PAGE 31 TO 40
Ɗakin kaca kaca da kaya gefe ta aje ta cire kayan ta watsar a gefe, tura kayan da ke kan gadon tayi gefe ta hau ta zauna bata damu da tayi wanka ta canja kaya ba, bude takeaway ɗin tayi tafara cin abinta tana danna waya hankalin ta kwance. Washagari tunda sassafe ya tashi nufi gidan Ummien sa,basu tashi ba ya zauna a pallow suna ta hira da Iya mai ma Ummy girki, tun yana yaro suke tare da Iya ke gidan, tana da kirki ga tsafta tare da halin dattako, sam bata nuna kwaɗayi a abinda ba abata ba. Umurni yabata tamai girki yana da marasa lafiya a asbiti baban wai course mate ɗin shi,aiko a mintina ƙalilan ta haɗa musu breakfast, harta gama ya ɗauka ya tafi dashi, su Cutie basu tashi ba.
Abba yafara kai mawa,ya farka amma yana kwance sai bin Aliyu da ido yake ,yana mamaki, yana so ya motsa bakin shi ya tambaye shi ina Jidda amma ba dama sau hawaye. Aliyu aje kwandon yayi jiki na rawa ya ƙarasa jikin gadon yana faɗin,"subhanallah Abba hawaye kuma mai yafaru. Kallo wanda ya kwana da Abba yayi,yace,"ya jikin nasa. Ɗan dattijon gyara zama yayi yace,"alhamdulillah, daya farka na kira Likita ya duba shi, an ƙara mai allura. "Masha Allah ubangiji ya ƙara masa lafiya. "Ameen ya Allah. "Ga abinci nan na kawo ma, zanje in duba ƙanwata da take gida".
Idon ta arufe yake tana kiran Abba. Tani riƙe mata hannuwa tayi tana faɗin sannu Jiddah kin farka. Cike da kulawa take maganan. Muryan da tajine yasata waye manyan idanuwan ta da sukayi mata nauyi. Ganin su Hansai yasa take mamakin,kallo tafara bin ɗakin dashi,daga gani nan ba ƙauyen su bane,ya akayi tazo nan waya kawo ta. Hansai tace, sannu Jidda Kulu bari akira Likita. Da mamaki take kallon Hansai nan asibiti ne to mi ya faru waya kawota nan.
Hansai jiki na rawa taje ta kira Likita suka dawo tare. Dudduba ta yayi, kafin yai mata tambayoyi yace,"ya sunan ki. Ahankali ta buɗe baki tace,"Jiddah. Good yace, yana gyaɗa kai, ya nuna Hansai yace yasunan wannan. Kallonta takai gareta tsawon minti ɗaya, tace," Hansai, wancan kuma Tani duk yan ƙauyen mune, ina Abba na, wake kula dashi ,mai ya kawo ni nan. Aruɗe take magana tana kallon
Dr. Gyara murya yayi yana murmishi yace,
PAGE 41 TO 45
Tani ta taso da hanzari tace,"sannu JIDDA, ya jikin. "Alhamdulillah", ta amsa dashi murya kasa kasa. To to Allah ya ƙaro dama". Amin", ta amsa dashi a taƙaice. Ko akira likitane. Tani ta ƙara tambaya. A temaka min zaki in rama sallolin da ake biyata". Da mamaki Hansai ta riƙe baki ganin karfin hali wai sallah zatayi, ita in tana ciwo ai bata rama sallah, lafiya ƙalau ma bata dameta ba,sai taga idon mutane takeyi, taɓa baki tayi kana daga bisani tace,"to bari intemaka miki, baki bari karnan jikin ki har ya ƙara ƙarfi.
Ta ƙarashe maganan da sigar tambaya. Ahankali ta girgiza kanta,kana tace,"ke Tani inna mutu fa, inje ince ma Allah maine? ince banji sauki ba. Lokaci ɗaya ta jero mata wa yannan tambayoyin. Mamaki Tani take yar ƙaraman yarinya da magana babba, yarinyar nan dai wuni take talla,ya akayi tasan karatun islamiya. Abinda ko ke faruwa, inde Jidda ta ɗau tallan goro da yamma, can gidan fura take tafiya,su suna da yawan islamiyoyi da boko, jikin wata islamiya take zama tana sauraran karatun su, anan duk ta iya abu buwa da yawa,tana sha'awan karatun addini,amma ita talla bazai bari tayi ba,kullum tana ti-ti yawon talla. "Temaka min manaTani".
Da tabari ta shigo ta same ta da icen dalbejiya ta jibga babu mai ce mata kanzil,Allah ya tsine ma Hansai take faÉ—a a zuciyarta. Duk da haka bata saduda ba, jira take ta fita,duk wahalar da aka bata anan sai ta fanshe ajikin JIDDAH.
Uban dame suke tiƙawa a tsakanin su,mutane sun taru ana raba su amma sam basa ji, har yakai da mutane sun koma kallon su. "Shegiya karuwa, karuwan cina yamin rana tunda ni ina iya sayan sabulu kizo ki ɗauke kina wanka". Fadan Atika datake ta huci kamar maciji. "Karuwa gakinan ƙatotuwar ashawo ciki nawa kika zubar. Faɗar Sa'ina da take ƙoƙarin cakumo Atiƙa,dakyar aka shiga tsakanin su,amma basu dena cin mutuncin juna ba da bacin su.
NIKO NACE ALLAH YA WADARAN RAKUMIN DAWA YAKI ƳAƳA.
"Shegiya yar iska ke Saminu da ya kawo dukiyar auren ki, ina ce har ubanshi kike lalata dashi. Fadan Atikah da har yanzun huci take tana zare ƙananun ido irin na uwarta. Mutanan wajan salati suka ɗauka cike da mamaki. Take dambe ya kara kaurewa tsakanin sun suna yaga ma juna kaya. Dakyar aka raba su, akaja Sa'ina akayi waje da ita. Asafiyar ranan ko, kauyen nan labarin su ake lungu da saƙo. Turo ƙofar da akayine yasa dukan su suka ɗago kai.............!
PAGE 46 TO 56
Lokaci dya ta fadada murmushin ta mai nuna alamun tsan tsan farin ciki ganin ta tace,"a'a Hauwa Jidda ce agidan namu yau lalle marhaban, ina Ibrahim din, ki shigo ma kin coge jikin ƙofa kamar baƙuwa". Murmushi tayi tana sunkuyar da kai ta ƙaraso cikin falon ta zauna a ƙasa. Keko Jidda wannan halin naki na ƙauyawan fulani nanan,sai wani noke jiki kikeyi kamar wata kifi. Kwallahiya Ummy. Lafiya lau ya kike, kitashi ki zauna kan kujera. Girgiza kai, Jidda tayi tana tura shi cikin hijjab. " ni wallahi ban san wannan hali, ina Abban naku nagan ki ke kaɗai?.
Share ƙwalla tayi kafin cikin da sha shiyar murya tace,"ina Aliyun ya tsaya. Yana waje yace," zai shigo",ta bata ansa a taƙaice. Aliyu ko yana jikin ƙofa yanajin komai dake wakana,ya turo ƙofar ahankali ya shigo, jikin sa a sanyaye, ko kafin ya ƙaraso tsakiyan pallow Ummy ta ture Cute dake kwance ajikin ta ta rai ɓace tayo kansa, yana dago fuska yaji saukan mari tas tas ke ratsa pallow hagu da dama take marin sa. Jikin Cute na rawa ta ƙara haye wa cikin lallausan kujeran pallow ta tura kanta saƙon kujeran a firgie JIDDA ta miƙe tana zaro ido.
Bata tada gani an doke babba ba a ƙauyen su, gani take in yaro ya girma ya wuce duka, koda ko wani irin laifi yayi, haka take ganin yayan kauyen su suyi ta ma iyayen su raini amma ba mai dukan su, ashe ba haka abin yake ba. Iyah dake hada masu Ummy breakfast da sauri ta aje ta fito pallow tana fadin subuhanallah, lafiya wa ake ma. Turus tayi ta hadiye maganan dake fitowa daga bakin ta ganin Ali zaki ake mari. kasa yayi da kan sa, gaban sa na tsanan ta fadi yana jira kawai tasamu bulala ta fara dukan shi,inde haka zaisa ta huce daga fushin da hau, don ko bijire mata da yayi akan auran Abeeda da wasiyar mahaifin shi da yayi batayi fushi haka ba,ta kauda komi don ta faranta masa ya rabbbb sa'iduni ya furta a zuciyar shi.
Aliyu, ni kake rainawa,ka dauke ni ako da yaushe ba abakin komi ba, banda mahimmanci awajan ka ko,tou wallahi Aliyu ko ban maka baki ba, duniya zata gaya ma, akoda yaushe ba burin ka ka faranta min ba, saide ka ɓata min ko, nagode Allag yasaka maka da alkhairi Allah yama albarka, Allah yabaka abinda kake nema duniya da lahira. Cikin mummunan bacin ran da bai taba sani zata iya ba take maganan, tana kai ƙarshe batare da tabi takan kowa ba dake pallow ta wuce hanyar birthroom din ta.
Daga Iyah har JIDDA suna tsaye cirko cirko, JIDDA cike take da dana sanin da bata gaya ma Ummy ba da tasan ranta zai baci har ta mare shi ta gaya munanan kalamai akan shi. Iyah ko mamaki take mai Aliyu yayi haka da haryasa Hajiya tayi wannan mugun fushin akan sa. Cute ko tana makure waje daya jikin ta har rawa yakeyi. Jidda jiki a sanyaye ta ƙarasa inda yake tsaye dafe da kumatuka da sukayi ja ta duƙa ta ruƙo guywowin sa,wani abu yaji ya ziyar ce shi mai kama da shocking din wutan lantar ki da sauri ya ja baya kirjin sa na tsanan ta bugu. Jikin ta sanyi yayi ahankali ta ta buɗe baki tace........!
0 Comments