashi ina zan kaishi ai ni ko aurenma zanyi ba irin shi zan Auraba dan yamin kankanta yamin kadan nifa nafisin namiji mai haiba? Shiru yayi bai sake magana ba Dan ji yake kamar da ganggan take gaya mai kuma dashi take.
Ita kuwa ta dage sai cewa take yara kanana dason tara mata yanafa da mata yake son kara Aure ina zai kaimu ".Ba tare daya kalleta ba yace" Wallahi ki dena raina namiji ni Na tabbata duk kankantar namiji zai dai cika miki mararki" Cikin tsoro da kunyar maganarsa ita har ga Allah ba haka take nufiba shi kuma Daga nan bai kuma magana ba dan ya mata daya tamkar da 1000 suna isa gida dakinshi ya shige yana ta nemawa kanshi mafita tun kafin aimai shigar sauri.
Ita ma Azumin take 5 dai-dai ta shiga kitchen ta hada musu abin buda baki kamar kullum, Bai shigo ba sai da akayi sallah sannan ya shigo a parlon Anty suka zauna, Fruit salad ta samai a Cup ta mika mai tana "Gashi kaci Sa'a na regema wallahi da shanyewa zanyi, shi kuwa Ido ya dan tsura mata tare da cewa "ai duk daya ne inma kin shanye ni kikewa tanadi gaba, Cikin rashin gane maganar da ya nade mata tace "ai yayi dadi ne shiyasa bazan hanaka ba "Wani irin kallo ya bita dashi A ranshi yace Na tabbata kinfi haka dadi A zahiri kuwa cewa yayi" Nagode baby "Jin haka yasa ta hade fuska ta bude baki da nufin cewa yaro Shiko gane Abinda take son fada yasa cikin sauri ya had'e bakinta da....?
0 Comments