NAMIJI BAYA KAD'AN
Page 1
Bazan manta da kiba kun zamo ni Na zamo Ku ina alfahari daku Khaleesat haydar Anty Fauzo Ummu Khamal Dr Rukayyat Aysha A Muhammad Rufaida Yusuf Jannart lamido sannu kawai suke jera mata shida Abida runtse idonta tayi saboda kayan dake jikin Abida na nuna ilahirin siffarta kanta kawai ta daga musu ta ja kafarta ta bar wajen zuciyar na mata wani irin tukiki data rasa na menenetana zuwa kan gadon ta tafada a wahale tana mmkin sauyawarta wani uban tsaki taja hade da runtse idanuwanta hangosu tayi a yanayin data gansu da sauri ta bude ido tan jijjiga kanta sam tarasa wanne kalan tunani zatayi ta samu saukin wannan yanayin data fada wanda tarasa gane kansa ga uban zogi da gefen goshinta ke mata.
Washegari jikinta asanyaye ta tashi tarasa gane yanayin data ke ciki rabonta da Mahmoud tun jiya data bige sukai mata sannu kanta ta dafe tana kallon breakfast din da Abida ta kawo mata tun dazu da safe. jikinta ba kwari ta tashi daga zaunen da take ta shiga toilet tai wanka ranta ajagule. tunda Khadeeja ta tare Mamy ranta ke suya abin na matukar damunta tarasa gane inda wannan kaddararren aure zaije uwa uba cikin da akace khadeejan nadashi sam ko kadan bata kaunar wannan cikin hnklinta tashe take kai komo tarasa hanyar da zatabi ta warware wannan daurin gwammon na auren Khadeeja da danta Mahmoud anty Ray ce tai sallama da kyar Mamy ta amsa tana kallom fuskar ta hannunta tasa ta dauki hijab ta kalli anty Ray tai mata alama da ido na sutafi ba musu anty Ray tabi bayanta har suk fito haraban gidan inda motocin su suke kai tsaye mota mamy ta shiga anty Ray ta shiga driver yaja su suka tafi gidan Mahmoud din dan zuciyar mamy takasa nutsuwa sai taje daga kalan zaman da sukeyi babban burinta taciwa bazawarar yarinyar nan mutunci ta hakuri ta bar mata danta dan tasha alwashin yau yau din nan sai Mahmoud yasaketa tagaji da tafasan da zuciyar ta ke mata akan hanya Anty Ray taiwa Mahmoud test akan lallai ya fice ya bar gidan kafin mamy takaraso.
Yana ganin test din ya maza ya bar gidan hankalin sa atashe yarasa gane kan mahaifiyar sa taki hakura da wannan lamarin na aurensa da Khadeeja. Driver na tsayawa afusace ta bud'e kofar motar ta fito tun kan tashiga gidan ta fara kiran sunan Mahmoud a kufule Anty Ray cikin sanyi da mmkin sauyawar mamy lokaci daya akan auren Khadeeja da Mahmoud da tayi kai tsaye bangaren khadeeja ta nufa tana kwalawa Mahmoud kira dan tasan mayen ta ne zuciyarta na bata yana cen dakinta yana maitar tashi kamar daga sama Khadeeja taji kiran tana barci dan har cikin dakin mamy ta shigo tana surfa masifa tana kwalawa Mahmoud kira a hankali Khadeeja ta bude idonta dayayi ja alamun bacci ne sosai acikinsa wani wawan mari mamy ta dauketa dashi wanda yasa Khadeejan wartsakewa daga nannauyan baccinta a gigice ta mike hade da sakin wani bahagon kuka me ban tausayi Anty ray ma da Abida mamakin marin sukai fuskokin su alamun tsoro suka k'ura musu ido cike da tausayin Khadeeja nuna mami tayi da dan yatsanta cikin karaji da masifa tace"uwarki zatai sallama ki kasa amsa mata tabbacin baki da tarbiyya ko? tun yaushe nake kwalawa dana kira kina ji kinyi biris dani, to ni ce uwar Mahmoud ayau kuma sai ya rabu dake tambadaddiya tarasa wa zata aura sai k'aninta har da daukan ciki dan tsabar tambadewa, na tsani wannan kaddararren auren naku kuma ayau za warwaresa dan bazan iya cigaba da zama dake a matsayin matar dana ba wallahi.
Takara tana fidda huci naban takaici babu abinda ke tashi sai sautin kukan khadeeja mai ban tausayi. waiwayowa mami tayi tana kallonsu Abida da suka tsura mata ido "ina yake shima shanyayyen?" girgiza mata kai Abida tayi tana jin ba dad'i aranta dan tasan muddin aka tab'a Khadeeja tofa bata taba gane kan mijinta shiyasa ko kadan batasan wannan hayaniyar yanzu "mami ya fita cen gida wajen Abba kuma bana jin zai dawo da wuri"wata wawar ajiyan zuciya mami tayi "sai ya dawo yau yasame ni shima dan ubansa yau sai ya rabu da tsohuwar guzumar nan!" tana cikin masifar Khadeeja na fidda kukan takaici kuka na fidda sauti na ban tausayi ga duk mai sauraronta wayar mami ce tayi kara number Abba tagani a kufule ta daga itafa ayanzu bataki aurenta ya mutu akan raba auren Khadeeja da Mahmoud abinda taji abban na fadane yass jikinta ya sanyaya ta kashe wayan tana fidda huci da kuma mamakin abinda Abban yace mikewa tayi ta watsawa Khadeeja mugun kallo "kisani tsohuwar bazawara kika tunanin wani zawarcin nan gaba zanje na dawo duk dare yau sai dai ki kwana gidan ubanki yarinya sai kace maiya.
Fuuu ta wuce anty ray da Abida suka bi bayanta mota ta fada tana takaicin rashin samun Mahmoud din a gida girgiza kai Anty ray tayi tace "mami yakamata ki fuskanci yarannan ki duba damuwarsu, auren nan daga Allah ne kina kallon rabo har ya ratsa, katseta mami tayi "rabon banza me ake da rabo irin wannan idan ina raye bazata haife wannan rabon ba"
shiru anty Ray tayi dan abin yafi karfin ta suna komawa gida labarin da Mamy taji ya gigita sosai Abba ne ya sa ta ta zauna ya fara mata jawabi "kinga abinda akaiwa Amira ko? bazan yarda ba sai na d'au mataki UWAR MIJINTA tai mata dukan tsiya har cikin jikinta ya zube sannan ga gociyar kashi a hannunta duka na fitan hankali kamar ba mutun ba kalleta fa!"wani irin masifaffen yanayi mami ta shiga lokaci daya tana kallon amira da fuskarka tasha bandage tana fidda kwalla ilahirin kamanninta sun sauya bazakace Amira yar gayu ce akai mata wannan mummunan dukan kuma ma wai uwar mijinta wani kuka mai kuna ya kufcewa mami kasa jure kallonta tayi gaba daya jikinta amace yake zuciyarta na harbawa da mugun sauri takaici da bakin cikin dataji yanzu bata taba tunanin akwai irinshi ba, jikin Abba a mace ya mike ya fice daga falon yana ayyana shi kadai yasan irin matakin da zai dauka kan mutanen nan wani bahagon kallo anty ray takewa mami tana girgiza kai kwalla na fitar mata " mamy kin gani ko.
Ishara ce wannan kome? kin daki yar mutane anyiwa taki dukan tsiya kina kokarin zubar da cikin yar wani an zubar dana taki yar, duniya kenan yanzu sakayya nan danan take zuwan wa mutun kanayi za ai maka ninkin ba ninki wanda Allah keso yake nunawa ishara"ta mike kwalla na zubar mata tana kallon Amira da itama kwallan takeyi jikin mami asanyaye take sauraron Anty ray zuciyar ta asanyaye.
yana kallon sun fice daga gidan ya shigo hankalinsa atashe kai komo ya fara yi yana son sanin halin da Khadeejan sa ke ciki ya na matukar kaunarta da kyar ya iya jurewa rashin ta na kwana biyu kasa jurewa yayi jikinsa na rawa yai bangaren ta sautin kukanta ya hautsina masa zuciya wani irin yanayi na bacin rai ya ziyarceshi kai tsaye wajenta yayi yana jin takaicin fitar kukan nata dayake taba masa zuciya.........
Page 2
Cikin wani irin taku na kasaita ya shigo cikin dakin ganinta a takure cen karshen gado ta cusa kanta cikin cinyoyinta kukan ta na fita cikin wani sauti me hautsina masa zuciya kai tsaye kusa da ita ya karasa ya zauna gefenta hade da janyo ta jikinsa kamshin turarenaa data ke so ta shaka shiya hana ta hankadesa dan mugun haushin sa take shi akanshi akai mata marin data hango taurari duk da haka sai da tayi yunkurin kwace kanta ta kasa dan ba karamin ruko yai mata a kurjinsa va hannunsa ya sa ya zuge zif dinta ya cusa hannunsa cikin jikinta yana shafa gadon bayanta hade da shafar fatan jikinta mai laushi da tsantsi kasa mata magana yayi saboda kukan ta na sa jin zafi musamman yasan dalilin faruwan kukan yasan mami ce cikin jarumta da dauriya hade da jin dadin shafar da yakewa fatarta data fara sashi cikin wani yanayi ya fara magana cikin muryar lallashi" kiyi hakuri babyna ki dinka kallon komai kamar bai faru ba, laifi nane ni na janyo miki amma kiyi hakuri komai zai wuce inshaa Allah, ki dauki komai amatsayin kaddara wacce zata zame miki alheri nan gaba ko ma ince ta zama musammaan dan babyn dake jikinki da kuma aurenmu shi kadai ya isa yasa ki gane ko mai mukaddari ne daga Allah, khadeeja babu wani bawa da ya isa ya kaucewa kaddarar sa tabbasa ikon Allah yafi karfin komai Allah ya kaddara ke tawa ce babu wanda ya isa ya rayu dake saini babu wanda ya isa ya dasa miki da sai ni babu wanda ya isa ya san budurcinki yasanki a ya mace sai ni duk da irin aure auren da kikayi sai da Allah ya tsare min ke wannan bai isheki yadda da k'addara ba.
Abadini maganarsa taso yin tasiri aZahiri kuwa wani dankaramin duka ta kaiwa Kirjinsa hade da fashewa da kuka ta turesa ya riko ta sosai hade da sake mannata kirjinsa kamar Za kwace ta har sai da tayi kara dan ya had'a jikinsu sosai kamar zasu manne su zama abu daya. cikin kuka ta fara magana ranta a bace yaron nan iskancin sa na kona mata rai " ka kyaleni nace! da gaskiyan mami data ce min katuwar banza da kanin cikinta wannan wacce iriyar wahalalliyar rayuwa ne ace ina auren kani na harda ciki? wannnan cikin sunasa gawa dan bazan haife takaici ba !"ta karasa da kuka sosai tana duka jikinsa still hannunsa na cikin jikinta yana shafawa da karfe har zuwa saitin cikinta murmushi yayi yana mamakin maganganunta khadeeja akwai son girma yasani tun asali haka take amma meyasa tunaninta bai zuwa kan way'anda suka fita daraja.
Hankalinsa kwance kamar bata fad'a masa wata magana ba"khadeeja kina karanta tarihin me sunanki kuwa? kina bincikan manyan mata da sukaiwa addini hidima masu daraja da kima"lumshe idonsa yayi dai dai inda yakai hannunshi ruwan cikinta yana jin dadin akwai dansa manne a ciki "kin san tana da shekara nawa ta auri masoyinmu annabi MUHAMMAD (s.a.w) itace mace ta farko data fara karban addini meyasa tilastawa kanki abinda bai kai ya kawo ba.
Ni dake Khadeeja har abada ba rabuwa haka zaki cigaba da haifamin y'aya kyawawa kamarki!"ya zamota daga jikinsa yana kallan karamin bakinta fuskarta tab hawaye harshensa yasa ya lashesu tana fusge fusge yasa hannu ya rike fuskan ya manna bakinshi cikin nata ya cafko harshenta yai mata wani cool kiss yadade yana shansu cikin sanyi da kwarewa idon shi a lunshe sannan ya saketa idonshi sun kada sun canza kala ajiyar zuciya yayi sannan ya mike ya rungume da hannuwansa ya zuba mata manyan idanuwansa da suka sauya kalaki kular min da kanki da kuma babyna idan bazaki daina kukan nan ba ayau sai na maimaita abinda ya faru har na baki baby ya karashe maganar hade sakin murmushin mugunta wani wawan kallo tai masa na jin haushi ya juya gaf da zai fita ta daga muryan ta me kuka tace "ciki dole na zubar Mahmoud ko baka so sai dai ko mai zai faru ya faru"kai ya girgiza ya fice ransa ab'ace dan bai kaunar yaji wani abun wanda zai taba masa lafiyan babynsa balle khadeeja na shan alwashin rabasa da gudan jininsa yasanta da kafiya tsab zata aikata abinda tashe girgiza kai yayi direct da yafito gidansu Khadeejan ya zarce sam baiyi niyyan hadata da iyayenta ba bashi da mafita tunda cikin ajikinta yake tsoronshi daya zata iya aikata duk abinda taso kansa ya dafe yana jin takaicin halin data jefa kanta taki hakura gidansu ya shiga cikin murna mama ta tarbe shi bayan sun gaisa kansa a kasa yana tunanin hanyar da zaibi ya fadawa maman ajiyar zuciya yayi kokad'an bai son hadata da iyayenta bashi da wata mafita ne sai wannan cikin hikima ya fadawa mama kafin ya kai karshe ta fara fada ranta matukar bace harshi ta hada kan meyasa tuntuni bai fada ba jikinsa asanyaye yabar gidan.
Yana barin gidan mama ta kira baban Khadeejan ta fad'a masa kan zataje tai mata fada bai hana ba dan shima ranaa ya baci abinda yaji khadeejan nasonyi, tana kwance idonta a rufe maganganun da Mahmoud yai mata dazu sun ratsata tabbas wannan almari daga Allah ne amma yazatayi da kiyayyar mami.
Juyi ta karayi hade da dafa cikinta wani takaici ya taso mata ta saki karamin tsaki muryar mama taji tana sallama zunbur ta mike da sauri tai falo ganin maman yasa ta karasa wa da sauri. kallon data ga maman na mata ne yasa jikinta yai sanyi ta kalli mama da idonta da ya cicciko da kwalla a hankali tace " mama sannu da zuwa"shiru tayi bata amsa haushin maman daya ace wai khadeejan ta ke kokarin aikata danye aiki akan dan cikinta tsaki mama tayi ta zauna tana karewa khadeejan kallo cikin hasala da fada ranta abace tace "anya khadeeja kina son ki cika da imani? kin wa tsar da kyakkyawar tarbiyyan ki.
Ina iliminki hankalinki da tunanin ki? wallahi muddin naji wani labari akan cikin nan zan yi mummunan saba miki Abban kuma yace sai dai ki nemi wani uban!"zaro ido khadeeja hade da zuban hawaye na mmkin inda mama taji zancen wato Mahmoud ya fada musu takaicinta ya karu tsawar da mama tayi ne yasa ta dagowa da sauri" muddin bazaki bi mijinki ba toh ki nemi wasu iyayen tunda kike rashin hankalinki naji labarin komai zuba miki ido ne naga abin zai zama bana kare ba to wallahi ki kuka da kanki taurin kan tsiya kamar kanki farau shi sunna yayi kuma Allah yai mishi albarka dan ina alfahari da wannan auren wallahi muddin kikace zaki dinka bata masa rai sai dai ki nemi wasu iyayen, k'aramar yarinya ce ke da zaayita lallashinki shashasha kawai.
Mama ta mike cike da fushi ta bar falon da sauri Khadeeja tabi bayanta tana bata hakuri cikin zubda hawaye tsayawa mama tayi "muddin kina son zaman lafiya ki kuma kiyaye bacin ranmu kibi mijinki "ta tafi tabarta a nan tsaye tana kukan takaici. da daddare bayan ta idar da sallar ishai zuciyarta ba dadi sam bataji dadin fadan mamansu ba Abida ce ta shigo dakin tana k'amshi jikinta sanye cikin kananan kaya masu fidda surarta a fili cikin yauki da iyayi tayi far da ido "anty Khadeeja barka da dare kizo babban falo zamuyi dinner megidan nason zanyi magana damu" ta juya ta fita kallon mamak Khadeeja tai mata sannan ta mike jikinta asanyaye ta tafi babban falon yanayin data gansu ne yasa ta faduwan gaba abida na jikinsa tana zuba masa kissa yana biye mata ganinta bai sa Abidan sauka daga jikinsa ba sai da ya janyeta hade da zubawa Khadeejan kallo haushi sosai yakamata dan jikinta har rawa rawa ya fara wanda tarasa na menene.
Da kyar taci abincin sbd tarin takaicin da Abidan keyi na shigewa Mahmoud shi kuma yana biye mata duk idanuwansa na kan Khadeeja bayan sun gama yayi hamdala hade da yi musu nasiha na su xauna lafiya sannan yace yau zasu raba kwana zai fara daga dakin khadeeja itakam yana gama jawabin tabar wajen dan gaba daya abunda sukai yasa ta nadamar Zuwa falon tun farko gashi ma wai har sun raba kwana kuma wai a dakinta yake.....
0 Comments