NAMIJI BAYA KADAN
Page 28
Cikin mamaki Anty tace."Wanne asibitin kuke?".Cikin tsura mata ido yace."Boshong clinic zamu je".Toh tace cikin mikewa tare da cewa ." yanzu Sulaiman zai kawoni".Katse kiran yayi tare da jawota jikinshi ya dan shafa fuskar ta yayin da yake murza sitiranta da hannu daya, Ita kam gaba daya tayi nukui sai manna kanta tayi a jikinshi har suka isa.
Suna isa aka tarbesu cikin kulawa yayin da suna shiga sanyin Air Condition dake ratsa Asibitin ya kara mata sanyin da take ji kai tsaye office din doctor suka shiga nan take aka fara dubata tare da daura mata ruwa dan kuzarin ta yayi k'asa sosai, Shi kam Mahmoud yana nanike da ita Dr sai binsu da ido yake yana murmushi dan suna burgeshi.
Bayan an gama binciken komai aka gano d'an kara min ciki dake makale a marar ta cikin happy Dr yazo ya mika Mahmoud hannu tare da cemai."Congrat matar ka na dauke da cikin wata daya da sati 2 kuma cikin Yana cikin koshin lafiya ba wani matsala itama da zaran cikin ya cika 4 Mornt dai komai zai normal" Ita kam Khadija da bacci ya fara dibarta cikin bacci taji kalaman likitan. Ido ta zaro woje gami da sa hannu kan cikin ta tana shafawa lokacin daya kuma sai hawaye shur-shur a ido mgn take sonyi amman ta kasa sai bakin ta dake rawa.
Shi kuwa Mahmoud wani irin farin ciki ne da bai taba jiba ya ziyar ci zuciyar shi gaba daya ya cika da annuri murmushi yake kamar zai hadiye lips enshi ruggume dr yayi sannan cikin murya ya kuma zame kasa yayi sujjada ga mahaliccin mu hamdala ya rinkayi muryar shi har yana rawa. A haka ya tashi ya zauna bakin gadon tare da jawota jikinshi ya ruggume ta yana sauke ajiyar zuciya (kamar dan da ya gane uwar sa bayan ta bace mai).
Hannushi ya tura cikin rigarta a hankali ya kife tafin hannushi kan mararta sai kuma ya murza hannun zuwa kan cikin ta yana mai mgn cikin jin dad'i da kamar rada yace."Baby kin gama min komai me zance dake Allah ya bani komai ta sana dinki Baby na kusa na samu aboki, na godewa Allah da ya bani ke ya kuma azar tamu da samun zuriya".
Magan ganunsa suka kara tuna mata wai cikin Mahmoud ne a jikinta sai kawai ta saki kuka tana mai tureshi daga jikin ta wani irin kunya ya rufeta shike nan yanzu ta tabbata matar Mahmoud harda cikin shi a jikinta sannan kowa ya ganta yasan abinda Mahmoud ya mata kafin ta samu cikin ace kanin ta wai yau shine mijin ta kuma harda cikin shi a jikinta. Sai kawai ta kife kanta kan pillow ta saki kuka mai cin rai. Shi kuwa hankali a tashe ya hau kan gadon ya tallabo kanta tare da jawota jikinshi ya ruggume ta murya a raunane yace. Baby cikin kikewa kuka bakya sona shine har ciki nama bakya sonshi wannan fa shi baida laifi kiyayyar ki ta tsaya kaina kar ta shafi abinda ke jikinki, Allah ya mana kyauta ke kuma ki butul ce harda kukan ki toh yanzu gaya min me kike so".
Cikin kukan ta matsa tare da zubda kollah tace."Dan Allah kayi hakuri kar ka gayawa kowa please Na tuba kasa ya zubar min da cikin ni banson haihuwa wallahi ni dai a zubar da cikin tun ba wanda ya sani ma.
Ido ya zare a tsorice a hankali ya kuma jawota jikinshi cikin lallashi ya hada bakinshi da nata kissing dinta yayi da kyau sannan ya tsare ta da ido murya a raunane yace." Kin san sanda cikin ya shiga ne.
kinsan me zaki haifa ne? kinsan rayuwar da zaiyi? Ko kyau tar da rabbi ya mana kika raina ki nitsu Khadija cikina fa kike cewa wai ince a zubar ciki na nefa dana nefa kinsan wahalar dana sha kafin na sameshi a ranar muka samu cikin kin manta a sume na wuni a wannan ranar dan nanefa na halal kike cewa a zubar me zaki gayawa mahalliccin mu.
Ita dai kauda kai tayi tare da cewa."Bana so wallahi ko zan Haihu ba da kai ba kam na haihu da kai nace kanina ne mijina ko nace kaninah ne uban yarana".Sosai zantu kanta suka bata mai rai cikin tsura mata ido ya nunata da yatsa jikin shi har rawa yake yana fidda numfashi da karfi yace." Ina binki ne ina lallaba kine dan ke macece kuma macce mai rauni ce da tawayan tunani Ku mata akan biku a hankali dan a fahimtar daku amman na lura abin naki rainine, dan haka ya zama dole na gyara miki tunanin ki, kiji da bakina wallahi kar bakin ki ya kuma furta Kalmar zubda cika in kuwa kikayi gagganci furtawa wallahi zaki gane kuren ki, cikina dai yana jikin ki wallahi ko kallon banza kikayi wa cikina zaki gane kuren ki wallahi kar ki kureni zan miki abin da bakya zato" .Baki ta tura da kame jikin ta dan ganin yadda yake bala, i kamar zai doketa har jikin shi na rawa har cikin ranta taji tsoron shi ya rufeta cikin sanyi ta bud'e baki a hankali tace."Dan Allah kayi hakuri a zubar da wannan in yaso gaba".
Bakinta tarufe tare da rumtse ido tasa hannu ta tare fuskar ta jin wani tsawa daya watsa mata ga hannushi da ya daga zai yarfa mata mari cikin rawan baki tace." wayyo Allah na wayyo Anty na".Dai-dai lokacin kuma Anty da Sulaiman da Anty Ray da suka hadu da ita a kofar gida suka taho tare, suka shiga ga ninsu yasa ya sauke hannushi. Suna shiga suka tsaya kanta suna mata sannu cikin kula Anty ta kalleshi a hankali tace."wai meke damun ta?.
Da sauri ta kalleshi cikin yanayin dan Allah kar ka fada sannan ta juya gun Anty a hankali tace." a a fa kawai murace yanzu ma tare zamu koma in ruwan nan ya kare".
Ita dai Anty shi take sauraron ganin haka yasa yace." Anty ciki ne take dashi Amman ba wani matsala".Cikin mamaki Anty Ray da su Anty suka zuba mata ido ikon Allah ciki Allah mai iko. Ita kam sake kifa kai tayi cikin kunya da takaici sai kuka ta saki cikin sanyi, bata sake dago kanta ba har ruwan ya kare Dr yazo ya cire aka sallah mesu suka koma.
Suna komawa Rayhana ta shiga gun Mamin su cikin farin ciki da dariya ta kalli Mamin dake konce gefen ta tace." kai Mami gaskiya Mahmoud dinki sai Allah wallahi kinga gwara da akayi mishi Auren nan yanzu da ba, ayiba ta ina cikin nan zai zo, gashi tun basu tareba sai ciki wallahi Abba yayi tunani dan ya toshe hanyar barna da ya yarda yamishi auren".Cikin mmki Mamin ta mike zaune tana kallon yar tata tace ."Ke wai tsaya mana waye mai cikin?".dariya tayi cikin sanyi tace ." Mami matar Mahmoudu kinda ke da ciki".
A kufule tace."Wacce daya a cikin su?".Ido ta tsura mata ganin yadda ta sauya a hankali tace."Khadija ce, Amman Mami ya naga kamar abin bakin ciki na gaya miki?".Aiko Mami kam a take sai zufa da rawan jiki cikin bala,i tace." Toh dama wanne bakin cikin ne ya wuce wannan da Abida ne da cikin ai nanne abin farin ciki tab lallai wato ita har ta samu gun haihuwa tun yanzu har ta rarumi ciki wallahi wannan cikin kam badai ta haife shi ba, Sai na bada cikin ai bazata ma sabu ba.
Ita kam Rayhana dafe kirki tayi tana kallon uwar tasu cikin tsoro da ker ta bude baki da nufin yi mata nasiha aiko tai kanta da bala, i harda cewa ta bace bata maza ta tafi gidan ta mgnar ba tata bace.
Haka ta tafi tana mai jin tsoron uwar tasu daga baya ta kira kaninta ta shaida mai kudurin mahaifi yarsun. Shi kam Mahmoud abu ya hade mai tunda itama mai abin bata sonshi sannan ga Mamin shi ma bata son cikin ga fiti nan Abida tunda taji Khadija nada ciki take mita ai ita kam tunda yana sonta gashi har ta samu ciki watoh ita kuma ko oho haka yasa take nace mai tai tace mai itama cikin take so. Haka Abu yayi ta juyawa Khadija dai ya sa mata takun kumi ya kuma hanata ko motsi mai karfi Mami kuma ba wanda yasan shirin ta sai Allah sai Abida da Adda Asabe.
Yauma kamar kullum da safe Mahmoud ne konce yana baccin gajiyar da Abida ta tara mai, cikin baccin yaji ta ta konta bayan shi a hankali tasa hannu ta shafa fuskar shi cikin rada tace."Hamma ka tashi Baby nake so".Mika yayi tare da juyowa gareta cikin baccin ya jawota jikinshi a hankali yace." ke bakya gajiya ne shifa cikin nan ba zafin nema ke kamo samu ba kiyi ta Addu'a zaki samu kinji ko".Makaleshi ta kuma cikin kirsa tace."Ko ban samu baby ba ni dai na isarwa mijina na kawar mai da buka tarsa".
Kara janta jikinshi yayi cikin ranshi yake cewa." inama Khadija ce mai jarum tar nan da yaji dad'in rayuwa amman sai saba nin haka ita wannan ko zai shekara gareta baijin gamsuwa sai dai kawai yana rege zafi, yayin da ita kuma Khadija cikin dare daya take kanwar mai da duk wani kishin sa ga ciki ammam ita bata so, mai son kuma bata samu ba, ita kuwa Abida ako da yaushe hamdalah take da Allah ya bata gwaranzon namiji.
A haka ya jawota suka shigewa juna shima rashin Khadija yasa dole ya saduda da ita, da ker suka sahirta wa juna sannan ya shirya ya nufi gida.Yana na shiga gidan Khadija na jinshi ta koma cikin daki ta konta ta hade fuska, Anty dake lura da rashin kula da take nunawa mijin nata cekin juya kai ta zauna gefen ta cikin fada da nasiha tace."
Khadija anya kinsan me kikayi kuwa shin kinsan cewa shi namiji tamkar yaro yake yadda ka horeshi a haka zai tafi shifa namiji dan son a nuna mai kula ne yanzu ke kinga gudun shi da kike alherine a gareki, wallahi duk sonki da yake kina dab da rasa zuciya sa dan waccar yarin yar ta gama gane logon sa ta kuma bishi a yadda Allah ya halicce shi domin ko dole ne ga duk wata ya mace taga tayi iya yinta ta samarwa mijinta gamsuwa Khadija ki kula ki gyara tun kafin lokaci ya kure miki, sam bakya bawa mijinki kula sai raki da mita da kike nuna mishi dole yana sonki zaiyi nesa dake tunda bakya bashi kulan da yake bukata daga gareki kinga ko dole yaje inda za, a kula dashi".Haka tai ta mata fada da nasiha ita kuwa sai shiru tayi tana rufe da ido jin yayi sallamah a parlon ta fice ta tafi dakin ta ita kuma Khadijan dama a d'akin su ita da Nabila take.
Bayan sun gaida da Antynne tace." ka isa tana dakin su". Toh yace tare da wucewa cikin d'akin a hankali ya taka har zuwa.........
Page 29
hankalinsa kwance ya kutsa cikin dakin kwance ya hangeta kan 3 siter kanta asama idonta alumshe fuskar ta tayi fayau lip dinta ya kara ja a nutsu ya kalli kirjinta ya cicciko sosai ajiyar zuciya ya sauke hade da lasar lips cikin zuciyarsa ya furta "ina sonki khadeeja!" cikin takun isa da kai ya tunkareta jin tafiya da shakar kamshin datake matukar so yasa ta mike zumbur tana kallonsa tafiyar da yakeyi ce ta kara kular da ita yaro karami yaita abin manya taja dan karamin tsaki ta kauda kai murmushi yai ya zauna kan kujerar hade da janyota jikinsa lumshe ido tayi tana shakar kamshin jikinsa hannunsa yasa a hankl yana shafar gashin kanta zuciyar shi fess khadeeja na dauke da cikinsa lumshe idon yai shima cikin kuzari yasa hannunsa yana shafar cikin yana jin tsananin sonsa cikin kasalalliyar murya ya furta "babyna hop kina kular min da kanki da kuma babyna na jikinki?" haushi kalamansa suka bata tayi shiru dan batasan kalan amsar da zata bashi ba tarasa yarda da wannan lamarin ita ce wai Khadeeja dauke da cikin kaninta Mahmoud takaici taji ta ko ina kamar zatayi me ta cije muryar ta na rawa ranta abace musamman jin hannunsa datayi yana shafar cikinta shafa ta lallashi da kiyayewashi.
Kufele ta so yin magana da kyar ta daure ta saita kanta cikin wahalalliyar murya ta takaici tace "Mahmoud please bana son cikin nan azubar dashi in yaso gaba sai.
Cikin wata razananniyar tsawa ya tunkudeta jikinsa ya mik'e idonsa ya firfito"enough khadeeja!" yana huci makar wanda yai dambe da zaki ya kara zare mata manyan idanuwansa da bacin rai yasa suka fara rinewa yazama jaja"abinna ki yayi yawa kiyayyar ta kai ki kyamaci dana? wanda yake jikinki meyasa bazaki gane bane kin san haka zata faru.
Idan aka zubar kina da tabbacin sake samun wani? ke kika bawa kanki shi ya isa! ya isa! bazan yarda da wannan tsarinba wallahi! wallahi! zan iya jure komai banda taba cikin jikinki! "takaicine yasashi kakarewa bai karasa maganar ba illa yarfe hannuwa daya dinka takaici yasa ya kaiwa kujera naushi itakam tunda ya fara fadan taga ya juye mata kamar bashiba ilahirin jikinta kyarma yake kanta akasa tana zubda kwalla gefe guda na ranta kuwa suya yake kaninta na surfa mata fada irin wannan kamar wani ubanta daya gefen kuma cike yake da matukar tsoranshi dan batayi tunanin Mahmoud na rikidewa ya koma haka ba tsura mata ido yai zuciyar a kuntace lallai Khadeeja bata kaunarsa tunda har bata son cikinsa wanda yake jikinta gabansa ya fadi ya lumshe ido harga Allah yana sonta amma baya jin zai jure wannan yanayin yaushe zata soshi har taso dansa dayake jikinta.
Yana girgiza kai yai mata magana a hasale" kina jina! "kai ta daga a tsorace"naga take takenki akan cikin nan yau zuwa gobe zaki tare a gidana ni zan kula da abina inyaso duk randa kika saukemin shi ki kama gabanki! sannan ki sani bake kadai bace mace da zan zauna kina min sakarcin da kika ga dama!"ya fice hawayen daya makale ya gangaro mata ta fashe da kukan maganarsa wai zata tare a gidansa itakam taga ta kanta daga wannan sai wannan abu iri iri zuciyar taki tahuta.yana fita bangaren Abba yayi zuciyarsa a hasale lallai rainin khadeeja yai yawa zai saita ta kam dan bazai jure taba masa gudan tsokansa gudan jininsa datake shirinyi sallama yayi Abba ya amsa ya shiga falon kansa akatsa dago Abba yayi yana kallonsa dan ya fuskanci yana tare da damuwa zama Mahmoud yayi kusa da mafhaifin nasa ya gaisheshi cikin kulawa ya amsa yana son karantar damuwar dannasa suna gama gaisawa ya fara sosa kansa yana son yiwa Abba maganar yarasa ta ina zai fara dan karamin murmushi Abba yayi ya fuskanceshi "yadai Mahmoud.
Cikin in ina ya tattaro nutsuwarsa ya fara magana "Abba ina ganin tunda me zai hana khadeeja ta tare tunda itama Abida ta dade da tarewa "murmushi Abba ya kumayi ya girgiza kai dan ya dade da tunanin haka dama ya gaji da zirga zirgan Mahmoud din kwara abashi matarsa suje cen sukarata" hakane Mahmoud nadade ina wannan tunanin cikin wannan satin nake son ta tare"ajiyar zuciya Mahmoud din yayi ya mike har yanzun zuciyarsa turiri kawai take bakin cikin abinda Khadeeja takeson aikatawa gudan jininsa ransa bace ya bar gidan ranan kam duk jarabar Abida sai da ta kyaleshi dan Rasa gane kansa tayi.
Cikin satin kam ta tare ranan da yanuwa suka rakota Anty ta dade tana mata nasiha akan ta bi mijinta kada tabiye zuciyarta haka suka barta tana rusa kuka tunani kala kala ga babban takaicinta wai ankawo ta gidan Mahmoud kaninta! ta kara rusa kuka tun tanayi har muryar ta dishe tana kukan har bacci ya kwasheta cikin dare ta farka saboda batayi shafai da wutiri ba a hankali cikin nutsuwa ta mike ta kunna wayarta taga agogo 2:40 ta mik'e ta shiga toilet ta daure auwala tana mmkin rashin zuwan Mahmoud tada sanshi kamar maye yau gata a gidanshi bai zo ba? tabe baki tayi tace "shiya sani na ma huta da jaraba" tai sallarta ta sauya kaya tai addu'a ta kwanta bacci mai nauyi yai awan gaba da ita karan kiran sallah ne ya tasheta ta mike bayan tayi addu'a ta shiga toilet ta dauro alwala tai raka'atainil fijr sannan tai sallan asuba tana gama azkar bacci ya kuma surarta wajen 11:00 taji maganar Abida sama sama a hankali ta bude ido hade da addu'a ta mike daga kwancen da take tana kallon Abidan tsaye akanta tana murmushi "Anty Khadeeja ina kwana? ga breakfast dinki nan yakamata ki tashi kici kinga bake ka dai bace"kallon mamaki Khadeeja tai mata ya akayi Abida ta zama haka.
Yarinyar da ko kallan arziki bata mata daga mata kai khadeeaj tayi Abidan ta fice mikewa tayi akasalance ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta zauna ta fara breakfast din har ta gama kwanciya ta karayi a hankali taji kwanciyar ta isheta dan karamin tsaki taja ta mike ta koma falonta kamshin data ke so taji a hankali ta lumshe ido tana bin wajen da take jin kamshin na fitowa har babban falon gidan muryar Mahmoud taji da Abida suna kyalkyala dariya gabanta taji yayi mummunan faduwa labulen falon ya daga hangosu tayi cikin wani yanayi na jin dadi wani irin zugi taji zuciyar ta nayi ta juya tana kokarin barin wajen saboda bakon yanayin data tsinci kanta ciki wanda tarasa na menene ga uban jiri data ji lokaci daya ta juya kenan taja kafarta da tai mata nauyi gum ta bige gefan goshinta karan buguwar sukaji suka fito dukansu shida Abida.
pleas! please! kuyi hakuri da wannan kadan ne dai gobe inshaa Allah zan cigaba da gashi nagode sosai fans da soyayyar ku......
Page 30
Karan da tayi sai da Anty ta jita Mami dake part din Abba ma ta danji karan kadan. Ita kuwa cikin azaba ta kakkame shi tana mai wani irin kuka da bashi hakuri da tuba da magiya juya kanta kawai take dan zafi da radadi. Shi kuwa zuwa yanzu bai san duniyar da yake ba, bare yasan halin da take.Can zuwa dan wani lokaci tayi wani irin yukkura ta damke hanna yenshi tare da sakin wani irin wahalellen kara cikin jan numfashi sai ta kuma sakewa ta maida kanta jikin pillow a sume tai luf ba numfashi bare kuka ko motsi. Shi koma har saida hakarsa ta cimma ruwa, sannan ya sahirta mata,cikin wani irin sanyi da yaji yana ratsashi ya zame ya konta gefen ta cikin karfin hali da rawan sanyin yasa hannu ya jawota jikinshi ya ruggume ta cikin kirjinshi tare da jawo blanket ya rufe su kanta yake shafawa yana dan bubbuga bayanta yana mai rawan sanyi so yake yayi magana amman ya kasa gashi shi baima san a sume take ba, daya bude baki zaiyi mgna sai yaji numfa shinsa na fizga hakoran sa su rinka dukan juna yana kat-kat, sai kara ruggume ta yake wai ko zaiji saukin sanyin da yakeji amman ina a haka yayi ta rawan darin har aka fara kiraye kiran sallah.
Yana ji yana son tashi amman ya kasa sai kar karwa da yake ko mgn ta ga gareshi yanaji har aka shiga sallah ya kasa tashi. Cikin ranshi ya rinka Addu,a Ana idar da sallah ya fara jin wani irin zufa na keto mai tako ina daga cikin naman jikinshi yake jin zufar na tsatstsa fowa, a hankali yaji kuzarin shi ya dawo, cikin sanyi da tausaya mata ya dan zameta jikin shi tare da shafa kanta ya subbaci goshin ta, cikin rawan murya yace."Khadija bani da abin da zan biyaki da wannan kyautan budurcin da kika min sai dai nai miki Addu'an rabbi ya biyaki da jannatul Firdausi domin kin gama min komai a rayuwa ta kin bani abin da banyi zaton samun shi ba kin sa rayuwa ta cikin farin ciki, fatana ubangiji ya cika rayuwar ki da farin ciki kin gama min komai".Haka yai ta sabbatu ba tare da sanin halin da take ciki ba sannan ya juya ya shiga toilet a nufin shi yayi wonka yazo yayi sallah sannan ya taima ka mata ya gyara ta itama kafin Mami ta dawo.
Wonkan yayi sannan ya fito ya zura jallabi yarsa sannan yayi sallah tare da zubawa Khadijan shi addu'oi.Yana idarwa ya koma kan gadon a hankali ya zauna gefenta tare da jawota jikin shi. a hankali ya zubawa kirjinta ido cikin mmk da firgici ya kara jawota ganin bugun zuciyarta baya harbawa, kunneshi ya kifa kan kahon zuciyar ta dip yaji ba motsi a hancin ta ya dan manna yatsar shi nannma ba numfashi, a tsori ce ya kara tallabo ta cikin rawan jiki da murya yace." inalillahi wa innalillahi raji un, Khady, Khady meke faruwa da mu Khadija tashi kar kiyi min haka".Sai kuma ya mike cikin tsoron ya dauki zanin ta ya daura mata sannan yaja dan gun tun hijabin da tazo dashi ya samata tare da mikewa ya debo ruwan sanyi yazo ya jawota jikin shi yasa hannu yana shafa mata ruwan a fuskar ta da kirjin ta Amman ina ko motsi batayi ba.
Cikin kaduwa ya fito parlon yana fita sukayi kicibis da Mami data shigo yanzu.
Ganin shi a rude kamar wanda yayi kisan kai yasa tayi kanshi da sauri cikin tuhuma tace."Kai Mahmoud lafiya kuwa meke faruwa me ya firgi taka haka?".Cikin tsoron ya kalli Mami fuska a karye yayi kalan tausayi sai kuma kawai ya nuna mata cikin d'akin tare da cewa."Mami bata numfashi zuciyar ta bata bugawa Mami ki duba min ita wallahi ina jin tsoro kar Na rasata".Kalaman shi sun kulle mata kai amman kuma sai kawai ta shiga dakin cikin mamakin ta karisa gefen gadon ido ta zare ganin, Khadijan ce konce kan gadon kuma gata a sume duk gashin kanta a hargitse sannan daga kasa inda take konce jinine a wurin.Kai a kulle ta yamutsa fuska cikin son gani me ya jawo wannan lamarin ta juya ta fita parlon a parlon ta same shi yana ta safa da marwa,cikin daga murya tace," kai Mahmoud me ya samu Khadijan ka gaya min meke faruwa da ita?".
Ido kawai ya sunkuyar cikin kunya dan bai san me zaice da ita ba. Anty kuwa tana kofar parlon ta tana jin abinda Mami ke fadi ta nufi dakin Mamin cikin tsoro da kaduwa, dan dama a firgice ta kwana tunda taji muryar Khadijan tana kuka sannan gashi gari ya waye bata dawo gunta ba.
Tana shiga ta kalli Mami cikin tsoro tace."Mami ina Khadijan? meke faruwa da ita?".Da hannu ta nuna mata dakin sannan ta juya ta shiga Antyn da Mahmoud din suka bita a baya. Suna shiga Anty kam ta ruggume ta cikin tsoro tana kiran sunan ta, shiru ba motsi Mami ce ta debo ruwa mai sanyi kalau tazo ta fesa mata a fuska.
Lokaci daya tayi wani irin ajiyar zuciya sai kuma ta damk'e hannun Anty da hannuta daya hannuta daya kuma ta damko hannun shi cikin kukan wahala da raunin murya tace." wayyo Allah nahh wayyo Anty na wayyooo Mama na Mahmoud zai kashe ni".Sai kuma ta kara damkesu cikin zubda kollah duk da idinta a rufe suke cikin kukan taci gaba da cewa."Please Dan Allah Mahmoud ka barni zan mutu Na tuba kamin afwa wayyo Mahmoud zaka kashe ni".
Anty kam duk da ba gaya mata akayi ba ta gano abin da ya ja mata wannan abu sai dai tacika da mamakin abin ita kuwa Mami cikin rashin fahimtar ta bisu da ido. Shi kuwa cikin jin kunya yasa hannu a kanta yana shafawa cikin sanyi yace......
contact-form
0 Comments