f Namiji Baya Kadan 6 to 7

Namiji Baya Kadan 6 to 7


Namiji Baya Kadan  6 to 7


                   Namiji Baya Kadan

Page 6

Juyowa ya kuma yi gareta tare da tsura mata ido, Itama idon ta zuba mai tare da cewa "aha inajin ka" A hankali ya kara rege tafiyar tare da maida hankali shi gareta cikin tsareta da ido yace. "Khadija gobe fa zanyi Aure".

Da sauri ta cilla mai harara tare da tabe baki ta kuma juyo cikin yanayin kai yaro ne tace. "Auren ai ba wasan yara bane kuma ba iya zance bane bare kace ka iya kai yanzu ko nauyin kalmar bakaji ba? Tun da ta fara mgn ya tsura mata ido bakinta kawai yake kallo sai da tai shiru sannan yace.

"Na taba miki irin zancen nanne" Kai ta girgiza sannan ya kara juyowa yana fuskantan ta yace." Toh wallahi ki yarda gobe zanyi Aure insha Allah tare dana Amira za,a daura.

Itama kara juyowa tayi cikin tabe fuska tace."Ya za'ayi na yarda tunda ban taba sanin kana neman Aure ba sannan banji zancen daga bakin manya ba hakazali ka ai da sauran ka ina kai ina Aure shin kama san mene Auren. Fuska ya hade nan da can ya kafeta da ido cikin hade murya yace.




ki shiga taitayinki fa da gaya min duk  mgnar da tazo bakinki wallahi zaki kona kanki ina gaya miki ki kama bakinki da cemin yaro tam. Toh fa Sannu yayana ai kam dole nace yaro kai ba yaron bane, sai ta kuma sa dariya ta nunashi da yatsa sai ta kuma dariya tana fadin. kalle ka fa yaro ko rinka baka faraba bare ka gama wai shine harda wani zakayi Aure Amman dai sai in Yar kauye zaka Aura ko? yar 12 years kai wlh kai kam ma ba wanda zai baka yarsa.

Dariya take sosai tana fadi mai abinda bai sonji. Cikin tunzura ya damko hannu ta ya matse da karfi har saida taji  hannun ya bada sauti das sannan zafi ya ratsata har saida ta zaro ido woje tare da cewa.Wayyo hannuna kai Mahmoud karyani zakayi ka sake min hannu kaji mugunta dan na fadi gaskiya. Shi kuwa ido ya tsura mata sannan ya kara matsota  yana mai piki-piki da ido tuni fuskarsa ta juya kara matsota yayi har kamar zai danneta jikin marfin motar murya na rawa yace.

Wallahi kina jawa kanki fitinar da bazaki iyaba kici gaba da cemin yaro wata ran zakiyi nadama.

 Ita dai hannu daya tasa tana kai da Allah sakar min hannu dan ni ba Sa'ar kabace sai ka jira yar shilan da zaka sauran ita zaka zarewa ido bani ba eh. dariya mugunta yayi sannan ya fizgota saida ta fada jikinshi ya matseta cikin kirjinshi lokaci daya ya fara sake kan mota suna kokarin afkawa cikin ramin.





Ita kuwa cikin jin zafin yadda ya matan da takaici wannan wanne irin rainine ko iskanci hannu tasa ta hankadeshi amman ta kasa kwatar kanta cikin takaicin tace. Me haka Mahmoud ban son iskanci ni Sa'arkace ko rashin kunya zaka nuna min aikin banza yaro dan kaga ana wasa da kai sai kuma raini ya shiga. Kicini ya take ta kwace kanta amman ta kasa sai shi da kanshi ya saketa tare da juyawa ya kalli titi. Habawa ita kam Khadija fada take kamar ta mareshi dan ya cikata tab.

Shi kuwa shiru yayi yana tuki sai zufan da ya keto mai duk da sanyin AC hannu yenshi kab rawa suke. So yake yayi mgn Amman kuma ya kasa bazai iyaba ko yace zai maganar zatake fita da i ina shiyasa sai kawai ya kame lips inshi na k'asa yai ta tsotsa yana jinta tana ta bala'i harda cewa.

Ai kai dole amaka Auren tun baka  jamana abin kunya ba aikin banza aikin wofi.

Shi kam bai kulaba har suka dawa ana bud'e musu gate yana shiga ko parking bai karisa yiba ta kama kokarin bude mota zata fita shiko komawa yayi ya jingina jikin sit sai numfashi yake fiddawa cikin sanyi.

Cikin fada tace."Ka bude min in fita dan ina da abinyi"Cikin wani irin murya yace .

"In in nakifa, ina gaya miki kibini a hankali "sun kuyowa tayi zata dannan pin d'in dan ta bude.




Cikin isa yace."Allah in kika yadda kika tab'ani wallahi zakisha matsa, ba abinda kika iya sai baki ai tida kince ban fara rinka bama bare Na gama, ako bai kamata ki kasa kwace kanki a hannuna ba"Komawa tayi ta zauna danji zai kuma matseta cikin hade fuska tace.

"Wallahi ka bude min banson mgn da kai "Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya bud'e mata tana fita. ta juyo ta watsamai harara tare da Jan tsaki ta juya ta tafi ko kayan bata dauka ba, Shima fita yayi tare da binta yana.

ba laifinki bane Amman time na zuwa zaki bari"A bakin shiga cikin gidan suka hadu dasu Abba da malam Abubakar Na fitowa tare suka dan kauce suka basu hanya tare da gaishesu  mlm Abubakar ya fara amsawa cikin girma yace "Allah ya muku albarka yasa haske a rayuwarku. Tare suka amsa shi oga yasan wacce Addu'ar akayi musu itako ta dauka a matsayin su na yaransune suka musu Addu'ar ga, Suna wucewa Abba yace "kai Mahmoud zonan"
Ita kuwa cikin gida ta shige abita.

Tana shiga parlon Anty ta shiga inda ta samu su Anty da Su Goggo Zahra gasu Aysha dasu Rayhana da Fatima dama duk sunzo Anty Rayhana tana yar fawa Amarya Amira kitso suna ta hira da nishadi tana shiga suka bige da hira suna ta raha, har dare yayi sanyi sannan suka farashirin bacci Fatima ce ta kalli Khadija cikin kula tace."Ni kam Khadija ina dinkin namu kin dawo shiru  kinsan harda nasu Mami da Anty sannan harda na Amarya "Tsaki ta dan ja tare da kwanciya tana dan kulle igiyar rigar baccin ta tace "Kayan suna cikin motar Mahmoud sai goben zai kawosu.




Ajiyar zuciya Anty tayi tare da cewa "har naji tsoro kar bai d'inka ba"Dariya sukayi tare da kwanciya.

Da safe misalin karfe 11 kofar gidan Alhj Ibrahim cike yake mak'il da Al'ummar Annabi manyan mutanen masu fada aji da malamai manya da matasa da yara tako ina a cike ake. Haka kuwa cikin gidama makil yake yan uwa da abokan arziki.

Su Khadija an tasa Amira a gaba dasu Fatima suna ta mata tsiya ita ko tuni ta nemi idannunta. Cikin juyawar iska sautin d'aura Auren _Mahmoud Ibrahim Mahmoud da _ Khadija Sani Mahmoud ya ratsa kunnuwan illahirin mutanen dake cikin gidan cikin mamaki da Al'ajabi aka rinka kallo kallon juna. Cikin sanyi Goggo Zahra dake gefe tace.

Alhamdulillah Allah ya sanya Alkhairi Mahmoudu Allah ya tayaka riko.

Rayhana ce cikin kad'uwa tace."Goggo Wai wanne Mahmoud dinne  yayi Aure kuma da wacce Khadijan. Lokaci daya kuma Aysha ma tace."Nima an daure min kai Wai da gske Mahmoud ne yayi Auren. Mami ce ta fito cikin bakin ciki da  hade fuska da takaici taje gaban Goggo Zahra cikin fushi kamar zatayi kuma tace. fisabilillahi Zahra yayanki yayi mana adalci ace ina Mahmoud ina Aure kuma ko Aure zaiyi ai sai a nema mai dai-dai dashi ina Khadija ina Mahmoud.

Khadija dake gefe cikin mmk da kad'uwa ta zazzaro ido woje tare da dafe kirjinta Murya na rawa tace.Wai me kuke fada ne ban gane kan mgnar ba Wai wacce Khadija kuma wanne Mahmoud din.




Cikin fushi Mami tace "waye kuma in banda ke akwai wata Khadijan ne bayan ke kin juya kokolwan yaro"Anty ma dake gefe cikin mamaki tace "Mami Khadija nanne aka aurawa Mahmoud.

Goggo Zahra ne cikin hade fuska tace" toh haramun ne ko yayuna basu kai suyi ikonsu kan yaran su bane.

Kamo hannu  Khadija tayi cikin kula tace "ki nitsu ki rike mijinki Allah yasa shine mijinki na har abada rabbi yasa sai mutuwa ce zata rabaku. Lokaci daya Hawaye ya ballo mata kamar da bakin kwarya cikin zubda kollah tace. Na shiga uku Goggo Zahra me kuke nufi. Mahmoud k'anina shine kike kirada sunan mijina.

Sai kuma kuka mai karfi ya kofce mata fad'a wa jikin Goggo Zahra tayi cikin kuka mai tsuma rai da kaji kasan zuciyar mai yinshi cike yake da takaici. Cikin kukan ta rike hannun Goggo Zahra ta kalleta fuska duk hawaye tace."Goggo Zahra ase yanzu Dan Allah ya jarabceni da mutuwar Aure sai a maidani tamkar yar kaza Goggo Zahra a rasa Wanda za'a cusamin sai  Mahmoud yaro k'arami Goggo yanzu su Abba ne suka min haka me Na aikata musu da zasu hukuntani da haka.

Cikin bacin rai Anty  da ke gefenta ta yarfa mata mari baki na rawa tace." iyayen naki kike gayawa haka ase basu isa dakeba kenan Khadija ase bazaki iya musu biyeyya ba.





Ita kam Khadija zuwa yanzu duhu ya rufe mata ido lokaci d'aya ta fara jin jiri. Kalaman, Mami yasata ta kara rudewa.

Cewa take "Ji muna furci ai da saninki bake kikace kar a gayawa kowa ba Dan gulma yanzu kice baki saniba.

Cikin kuka tace." Wallahi Mami ban saniba wlh bada yardana akayi ba ".

Sai Kuma ta zame tayi k'asa cikin....top.

Page 7

Bani da lokacin ku bare nace naji zafin zantu kanku a kaina zaginku kanku zai koma abinda na sani baku da damar dakatar dani akan harkar nan na rubuce-rubuce baku isaba dan baku kuka saniba kuma bansa ko wacce karantawa a doleba kuma bazan FASA abin danayi niya ba fans Na muje zuwa ga Mahmoud on top.

Zamewa kan gado tayi tare da kife kanta cikin pillows ta saki kuka mai tsuma rai tana kukanne har numfashinta na fizga, Goggo Zahra yace ta matso kanta cikin sanyi tace.

Haba Khadija Aure fa akayi muku ba zaman banza ba Mahmoud fa dan uwanki ne shin akwai abinda baki sani bane a yanzu ba abinda ya rage face kiyi biyeyya ga Allah da manzonsa  sai kuma kiyiwa iyayenkin da'a kiyiwa mijinki biyeyyah.

Maganar Goggo Zahra kara sata kuka tayi dan ji take kamar wuta take watsa mata in tace Wai Mahmoud mijinta ne tuni fuskarta ta jeme tayi jazir idanta duk sun kumbura lokaci daya muryarta ta disashe har sautin kukan bai fita sosai.

Ayyah Aysha ma sai k'ollah tai ta sharewa dan tasan ba'ayiwa yar uwarta adalciba Anty Rayhana dama mai sanyi ce da tausayin yan uwanta zama gefenta tayi tana.





Ayyah Khadija kibar kukan nan haka zai cutar da ke, Aurene an rigada a d'aura bamu da wani abin yi a kai ni Na fahim ceki, Kiyi hakuri da Abinda Mami tace miki insha Allah itama zata fahimta.

Kanta ta dago cikin muryar kukan tace."Ni na tsani Mahmoud bana kaunar ganin shi sabida ya cuceni ya min karya sannan ya hada min sherri. Fatima dake tsaye gefe cikin jin zafin furu cin da tayi Na cewa ta tsani Mahmoud ta dan ja tsaki tare da cewa.

Toh sai me ki tsaneshin mana ai Uwarsa da mukam muna sonshi. Tana kaiwa nan ta fice abinta. Anty ce ta bita da ido cikin mmk sannan ta kalli Goggo Zahra tace. Ni tsoro naji kar Auren nan ya haddasa mana fitina a family. Mikewa Goggo Zahran tayi cikin cewa. insha Allah sai Alkhairi, Shi kuwa Mahmoud A kofar gida hatta ya Auwal mmk ya rinkyi yana bin kanin nashi da ido shi da zugar abokanshi, shi dai yabar batun Auren Khadija tun randa iyayen Nazir sukazo Abba yace musu, ya mata miji sannan  ya basu hak'uri, ase dama Mahmoud ne mijin.

Shiko Mahmoud Yau itace ranar farin cikinsa gaba daya bakinshi ya kasa rufuwa gashi yayi fita ta alfarma ya fito a Mahmoud on top manyan kaya ya saka harda gare shaddace yar asali kalan sararin samaniya sannan yasa hula fara  sai takalmi shima fari Sai agogon Daimon dake makale a hannu shi farar fatarsa ta taimaka wurin fiddashi gashin kanshi nan duk ya konto ta k'eyarsa sai kamshi yake zubawa yana taku cikin k'asaita sai fatan Alkhairi ake mai hatta manyan mutane sai sumika mai hannu suna mai Addu'ar Allah tayashi riko.

A daya gefen zuciyar Sa kuwa cike take da farga ban ya Khadija zata tsinkayi zancen sannan taya zata fahimce shi  ko me zatace dashi, a hankali kuma sai yaji sanyi inya tuna yadda suka shaku a ganin shi ba zatayi wuyar fahimtar saba. 

Da kyar  ya samu ya zullewa abokanshi sannan ya nufi cikin gida amsa kirani Abba, A parlon shi ya samesu kusan gaba dayansu ya suna parlon gaban Abbanshi ya zauna cikin kula Abba yayi gyaran murya tare  dacewa. Alhamdulillah yau Allah yasa An daura Auren Amira da Amir sannan kuma an d'aura Auren Mahmoud da Khadija wanda nasan kadanne daga cikinku suka san dashi. Abin da nake so ku fahinmta shi Aure nufi ne na Allah haka Allah ya tsara Aure tsakanin Mahmoud da Khadija ba yinmu bane, yin Allah ne, Gaba d'aya shiru sukayi sai Auwal ne ya dan kalli mahaifin nashi tare da cewa. Tohhh Allah dai ya kyauta.





Amin suka amsa baki d'aya, Mami ce ta kalli Mahmoud din cikin hade fuska tace. Mahmoud matsayin na kenan ina mahaifi yarka Amman har kayi neman Aure cikin muna furci duk ban saniba wato kana da wata uwar da tafini ko. Cikin sanyi ya dan ja jikinshi ya matsota kanshi ya dan daura kan cinyarta tareda cirehular kanshi.

Murya a sanyaye yace."Kimin afuwa Mami na Auren ne ya kama ni dole wallahi bazan iya rayuwa ba mata ba ina da buk'atar mace a rayuwa ta shiyasa Mami Na ba boye miki nayi ba Abba ne yace a bari sai Abu ya tabbata sannan kuma kin sani, Annabinmu da kanshi yace A suturta nema a bayyana samu. Duk parlon shiru sukayi duk kunya ta rufe su shiko ko a jikinshi, Haka Abba yai ta musu nasiha har duk suka fahimci illar dake cikin hana shi yin Auren, Shi kuwa Mahmoud cikin rada ya matsota gun Anty Rayhana a hankali yace, Anty Ray ina Matata ban ganta ba hankali na ya bar jikina.

Cikin sanyi itama ta bashi labarin halin da Khadijan ke ciki. Lokaci daya fuskarsa ta sauya shi da kanshi yasan yayiwa Khadynshi laifi gashi bai son bacin ranta, Suna fita parlon kai tsaye cikin gida yayi aiko yan uwa da abokan wasa sukayi caa a kanshi suna, Masha Allah kaga yaro mai kamshin angwaye Mahmoud on top kenan Allah ya sanya Alkhairi ya bada zaman lafaya. Shi kuwa murmushi kawai yake dan yi tare da cewa Amin. Ita kuwa tana jinshi ya shigo parlon Anty ta tashi cikin jin jirin ta rufe kofar sannan ta zame a wurin cikin jin tsanarsa a ranta.

Anty Rayhana tai ta kiranta ta bude taki, Cikin sanyi yace "Anty Ray barta"Sai ya juya ya shiga dakin Mami ananma kanneta sunyi ta mai fatan Alkhairi yayinda wasu ke mai kallon ya d'ebo dala ba gammo.

Ya fita dakinshi ya shige cikin karfin hali ya ja woyarsa  number ta ya tsurawa ido sannan a hankali ya dannan Calling. Ita kuwa tana dakin tayi kukan har ta gaji ta koma ta konta cikin tsiyayar da kollah, A hankali taji woyarta Na suwa bata dagaba har ta tsinke a haka har kusan 5 miss call Sannan ta rinka jin sautin shigar text message a nanne ta jawo woyar tana dubawa tabta shine sai kawai ta saki kuka tare da cillah woyar gefe.

Haka yai ta tura mata text da kiranta Amman taki kulawa, ta kuma kiba bude dakin, har saida la'asar tai sannan Anty tazo tai ta fada tana budewa Anty ta shiga rike da phone dinta cikin fad'a tace."Wai ke meyasa kike da taurin kai ne ya za'ayi mijinki yai ta kira bazaki daga ba har sai yaita kirana. Mika mata woyar tayi tare da cewa "gashi ki karba"Dole ta karba, Tana goge kollah, A hankali tasa a kunne cikin dashewar murya da rawan muryar tace,"Salam"Shi kuwa jin muryarta ya bashi tsoro cikin sanyi ya koma kan 3 stires ya zauna cikin sanyida yanayin lallashi yace,"kiyi hakura Matata ki dena wahal min da zuciyarki da jikinki ki jikaina ki daina min asarar hawayenki kiyiwa mijinki uzuri matata.






Kuka mai cin rai ta kuma saki jin Wai Mahmoud ke kiranta Matata Wai shi kuma mijin ta. Shi kuwa kukan ya kara tunzuroshi baiki ace tana kusa dashiba da ya tabbata zai tsaida kukan.

Cikin lallashi yace."Hayatina  kimin mgn kibar kukan nan". Cikin kukan ganin Anty ta shiga toilet tace." Allah ya isana kuma sai Allah ya saka min ka cuceni".Sai kuma ta katse kiran. Anty Na fita tace "Maza kema shiga kiyi wonka ki fito ki bar kukan nan dan ya isheni haba da mai zanji da habaicin Mami da kanneta ko da kukanki haba Khadija ki tausaya min mana kinsan dai banson kukanki  kalli Nabila yarinya karama itama kin sata kuka har zazzabi ya rufeta.

A haka dai ta sata dole yaje tayi wonka tana fita ta samu su Anty Ray da Fatima har Amarya ita suke jira tazo ta basu kayansu da ta karb'o musu jiya.

Mami ce ta leko cikin fada tace "wai ko baza'a bada  kayan banne, cikin dishewar murya tace." Ayyah Mami kayan suna gun shine fa" Fatima ta karbo mana.

Baki fatiman ta tabe cikin takaici tace."Wallahi bazan kuma zuwa ba naje kusan sau 3 yace bazai bayarba in mun damu kije. Cikin cika da takaici tace. Toh wallahi sai dai mu hak'ura Dan bazan jeba.

Anty ne tace. Ke harda wallahi hinki to wallahi maza mike ki karbo kinaga tun d'azu Amira ta shirya ke ake jira duk wuri ya cika.

Mami ce ta kalleta cikin fada tace "maza fito ki karbo mana"cikin zubda kollah tace, Ayyah Anty kirashi kice Anty Ray zatazo ta karba. Jin tausa yinta yasa ta kirashi yana dagawa sai cewa yayi Anty, Khadija tazo ta karbar muku abinku mana"Haka tasa dole suka sata ta fito ta nufi part dinsu a parlon ta tsaya cikin jin tsanarsa tace"ka fito ka bani kayan"Shi kuwa dama tunda ya ga tana zuwa ta window yayi sauri ya fitar da Nata cikin din kunan sannan ya fitar da saura ya kira Fatima tazo ta karb'a. So tana tsakiyar parlon shi kuma ya shigo parlon ta bayan ta.





Jin motsin mutune a bayanta yasa ta juyo da sauri ganin shi ya sata sai hawaye shar a ranta take cewa yanzu d'an yaron nanne za,ace mijin ta.

Kanta ya nufa itako ganin haka yasa ta rinka Jan baya-baya har ta fada kan 3 stirs A hankali ya zauna gefenta cikin tsura mata ido yasa hannu zai jawota tai maza ta buge hannu  ganin haka yasa cikin isa ya fizgota jikinshi ya matsota a kirjinshi cikin sauke numfashi ya tallabo kanta murya da jikinshi na rawa yasa hannushi ya....

contact-fom

Post a Comment

0 Comments