PAGE 1 TO 5
Ƙauyen Lafani wani ƙauye ne a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Illela local govment yamma da ƙauyen ciwake, sanaan mutanen garin noma, mazan garin kusan mafi aka sarin su suna fita hausa (lagos ibadan etc) shi ake nufi da hausa.
WANNAN KENAN
"Jiddah-Jidda, wai Jiddah dan uwarki bakiji ina kiran kine, ko so kike muryata ta dashe? shegiya dangin mayu masu ƙashin tsiya,yanda uban naki yake kwance ba cas sai an juyar tayaya in baki fita kinyo talla ba zan ciyar dake dashi, su Atiƙha dai da Sa'ina wa yanda suka kawo dukiyar auran su, sun hana su tallah, ke ko basu hana su bama baza suyiba, tunda gaki ƙatuwar banza duk kin tsofe musu shekara sha huɗu ba mashin shini duk ƙauyen nan babu sa'ar ki, ni wallahi da babban budurwa gwamma ƙaraman bazawara.
Wata yar matashiyar dattijuwa,bazama akirata dattijuwa ba, kasancewar yayan ƙauye ana musu auran wuri, ga wahala da rashin gyara ke sa su su tsofe, fara ce gajera mai faɗeɗen baki da gajeran hanci, daja daja take da ƙazanta.
Daga wani É—an É—aki Jidda share hawayen da ya zubo mata gyara ma mahaifinta kwanciya tayi bayan ta goge masa jiki ta cire masa kayan da yayi fitsari ta aje a gefe,"Gwaggo ina zuwa,na gyara ma Abba jikine bari in É—auko hijjabi.
Fyace majina tayi da saleɓen zanin ta daga bisani tace,"dan uwarki ma karki fito, in rana tayi kyasan yanda zakiyi da kayan nan nide kuɗi nake buƙata. Fitowa tayi da sanye da hijjab ɗinta duƙun-duƙun ta cukuykuye shi don matuƙar kunya takeji yanda take fita,yau inshaAllahu sai taje ƙauyen ɗan boka wajan yayar mahaifiyarta ta samo ɗan sabulu na wanka dana wanki tazo har kayan kashi da fitsarin Abbanta ta wanke,don duk tallan nan da take ma Gwaggo iyakan ta ta bata abinci ba suturan balle tokan wanka dana wanki.
Ɗaukan bokitin wainar tayi ta ɗaura akai ta fita, bayan gwaggo ta gaya mata na nawa tayi. Zahra kenan , bata aje komi ba face gulma,ba ruwan ta da sallah tun ƙarfe uku na dare take tashi ta hasa wutan ta ɗaura masa, ba ruwan ta da sallah ko wanke ido, neman kuɗi ne kawai a gaban ta. "Zarah ki wanke min kayana gaskiya duk sunyi dauɗa".
Faɗan wata yar yarinya bai kama da zarah kallo daya zakai mata zaka tabbatar da yarta ce, yarinyar bazata gaza shekara sha ɗaya ba, ɗaure take da ɗaurin ƙirji kan nan daga daga ba kitso hamma take tana miƙa.
"Kajimin ƴar kaza-kazan uwa,in ankai ki gidan Hallirun hakanan ubanki zai rinƙa zuwa miki aiki".
"Wallahi Zarah kwasowa zanyi in rinka kawo miki,ai baki koya min ba".
"Gafaran kudai mai kuke tattaunawa ne hayani har killa tunda safen nan?
Wata yarinya yar kimanin shekara sha uku tana sanye da riga da zani, ta É—auke da bakar leda.
"Ke kuma daga gidan uban wa kika kwana? Ya tsina fuska tayi tace,"ke zarah ansa wannan Alhaji Sa'idu ne ya ce inkawo miki kaji ne ki goge wiya. Lokaci daya Zarah ta washe hauru ta amshi ledan tana dubawa, Alhaji Sa'idu ɗan albarka, kinsan de gidam sarkin aska sun kawo kayan auren ki koh,tou ki iya takun ki a hankali, karki bari ki kawo min ciki gida. Kinga Zarah innayi cikin ma uban shi yafi kowa kuɗi a wannan ƙauyen namu,ko zubar wa bazan yi ba don inci gado.
Jidda ko tana fita tayi sa'an saida masar ta, daganan ta wuce É—an boka inda yar mahaifiyata ta amso sabulu da omo,a gaggauce bata zauna ba ta juyo don tana tsoro kar Gwaggo ta casa ta,don don yau tana da cin kasuwar gada kuma tana so ta tsamtsame kayan su.
Assalamualaikum gwaggo n dawo". Tana aje bokitin.nTou ina ruwa na,da dwowar ki,bani kuɗina in biyar ya ɓace wallahi sai na naɗa miki na jaki, Cike da masifa take maganan. Miƙa mata tayi daidai lokacin ledan sabulun ya faɗo. Da kallo Zarah tabi leda kafin ta ɗago,tace,"kuɗina kike ɓoye wa ki kashe,shegiyar ɓarauniya, Girgiza kai tayi jikin ta ma rawa tace......
PAGE 6 TO 10
Girgiza kai tayi jikin ta na ɓari yana rawa tace,"Gwaggo ban taɓa miki kuɗi ba wallahi. Ahasale tace,"in baki taɓa min kuɗi ba kanti sani kikaje kikai sata koko yawon ta zubar ɗin da kike zuwa yi anan kika samo, dole ma yau in duba ki,don karki kwaso min abin kunya duniya ta zageni baccin ina iyakan KoKarina akan ki. "Gwaggo wallahi Inna Mairamu ta tabbani,naje Dan boka ne kayana duk sunyi dauɗa". Cikin muryan kuka take maganan,yayinda hawaye ya saukko kan farar fatan fuskan ta da ta koɗe da datti. Gwafar uban can, har can kika je don kija min zagi, in banda kin rainani, in Daura miki talla ki wuce Dan boka wajan munafukar Inna ki,tou uban mai kika ce mata, wani sharri kika laƙaba min, ko kinje tabaki sabon maitan ne, Cike da masifa take maganan,ta ƙarashe maganan da sigar tambaya.
Girgiza kai take yayinda hawaye ke cigaba da wanke mata fuska. Sa hannu Zahra tayi ta wufce ledan sabulun. "Bazaki wanki da wankan ba,saide ki mutu cikin dauɗa,harni zaki gaya ma kayanki sunyi dauɗa". Tana magana tana dukan ƙirjinta, Gwagg, Zanci uwarki kika ƙara kiran sunana kurwata kur la'ilafi ƙafa dubu,in wani sidda barun maitan aka ƙara baki toh namana ɗaci.
"Zarah wai miyasa baki karkashe ƴar iska da mari,bata san ban bancin ɗiyar bora da ɗiyan mowa ba,da kin bari ta fara wanka da wanki,wannan mai ƙwalaƙwalan idanuwan sai tace tafi ƙarfin miki talla".
FaDar AtiKa dake zaune kan gadon kara ƙarKashin bishiyar dalbejiya tana kallo a wayarta sha kiɗanka baƙauye. Ke Atiƙa ina zanyi sake, ai wallahi a ƙauyen nan na lafani JIDDAH sai ta zama abin kwatance ba boka ba mallam,amma sai ta zama mafi ƙatuwar budurwan da ta tsufa ba aure,inko kinga tafara tsafta ta samu wanda zai aureta sai bayan raina". Sum sum Jiddah ta wuce tana sharan ƙwalla ta nufi ɗakin da mahaifin ta yake kwance,da sallama ta shiga ɗakin duk da tasan bazai iya amsawa ba.
Ƙarasawa tayi kan gadon karan da ko tabarma babu akai da yake kwance. Hawaye tagani nabin fuskan shi,jikin ta na rawa ta duƙa daidai kan fuskan shi duk tabi ta ruɗe jikinta har yafi ɗazun rawa,don sam bataso taga mahaifinta cikin damuwa,da da dama ta ɗauke mai ciwon da ta cire mai ajikin shi tace,"subuhanallah Abba hawayen kuma na miye?,dan Allah Abba kadena damuwa cuta aiba mutuwa bace,zaka warke inshaAllahu kaji Abba". Cikin muryan lallashi take maganan,tana haɗiye kukan dake ƙoƙarin ƙwace mata. Dady Dady katashi kamin wanka natafi school, Momy tace in tasoka ai ita ba Yar aiki bace,kuma kar in ƙara tashinta in tana bacci".
FaDan wata ƴar cute girl da bata wuce shekara biyar ba da take tsaye bakin gadon mahaifinta tana bubbuga ƙafafuwan sa. Girgiza kai yayi lallai Abeeda bata da ranan shiryuwa,ace ka haifi Ya bazaka iya kula da ita ba, taɓa baki yayi ya miƙe yana kallon agogon da ke manne jikin ginar ɗakin lokaci guda yace,"muje bedroom ɗinki,inyi miki wanka kinji Little cute.
Ko alaman damuwa babu atattare dashi don inda sabo ya saba da halin Abeeda,kamar ba auran soyayya sukayi ba,burinta guda tahau motor tasa manyan kaya sam bata damu da gyaran gida ba,balle kula da Æ´ar da ta haifa,gashi mugun halinta baisa ta zauna da Yan aiki. Daf da zasu shiga bedroom É—inta ta tace,"Dady ka samo min Nany gaskiya".
Shafa kanta yayi yana murmushi yace,"inshaAllahu Little Cute É—ina ,zansa Hajiya Mama ta samo miki new nany. Tsalle tayi cike da murna tace,"thank you Dady i love you",tare da manna masa kiss a hannu.
Tare suka sake ma juna murmushi. Wanka yayi mata ya shiryata kafin yaje kitchen ya dafa musu indomie da Kwai, abaki ya bata kafin taje ta Dauko jakan ta ya kira driver ta ya tafi da ita makaranta.
Nufan Dakin matan shi Abeeda yayi, tana kwance kan gado ga uban tulin kaya ba ninki, ranshi yaji yayi matuƙar ƙara ɓaci da halin Abeeda ƙwafa yayi, sai lokacin tasan ma anbuɗo ƙofa anshigo sam bata sani ba.Ɗan gajeran tsaki taja ta gyara kwanciyar ta taci gaba da danna wayarta alaman chart take a hasale yayo kanta yasa hannu.
PAGE 11 TO 15
Yafisge wayar ya bugata da bango ta fashe ta watse. Buɗe baki tayi da hanci ta kalle shi ta kalle inda wayar ta fashe. Azuciye yake kallonta,kallon raini da ƙasƙanci ya kumbura yayi fam. "Wai dan Aliyu wannan wani irin wulaƙanci ne,har yakai yau da ka fasa min wayata".Cikin ƙunan rai take magana,don chart ɗin da suke da ƙawayen ta awani group ya ɗau daɗi gashi ya fasa wayar. Murza ƴan yatsu yakama yi yana nuna ta da ɗaya,yace,"Abeeda wallahi tallahi sai nayi mum-munanan saɓa miki,ke wata irin sakarya ce ƙazamar gida,wacce bata san ciwon kanta ba,wallahi Abeeda baki san inda yake miki ciwo ba,ji ɗakin ki,inda kike kwana kamar juji bola,anjima kifita ko ɗan kamar matan gwamna.
Nau yayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yaci gaba da faɗin ɗakin ki kenan inaga falo,toilet kitchen tirrr da auran ƙazama irinki,bedroom ɗina dana ƴarki sai in ni na gyara,tou wallahi daga yau nazo na ƙara ganin kina chart baki aikin da matan gida maana matan aure sukeyi ba wallahi sai na mummunan saɓa miki,mtsewww. Ya ƙarashe maganan dajan tsaki. "Aliyu ni ba ƴar aiki bane inko kanaso kaga waje tass kanemo ƴar aiki,kuma wallahi ba abinda zan gyara".Cike da rashin kunya take maganan kana,ta miƙe ta faɗa toilet kai ko ɗan kwali babu tabarshi tsaye.
Girgiza kai kawai yayi yafita ranshi na ƙuna.
NIKO NACE DAMA DUK WANDA BAIJI BARI BA,YAJI YEHO,YANZUN ALIYU TAURIN KANKA WA GARI YA WAYA
Abba na inshaAllahu zakaji sauƙi ka taka kamar yanda kowa ke! "Kina fitowa ki ɗau lalamen ga ki bashi abinda ya rage kisha kizo ki ɗebo ruwa kafin lokacin gada yayi koko sai nazo na lallasa miki jiki".
Maganan Zarah ne ya katse mata maganan da take wa mahaifinta,miƙewa tayi jiki a saɓule tacire hijjab ɗinta tasa akan ƙofa tafito ta ta ɗau ƙwaryan dake buɗe duk ƙuda nabi kana,ta ɗauke ludayin dake gefe kan wani fayfay tasa acikin lalamen ta nufi ɗaki. Aje ƙwaryan tayi ta gyara masa kwanciya ta yanda zata bashi baibiyo ta hanci ba ta ɗeba takai mai baki taga ya kauda kai,murmushi tayo don tasan mai kauda kan yake nufi. Zama tayi ta lanƙwashe ƙafarta ta fara sha ,ganin ta fara sha yafara murmushi,don wani lokaci bai fara shan fura ko lalame sai yaga tasha ta ƙwoshi kafin yake karɓan wanda taba shi,hakan ko akayi sai da ta ɗansha,duk da lalamen baida wani yawa,kafin tabashi yasha.
Tana gama bashi ya goge mai baki ta gyara mai kwanciya kafin ta kwashe kayan tafita ta ɗau bokati tafita rijiyan dake jikin gidan su ta baya ta ɗebo ruwan ta cika ko ina. Fakan idon Zarah tayi ta kamfata ruwan taje tayi wanka,duk da babu kayan da zata sauya,wannan masu warin datti da dauɗa ta kuma sawa tafito ta anshi sautun zuwa cin kasuwar gada. "Wallahi Salman nagaji da zama da Abeeda,ƙazantar ta tayi yawa". Aliyu ne cike da takaici yake gayama Salman damuwar shi.
Ni wallahi Aliyu da kaji maganan Ummie game da aure da baka shiga halin damuwan nan ba,jiyanda ka susuce kazama kaima wani ƙazami dakai". "Wallahi ko Salman nabiye wa son zuciya,nayi zaɓen ƙyale-ƙyalen banza,zaɓen tumin dare". "Wallahi fushin Ummie ne kaje ka lallaɓatw kabata haƙuri Allah bashi kwana biyu kanuna mata kana son waccan yarinyar".Hakane ko aboki koko amini zance,duk da bata nuna mani komi game da auran Abeeda banbi wasiyar mahaifina ba,ɓacin ran da nasa mata a lokacin shi kaɗai ya isa yabibiye ni".
Tattaunawa suka rinƙa yi yanda zasu ɓullo ma wannan alamarin. Dafda magariba ta dawo niƙi-niƙi da kayan da suka fi ƙarfinta. "A'a Hauwa Jidda kindawo gadan ne,wai bakijin kunya goɗai-goɗai dake kina zuwa cin kasuwa. Haɗa rai Jidda tayi tamm kamar zata fashe ta haɗa giran sama dana ƙasa,a hasale tace,"Maa'u ina ruwanki,banjin kunyar ke da kike da kunyar ai baki zuwa. Maa'u ƙawar shashancin Atiƙa ce duk sa'ani suke da Atiƙa bata da kunya sosai. Riƙe ƙugu Maa'u tayi,kana tace,"ke mayya bora kawai harkinyi bakin da zaki zageni yau keda Zarah ne,sai naja an lakaɗa miki dukan tsiya". Tsaki Jidda taja,tare da cewa kije ki faɗa mata inyaso karta barni da rai. "Kam bala'i haka kikace. Ko tanka ta Jidda bata kuma yiba.
Wucewa tayi kai tsaye gidan su Jidda tana kuka ta kwashe ƙarya da gaskiya ta faɗa ma Zarah da ƴaƴanta,zarah tacika tai fam jiran jidda take ta ɗau mummunan mataki akanta. Jidda ko da ƙyar tasamu yaron da ya temaka mata ya ɗauko mata kayan.
Assalam, batakai da ƙarasa sallaman ba ko sai dai taji sauka abu akanta wanda yayi sanadiyar.
PAGE 17 TO 20
Assalam, bata kai da ƙarasa sallaman ba ko,sai dai taji saukan abu akanta,wanda yayi sanadiyar zubewar ta ƙasa wanwar babu motsi. Duk da haka Zarah bata kula da aika-aikan da tayi ba,ta bita ta hau ruwan cikin ta tana ta bugu bata ji bata gani. Hansai ce tazo wucewa taga tana dukan ta,amma ko motsawa batayi,tazo a zuciye ta ja Zarah gefe ta wurgar,kan Jiddah ta nufa tana girgiza ta. "Ke Hansai kina shiga min hanci da duƙunƙune akan lamuran gidana,in banda iskanci ƴarki ko ƴata. Cike da masifa take hayayyaƙo ma Hansai. "Tou sakaryar mace sha-sha-sha samna,kin kashe masu ƴa kin huta".
Kuru-ruwa Zarah ta sake take mutane suka fif-fito,ga Jidda kwance bata ko motsi. Na shiga uku na lalace ni Zarah, Cike da tashin hankali duk ta ruɗe take magana. Aiko baki shiga uku ba tukunan,yanzun zan ruga gidam mai gari inkai ƙaranki,Allah bashi a turo da ƴan sanda daga birni atafi dake ki bayani". Faɗan wani ɗan matashin yaro da jiya yadawo daga cirani. Hansai tace,"wallahi ko hanzarta Zarah bata da mutunci bata da imani. "Dan Allah kuyi haƙuri kuyi min rai.
Atiƙa da Sa'inah ko duk sunyi ƙulu-ƙulu da ido ,sun rakuɓe a gefe.
"Ummie na tuba. Faɗan Aliyu dake duƙe gaban mahaifiyar sa ya haɗa hannuwan shi biyu tare da maraice murya. Murmushi tayi tare da gyara zama,tace,"mai kayi kuma da kake neman tuba. Ta tambaya cike da mamaki. "Ummie kinfa sani,Ummie na tuba zan zauna da ita. Riƙe baki tayi da mamaki,kafin ta kuma cewa,"wai kai lafiyan ka kuwa?,wa zaka zauna da ita?,ina Abeedah. Lokaci ɗaya ta jero masa wa ƴannan tambayoyin. Ummie ɗiyar baba Ibrahim nake nufi,na gaji da auran Abeeda Ummie,ƙazantat-ta yayi yawa,Ummie harfa Cutie bata kula da ita".
Taɓa fuskan tayi,ta kauda kai gefe kafin tace. Wai ke Aisha kina tunanin zan maida kaina ƴar aiki ne?,wallahi bai isa ba. Faɗan Abeedah dake zaune rashe-rashe a ɗakin ƙawarta Aisha. Aisha murmushi tayi kafin tace,"kar ki saki jiki kiyi aikin gida ,wallahi ƙawata jikin ki ɓaci yakeyi,ni kin gani kafin ya fita sai yayi komi,tunda yace bai son ƴan aiki". Ai ke kin huta,kin samu mijin marainiya,kin dace miji,ba kalan nawa ba sai girman kai kamar fir'auna. Dariya suka sheƙe dashi suka tafa.
SHIN WANI HALI JIDDAH TAKE.
SHIN MAI UMMY ZATA CE MA ALIYU.
ANYA KUWA AISHA BA RAINA MA ABEEDA HANKALI TAKE BA.
0 Comments