f Ashe Kaine Mijina 1 to 10

Ashe Kaine Mijina 1 to 10




Ashe Kaine Mijina 1 to 10

                                                   ASHE KAINE MIJINA 


ASHE KAINE MIJINA  1


Ke nazia kiyi sauri ki tattaro kayanki kizo mu tafi yayanki yana jiranmu, ko walle mu tafi mu barki! ganinan zuwa inna! nazia ta baiwa inna amsa tan a kokarin fitowa daga tadinka da dan gunshin kayanta a hannu, da yar jakarta inna ta kalleta a hantare, kekam kinji haushi Kullum idan za'afita sai an barki, duk zumudin da kike ya zama na banza tunda har na rigaki shiryawa, nazia ta kwashe da dariya, wallahi inna kesan kayana sunada yawa shi yasa ban samu na fito da wuriba, ke dan Allah wuce ki bani guri ko in hantareki, mara kunya, dama haka kike kullum da bakar shiririta. 








Ta kara kwashewa da daria, hadda gaiyatawa, duk wanda yaga nazia a gida idan ya ganta awaje zai dauka ba ita bace, yanda take daure fuska kamar bata taba murmushi ba, zaka dauka kamar ma bata taba dariyaba a rayuwarta, ce tafito da dan gudu gudu tana kallon ko ina idan basuyi Mantuwa ba ta kalle ko ina amma komai babu tafito tana murmushi, yayanta ya kalleta, ke wallahi kinci albarkacin inna da sai mu tafi mu barki kinfi kowa cewa a koma birni amma kuma kinfi kowa shiririta, yayi tsaki, na fashe  da dariya abina na fada jikinsa yi hakuri yayana, yanzu ai gashinan na fito mu tafi ko, amma fa abu daya ya rage min, inna da yaya duk suka juyo suna kallon juna da mamaki, inna tace dama baki kammala ba a'a inna na kare komai amma ai kince inje gidan.

ASHE KAINE MIJINA  2


Amma ai kince inje gidan su abban fatin birni in musu ban kwana, Inna ta saka salati tana tafa hannu, dama nazia da nace kije ki musu sallama bakije kin musu sallama ba, yar duniyar ta kara kyalkyalewa da dariya, amma anyi shakiyiyar yarinya inji inna, ta kawo min duka amma ina na kauce, na kara kyalkyalewa da dariya, mutuniya banza, sai ta ishe mutane da dariya sai kace mai tabin jinnu, yaya ya gama kufula, baice komai ba! Na zabga a guje ina ta dariya, ina shiga dayar kwanar na daure fuska, kamar banice mai kyalkyala dariyannan ba, na gyara hijabina nashiga gidansu hafizin birni mamanshi tana ganina ta hau washe baki, tana min kirarin da ta sabamma ko ajikana nasha magani abina tace auta matar auta, badai tafiyar ceta tashiba, kamar banason magana na kebe baki nace, yar nan Allah ya kaiku ya lafiya gashi sameer baya nan da sai in ce ya baki number yayannaki nura idan kunje sai ku nemishi ku rika kaisawa, bance mata komai ba, ta kare surutanta, nace zamu wuce su yaya hafizu suna jirana, tace to yarnan Allah ya miki albarka, ta bani kudi wai insha ruwa a hanya amma nakin karba, nace ina fati take? Allah sarki bata dawo makaranta ba idan tadawo zan fada mata kun tafi, zatayi kewa Wallahi zan wuce yarnan bazaki karbi kudin ba nagode hajiya, dama itama ta sanni da taurin kai aranta take
cewa tauri da tauri sai kaka.


ASHE KAINE MIJINA  3



Sai kaka, koda na karaso na tarar da an kulle gidan mu kuma ba motar yayaba labarinta. Tuni hanjin cikina suka shiga kadawa idona suka cika fall da hawaye sai kuka, yanzu su yaya da inna sun tafi barni, kuka Sosai nakeyi na zauna daram a kofar gidan mu na rufe ido ina kuka, maimakon indan zagaya amma anan na dabe ina kuka, sai ji nayi ankwasheni da mari ta gefen fuskanta! Kutumar uba waye yake dukana duk da ina cikin kunci amma dabala na dago kai inga wane dan iska ne yake dukana.










 Daga kan da zanyi sai kawai naga yaya, fuskar nan a turnuke kamar an aiko mishi mutuwa, wallahi idan baki tashi mun wuce ba zan babbalaki anan, mamaki da tsoro ya cikani, araina nace su tafi su barni sannan kuma yazo yana dukana da zagi, araina na fara balle na daure fuska, ashe nice banida kai mota gatachangaban gidan mu kadan kwana sukayi suna jirana, da yake ni idan ina tafiyan bana kage sai ban hango motar ba, na kuwa sha kunu na fuske abina, ya shiga gaba ina bin bayanshi saida muka isa jikin mota naja na tsaya, kamin kace kwabo inna ta wankeni da wani marin, ta buda baki zatayi magana na rigata nashiga uku, nace minayi muku kukeson ku kasheni,sai inna ta shige mota ta barni, naci gaba dan kunga ina zumudin zuwa birnin ne ake min wulakanci, to Wallahi na fasa zuwa birnin banaso, bazanjeba asaukemin kayana ba inda zanje, na kara fashewa da wani kuka yaya ko kallona baiyiba shima ya zagaya ya shiga mota ya kunna yana jiran inshiga amma ina taurin kai ya motsa ko ajikina, yayi horn alamar in shiga amma ina sai ya fito.


ASHE KAINE MIJINA 4


sai ya fito, kinsan Allah nazia idan baki wuce muka tafi ba zan babbalaki yanzu nan, ko kallonsa banyiba, na kauda kaina gefe, yaga da gaske nake yakaimin duka, ko in kauce na tsaya qiqam mugun halin ya mosta hakan ya qara bashi haushi, dama shima gwanine a gun zuciya amma dai bai kaini ba, yafara dukana har na fadi yasa kafa yayi ball dani, hankakin Inna ya tashi tasan idan zai kasheni a gurinnan ba tashi zanyiba, kuma tunda nace bazan jeba ba tafiyar zanyiba, tazo ta janye yaya hafeez daga gareni, ba halin tamishi fada yanda taga ya chanza har fuskarshi tayi ja dan tsananin fushi,da yake shi yaya hafeez fari ne Sosai ko kunya yaji sai kaga yayi ja, haka lokacin sanyi ma ja yakeyi, uwa uba idan yayi fushi sai yayi jaa kamarbature haka yake, tayi gefe dashi ta daura hannunta akan kafadar shi ta dama, haba yaya! Ya zaka biyewa nazia.










Yarinyar da ba hankali ya ishetaba, kuma sam batasan ciwon kantaba, wuce ka shiga mota bari in daukota, yayimini wani mugun kallo, rai a bace ya shiga mota yana huci "nima dai m. jabo da nake biye dasu ya bani tsoro dan nayi niyyar in gudu sai mun hadu birni amma dai nayi ta maza na tsaya" inna tazo ta durkusa kusa dani, tace ba tafiya mukayiba kinsan haryar karamace shine sai yayanki yace bari muyikwana kamin kizo shi yasa baki hango muba kuma ke gashi bakya kallon hanyakina zuwa baki ganmu ba maimakon ki duba gefenki sai kawai kika nemi gurikika zauna kika fara kuka, abin ya bani haushi ne dan kada yayanki yace na goyi bayan ki shi yasa nima na dakeke amma nima raina baiso ba, haba autan inna kuka ba naki bane kinga kin bata wa yayanki lokaci kusan awabiyu fa muna jiran ki kuma ya gayamana yanada aiki kuma duk ke kika janyoaraina.

ASHE KAINE MIJINA 5


Araina naji dadi ko banza na bata masa Lokaci, amma kuma naji jiki, Lallainice banida gaskiya sabida ina zuwa kawai banga motaba sai na zauna na farakuka, kuma ni kaina nasan ba yanda za'ayi su tafi su barni, wauta ce takedamuna ko qauyanci? na bude baki cike da yawu da jini na zubar da yawun gefen inna, inna da taga jini hankalinta ya kara tashi, maimakon in sassautoin lallaba in tashi mutafi sai na fuske, "kamar jabo tayi rashin kunya ta
fuske" ina sheshe kar kuna bace inna ba inda zani na fasa tafiya,birnin banza, dan yagainason inje birni ne shi isa yake min wulakanci, yanzu kuma nafasa zuwa asaukemin kayana, ashe yaya yana jina, da karfi ya fito motar ya bude bayan motar motar ya ciromin kayana ya jefini dasu kikaji jakar timmn akaina, tabbas wannan yafi dukan da yamin konan rai, inna ta kalleshi, tadaure fuska, ashe bakada hankali. Mukayi kenan? to sai ka fito min da nawa kayan nima ba zaniba, tunda abin naku rainin hankaline, hankalin yaya yatashi, nima dai naji tsoro kuma naji kunya, ya durkusa inna, kamin shiruka fito min da kayana nace ba zaniba ko dolene, narasa yanda zanyi akaina ake mishi fada kuma nice banida gaskiya ga uban taurin kai, ya juyo gurina nazia dan Allah kiyi hakuri, na sunkuyar dakai banji dadin abinda na masa ba. Itama inna taga rashin da cewar hakan abu ya hade masa biyu ta mike tsayeke nazia tashi ki shiga mota kaima wuce mu tafi sumui sumui kamar munafuk
a na mike zan dauki jakar kayana yaya ya karba inna tace sake mata kayanta ta dauka da kanta, Lallai ban kyautaba kuma duk ni na janyo amma.


ASHE KAINE MIJINA 6


Amma ya zanyi fuskewa kawai zan cigaba dayi yaya yashiga mota nima nashiga, nasani sarai idan akwai abinda ya tsana baifi ashiga bayan mota a barshi shi kadai a gaba ba, na kuwa fuske nabi Inna baya, ya kalleni irin kallon tausayi muka hada ido amma na fuske abina, na bude baya zan zauna. Inna tace nan kika saba zama Sumui sumui naje gaba na zauna, yaja mota sai sakwato birnin shehu, sokoto garin dan fodiyyo garin karamci karin 
mutumci, garin dattako, garin kashe kunya, na jinjina muku sakwatawa, Allah ya barmu da kaunar ma'aiki. 











Tunda muka shigo nake raba ido sabida karin yamin, Gaskiya karin yanada kyau da tsabta, sai kalle kalle nake sabida tunda nake ban taba zuwa sokoto ba sai yau, rabona da sokoto tun ina shan nonon innata, haka kawai najihawaye suna saukomin, Lallai ban kyautawa yayaba! Na mishi butulci Sosai, shine wanda Kullum burinsa ganin farin cikina! Shine Kullum burinsa farantawa mahaifiyata. Muna kauye amma ba wanda zai kirani da ba kauya! Bawanda zai rainani, a kauyen mu nice gwana, nice yar gayu, nice kowa yakeso, kuma duk albarkacin yayanane, yanzu haka da na shigo cikin birni duk yan matan da na rika hangowa a mota, ba ko wacce na gani da irin tufafinaba, sai daidai ku,  yaya yayi ta fadamin tufafin da yake min ai na manyan matane dinkin ma haka, tufafina masu tsada na yayan masu kudi amma shine zan yiwa butulci irin wannan gaskiya dole in.

 ASHE KAINE MIJINA 7


Dole in bashi hakuri, na dan faki ido na kalleshi, sai ya kara bani tausayi, matuka narasa irin halina, tun bayan rasuwar mahaifin mu munsha wahalar duniya, wanda daga baya yaya yana karatu yana bin motar daukar kayan gwari irinsu ayaba da lemo da mangoro, duk dai wani fruits da ake yayi, haka zasu loda cikin mota idan sun isa gari sai su sauke, ana biyansu, kuma hakan yake karatu yana wannan sana'ar har ya kare secondary anan mai gari ya dauki nauyinsa da yake mai karin mu abokin marigayi babane, ya dauki nauyinsa yaje dan fodiyyo sok anan yayi digree na farko yana kammalawa yafara karantar wa a sokoto cement primary anan dai ya sami kudin shiga Sosai har ya ci gaba da karatunsa, duk albashinsa akan mu yake karewa sabidayaya mutum ne mai zuciyan yi kuma yanada son fitarda kanshi dama wani nashi kunya shi isa tun yana karami da yake dako kayan kwalliya ina dasu komai yana siyamin har na tasa nadan girma, kuma sam bashida kyashi duk abinda ya samu inna da nazia. Mu biyu muke a gurin mahaifin mu ni da yaya, mahaifin mu ma'aikacin prison ne yana gadi a sokoto prison a wani rikici da akayi a gidan yari aka harbeshi anan Allah ya karbi ranshi, tun daganan muka dawo kauyen mahaifiyata da zama tun ina shan nono atakaice dai bansan mahaifinaba.

ASHE KAINE MIJINA 8


Bansan mahaifinaba sai yaya da inna stakanina da yaya shekara takwas ne, sabida inna tace har ta daina tunanin haihuwa sai ta sami cikina ta haifeni, yaya na matukar sona kamar shine babana, bansan wahalar rayuwaba sam. Ki fito mun iso naji ya fada cikin sassanyar murya, tausayinsa ya kara kamani, ban san lokacin da na masa murmushiba, amma sam fuskar sa bata kaina, gidan da na gani ya tsoratani, wani facecen gidane, da gate yayaya bude, muka shiga, naga ikon Allah araina nace a cikin wannan gidan zamu zauna, sabida ko a mafarki ban taba ganina a iran wannan gidan ba, gidane bangare biyu ban gare daya an kammala ginin dayan bankaren kuma ba'a kammalaba amma wanchan bangaren da ba'a kammalaba yafi bankaren mu girma, muka shiga, muna shiga na tabbatar da yaya yamin gatan da yake fadarzai mini, naga so da kaunar da yace zai nuna mini, tabbas nayi sa'ar dan uwa, wasu hawaye suka sake zubomin, yaya ya shigo da kayan mu, ya nunamin dakina komai a tsare hattana kayan make up an saka min toilet dinasai wanda ya gani dakin inna ma haka komai tsab an gyara, sai dayan dakin da ya nuna mana na baki, ya nuna ma inna kitchen da kayan abinci da komai a ciki duk da tana daure masa fuska yana mata bayanin komai nima yam
in bayanin komai amma yaki bari mu hada ido yayi waya ya.


ASHE KAINE MIJINA 9


Yayi waya yace aturo yaron sun iso, almajiri ya nema mana wanda zai rikamana cefane da sauransu, ya baiwa inna kudi kamar yanda ya saba sai kawaiyace sai anjima ya fita, nida inna mukayi jugum jugum sabon gida sabuwarrayuwa, Lallai yaya ya cika min alkawarina, sabida ya kawo ni birni kamar yanda kullum nake cewa inason akawoni birni gurin mijina, yau gani a birni a birnin ma sokoto birnin shehu, gari mai kyau kuma gida mai kyau, in kalli inna ina tsoron in mata magana naga ta daure fuska, sai na tashinashige dakina, nayita kalle kalle, komai a tsare kuma tasaba dai dai da bukatar duk wani dan birni, hotona dana yaya da inna munyi kyau Sosai anyi babban frame dinsa an kafa a dakina, nayi kyau a hoton yarinta na a fuskakarara amma bai hana kyauna fitowa ba, yar karamar fuskata da manyan idanuwana das dasu, gaskiya nayi kyau a hoton, na zauna jigum, saina fara tunanin kawayena na kauye fatima yarin yayar nura ce duk kauyen mu ita kadai tamu tazo da ita sabida itama yar gayuce iyayenta suna birniamma ita tana kauye abinta, nura shine wanda tun da mahaifiyata ta sami cikina yace idan mace aka haifa matarshi ce, kuwa akayi tunda aka haifeni ya ke sona ana cemin matar nura, mamanshi takance dani auta matar auta, tun inada shekara uku, ya koma birni gurin yayanshi baban fatima kawataban kara ganinsa ba har yanzu da nakeda shekera 14 a duniya.

ASHE KAINE MIJINA 10


Shekara 14 A duniya, tun ina cewa a kaini birni gurin mijina har na dainada na fara wayo na fahimci ba sona yake ba, lamarin kauye ne kawai, gashikuwa mahaifina yace bai yarda in auri wani idan bashiba, kuma kowa ya san ni matar nura ce, amma nura sam bai damu da harkataba, bai damu daniba, ko kauye yaje gurin mamarshi baya kwana ranar da yaje ranar yake dawowaban taba kaninsaba sai dai yakan yomin tsaraba tuli tuli, nida fatima, da alama ma iyayen fatimar ne suke min siyayyar, sabida komai iri dayane nida ita, shi isa shima yayana komai iri daya yake mana da ita, Allah sarki fatima ko Yaushe zamu kara haduwa gashi tace zata bani address din kanwar ta idan nazo birni muyi kawance amma nazo tana skull ina cikin wannan tunanin sai naji kiran inna natashi naje, kizo ki hada mana abinci idan kin iya nidai kam ban iya aiki da gas cooker ba, nace nima ban iyaba, nadauki a shana naje gurin da ake wancan ginin na tattaro itace na hura wutana mana girki, muka danne abinmu, har lokacin fuskar inna a daure take narasa yanda zanyi in bata haquri sai bayan magarib yaya ya dawo yashigo da ledodi dayar ledar tablet ce da kuma wayoyo guda biyu, ya bani tab din ya hadamin da wayar, da sim itama inna ya bata wayar ya nuna min yanda akekunnawa da kashewa da Sauran abubuwan duk dai fuskar shi ba yabo ba fall
asa amma yaki bari mu hada ido yace zancen school dinki gobe zan kaiki mak
arantar da zakiyi karatu sai kiganta dama anyi komai kaiki kawai za'ayi...?



contact-form

Post a Comment

1 Comments

pallasoberhaus said…
Play free games online at Mapyro Casino
Enjoy 서울특별 출장마사지 free casino games online from Mapyro. 바카라 사이트 Choose from a 울산광역 출장마사지 variety of top games, including slots, table games and 보령 출장마사지 video poker. You can 광명 출장샵 also find other