f Ashe Kaine Mijina 11 to 21

Ashe Kaine Mijina 11 to 21

 

Ashe Kaine Mijina 11 to 21


   Ashe Kaina Mijina

ASHE KAINE MIJINA 11

Za'ayi, naji dadi Sosai a raina da jin zancen makaranta sabida har nakai jss3 nayi kawai aka shigo da zancen birni, yaya ya juyo gun inna ya sassauta murya, ya fara baiwa inna hakuri abinda ya faru dazu da safe, inna tace ba komai nima nan na Sami dama na bashi hakurin rashin ta idon da na masa, dan uwa rabin jiki aka yafi juna muka dawo kamar yanda muke ada, farin cikina ya karu ganin cewa yaya na da innata sun daina fushi dani, duk mun saki jiki kamar ba'abinda ya faru da safe har na bama da yaya lab arin yanda mukayi girki, yasha dariya, karshe yace za'asamo wa inna wacce zata tayata zama da aikace aikace tunda ni makaran zan rika zuwa, dakyar dai inna ta amince da mai tayata zama, mun shiga kitchen yaya ya nuna min yanda ake amfani da komai, mukaje bayi yanuna min yanda ake komai da komai, munyi hira Sosai dashi daga bisani ya wuce dakinsa nima nabi inna da kinta dan nasan bazan iya kwana ni kadaiba, naje muka fara hira nida inna ta, acikin hirarta dai ta hada da wa'azi, ta qara jan hankalina akan zafin rai irin nawa, taja kunnena akan yanzu nashigo wata sabuwar rayuwa mutane daban komai daban so dole sai na san yanda zan riqa hulda da mutane.








Kuma ta ja min kunne daga yin mugayen kawaye, da kama kai kada in rika shishigi ga wayanda suka fi karfina, in kama mutuncina insan cewa ni ba kowa bace, ta kare muka dauko waya na nuna mata iya abinda na gane nasan kuma zata kane, ni kuma nahau daddana tawa ina kara fahimtar abubuwa, haka dai har bacci mai nauyi ya daukeni nabar inna tana.

ASHE KAINE MIJINA - 12

Nabar inna tana ta kallon wayarta,dama tunda asuba yaya yace in shirya zai wuce aiki yanason ya kaini skull,din mu ai ko dan kada amaimata dan gidan jiya tun asuba ban koma bacci ba, bayan mun kare break fast muka dauki hanyan makarantar daza'akaini, tun daga nesa na hango hadaddun motoci suna sauke yaransu, nasan cewa wannan skull din ta well to do ce, araina nace yaya ya kawoni gurin yayan masu kudi, tun bamu isa admn block ba na ba na fahimci wasu yara yan mata suna ta kallona suna dariya, araina naceko dai sun gane cewa daga kauye nake, haka na fuske abina, sabida nasan ba nida munin da za'amin dariya, haka ni bana tafiya bazar bazar " kamar zainab khalifa princess zainab" bare ince na kwafsa, to dai haka har muka iso admin block ina tunane tunane, matsalar farko dana fuskanta rashin iya speakd a English , ina gane duk abinda ake fada amma bana iya bada amsa, shimad ai da ni dakikiyace da dan karatun kauye ba abinda zan iya yaya ya bada.

A dina daya karbo a qauyenmu, akamin interview dagyar dai suka aminta na zauna jss3 maimakon ss1 da zanje, shima jss3 din saida yaya ya dage dan jss1 sukaso su kaini tunda bana iya magana da English, admn off ya kira wana yarinya yace ta nunamin clss dinmu, ta kuwa nunamin nashiga nayi sallama da yaya, na wuce clss Lallai sabuwar rayuwa da mutane kala kala, abinda yafi bani haushi kallona da suke suna dariya na kare musu kallo ba wacce takaini ko kyau bare.....?

ASHE KAINE MIJINA - 13

Takaini kyau bare suce ni mummunace, Lokaci daya naji na tsanesu dukan suna tsani rayuwar birni ma, ina tsoron in musu magana akan dariyar da su ke min in gudun su faramin turancin iskanci dan na kula ba wanda yake Hausa cikin su, haka na kama mutuncina, na zauna a clss din a kuntace ba dadin rai har aka tashi break fast, sai yanzu na tuna yaya bai bani ko gwandalaba, Kuma gashi banzo da wayataba, haka dai na zauna idona sukayi rau rau, kamar zanyi kuka, ina zaune ni kadai wata yarinya tashigo ga dukkan alamu na girmeta, sister bissimillah ko, nidan bansan miye takeshaba dan yaya baitaba kawo mana irin abin ba, nayi murmushin dole, no na gode, tayi dariya ai wallahi saikinci, ta bani dariya yanayin rigimarta kamar fatimata ta kauye,kuma ga kama da sukayi da fatimar nace a'a ina azumine da yake yau.










Monday da mizai hana in siyo nima inci, ta kwashe da dariya, nada uka ta gane qaryar dana sharamatane, ta kalleni kice dai kawar tawa malamace, araina nace yaushe na zama kawarki haduwar minti biyu, ta kalkeni sunan khadija, Muhammad, ana kirana da sister kaduna, amma fili na maimata sunanta sister kaduna, tace of course, ko sunan ba dadine, nayi murmushi araina nace kada ta faramin turancin banza,Aah da dadi mana inason in zabi wanda zan kiraki dashine, tayi murmushi da yake ta cika baki da cake, ke ya sunanki, sunana nazia Muhammad, itama ta mimaita sunan, yadai, no kamar na tabajin sunan ne a wani guri amma na manta, nikuma araina nace nikam a gurin fatima ce naji sunan ki sista kd , nice to meat you, nace thanks, na kasa daurewa nace nihal dan Allah miyasa tunda nazo sukemin dariyane? Itama tayi dariya tace sabida kin.....?

ASHE KAINE MIJINA - 14

Sabida kin saka sababbin kaya baki musu iron ba, kinsan fa yanzu an waye an ci gaba, ba yanda za'ayi ka saka sababbin kaya baka musu iron ba, ana ganinka za'agane kuma sai a maka dariya, shi isa kikaga suna dariya, amma kada ki damu gobe idan zakizo sai koyi kokari kiyi iron din uniform dinki kamin kizo, araina nace da yake su yan birni yan iskane ba dole suma mara iron dariya, a fili nayi murmushi, na kalli kayana na tabbatar da cewa da gani an san sababbine, sai na fuske, na basar da maganar, munanan har yara suka dawo break, malami ya shigo aka gaidashi anan yake tambayata ni bakuwace nace eh, sauran yan clss sai dariya sukemin, araina nace wato rainin wayon hadda malamai akeyinsa, tun lokacin nayi marking din S/S master, hadda shi a yiwa students rainin wayo, haka dai har aka tashi makaranta zuciyata cike da qunci da tsanar birni da mutanen birni, bayan an tashima saida naga tasku, sabida kowa anzo an daukeshi, wasu kuma skull bus take kaisu, ni kuwa bansan ko inaba bare inje kuma bansan kowaba, haka na zauna jikin gate har 3:30 sannan yaya yazo ya daukeni, sister ya karatun dai? Ya naga fuskarki ba annuri ko skull din bata miki ba, Na turo baki wallahi yaya ba skull din bace students dinne basuda kirki, hakafa duk inda na wuce sunamin dariya, wai banyi iron ba shima ya kalleni ya kwashe da dariya, au hadda kai yaya! to ke sister ai dole a miki dariya kin saka kaya haka kamar....?

ASHE KAINE MIJINA - 15

Kamar wata zainab khalife ba tsari ba komai, ban san lokacin da na kyalkyale da dariyaba, wallahi yaya ka raina zainab khalifa, kuma ita ganin kanta takeyi wayayyiya tunda ta zauna kasar waje,har ma yanda takejin da yaruka kala kala, ki barta shirmen banza takeyi, ni haushi take bani, kinsan yanzu wani abokina takeso, Na gyalgyale da dariya, wallahi yaya duk sai na gayawa gwagwo sharrin da kake yiwa yarta, ya harareni, kefa matsalar ki kenan yanzu sai kije ki fada, Sosai kuwa sai in fada mata kana tsinar mata ya, to ai abokiyar wasan muce, gwago ba abinda zatayi, Kullum dah aka kake fakewa kana zagar mata ya.










Da hirar zainb khalifa "presences zainab" muka iso gida, ina abincina yunwa nakeji, yaya yayi salati, sorry sister Wallahi sam na manta ban baki kudin break ba, mi kikaci, Nayi mumushi.! Banci komai ba hasali ma da wata sis kadee ta min tayi cewa nayi azumi nakeyi, Yaya ya zagayo ya dafa kaina, kiyi haquri sister Allah namanta sam.! Laa yaya ba komai fa, ai nasan mantawakayi idan ba mantuwa ba ba yanda zaka barni da yunwa, yauwa kici abinci ki huta anjima zamu je day to day shopping, idan kin kammala ki kirani.....?

ASHE KAINE MIJINA - 16

Kammala ki kirani a waya sai muje ko, Ina kokarin dura lomar a bakina nacemishi to yaya, ya wuce, nici gaba da chin abincina ina baiwa innata labarin rashin kirkin yan makarantamu, da kuma qawar da nayi sister khadee, da kuma tsinar da yaya ya rika yiwa Zainb khalifa a mota, inna itama dariya tamun, ai sai na hada yayanki aure da zainb khalifa muga karshe tsiya, na kyalkyale da dariya, wallahi kema kinsan inna zakisa kawai ya qara tsanartane,dama haushinta yakeji, Allah sarki zainb nifa bana ganin abinda yaya yakecewa tana dashi, kawai tanada dan Rawan kaine, inna tace nidai ba ruwana,nayi murmushi, muna chin abinci muna hira har na kammala, inna bari inje in danyi bacci, inna ki tayar dani 4:30 please, to Allah yakaimu,Kamin biyar dagani har yaya mun gama shiryawa, har munshiga mota muka dauki hanya sai DAY TO DAY, gurin ya hadu Sosai, super market ne hade da rest aurant da kuma park a gurin, nidai kam fuskewa nayi kada a gane sabon shigace ni,amma Lallai gurin ya burgeni matuka na sha magani ga shigar da nayi nasan karyar yan birni Su nunan dressing, ina tsosta minti na a hankali, irin nima yar birnin nan dan na kula birni yan rainin wayone Sai Su nemi Su min dariya wannan karon kuwa na shirya chin uban Su, "ni jabo araina nace kaji naziah da zuwa birni Sai xancen cin uba"....?

ASHE KAINE MIJINA - 17

Munshiga day to day, munyi shopping, kayan make up, ba kara kwasowa da turaruka kala kala da Su chocolate ba abinda bai siyamin ba, muna fitowa cikin ikon Allah na hadu da Sister khadee sunzo siyayyah,itada wani hand someguy, araina nace kafa.

Dai Saurayinta ne, dan yanayin yanda naga yana batakulawa ko motsi tayi a kan idon sa sai kuma Suka burgeni, wannanshine ammar shi zan aura Insha Allah, ta wani lumshe ido ta kalle shi, shi ko wawan Sai murmushi yake, tace wannan fa ko dai shine angon namu,tuni yaya ya daure fuska, na kalli yaya naga yasha magani no yayane faT, a dan sosa kai irin taji kunyar nan, ta gaida yaya na gaya ma yaya itace wacce ta min mutunci suka gaisa da yaya, yadan saki rai, mu dan kebe da ita ke mutuniyar ai na dauka wannan kamu kikayi guy haka har guy, kina tare da ammar dinki kina kallon wani, tayi dariya aike ba'a tsayawa guri daya ne, har na fara joules naga saurayinki zaifi my ammar, mita gani kuma tace kai ammar dina fa karkene araina nace wannan yarinya da saurin sabo take, muka danyi tadi muka sha ice cream tare daga baya mukayi sallama muka wuce, muka dawo gida cike da farinciki.

Kwanaki sun shude, watanni sun haura shekaru sun jaa kaba, nida sister khee mun zama daya, mun zama qawayen juna, fiye da tunanin mutum dan kuwa komin ta yayi kama dana fatima na, mun zama abinda muka zama a skull, amma nafita wayo, duk wani neman magana ni nake turata tanayi amma ita bata ganewa kuma bata ganeba, idan akazo in fuske a mata bulalarta, koda tace ni na turata ba wanda yake yarda sabida kowa yana min kallon waliyiya dan ba mai ganin koda murmushi na bayan ita.








Duk wannan shaquwar tamu da nihal kusan shekara biyu amma tunda nake saudaya na taba zuwa gidansu, sabida yaya baya bari, hattana qawaye baya bari inayi barkatai, bare zancen samari, Nihal ta roqi yaya da kanta, akan ya barni inje gidansu, haka kuwa akayi yaya ya barni amma bazai kainiba sai dai in shiga motar kasuwa sabida yana da aiki sosai a office, ban damuba coz inason fita, na shirya tsab na musu tsaraba, na nemi motarda zata kaini unguwarsu, saida na fito na fuskanci garin akwai hadari sosai, na sami mota na shiga sai unguwarsu nihal, kofar rini.....?

ASHE KAINE MIJINA - 18

Unguwar su sis khadee kofar rini, ina isowa unguwar hadari ya fara tasowa tare da iska, duk wanda yasan hadarin Sokoto yasan yanda yake da iska maihade da qasa a ciki, idona suka cika da qasa, har bana ganin gabana sosai, unguwar ba kowa, tayi shiru sai qarar itace da suke kadawa kakeji, kowa ya shige gidansa, iska akeyi sam bana ganin gabana, sai samun kaina nayicikin katon ramin kwata tsundum, Subahanallahi, na fara swimming a kwata,mai uban wari ga kaina da ya bugu, haba ga ruwan sama an farayi kuma da karfi, na tabbatar da idan ruwannan sukafi haka karfi wucewa zasuyi dani, na tabbatarda kuma mutuwa ta tazo, dagyar Allah ya taimakeni na fito ramin nan, ruwa kamar da bakin gwarya, na fito amma na baro jakata jikin kwata, kuma gashi tace idan na iso in kirata, dan ban gane kwatancen da tamini ba gashi wayar na cikin jaka, jaka kuma na cikin kwata, sai kaka.

Ga ciwon kai buguwar da nayi, nasan ba tazin da zata daukeni haka dame dame da kwata in bata mishi mota, nasan ko na sami mota banida ko kwandala, haka naja jiki na rabe jikin gate din wani gida, ina tsaye sai ga wata motatazo music ne yake tashi sosai, saida suka iso kusa dani suka tsaya suka kwashe da dariya, nadago na kallesu, bance komai ba ba bakin musu tsiya, sukayi horn aka bude musu suka shiga gidan, araina nace dole in bar nan gurinDan yaran gidannan da alama basuda kirki dagani yan iskane, na duba gabas da yamma ba mafaka sai nan, sai kawai na haqura har a kare ruwan kunyar duniya ta isheni, jikina duk kwata, ga ciwon kai ya tsananta har na kasa tsayuwa na tsuguna, ruwa yaki zakaitawa sai.

ASHE KAINE MIJINA - 19

Yaki tsaqaitawa Sai na yanke shawarar bari in daure in dan shiga ruwannanidan kwatar jikina ta wanke, my be zan samun abin hawa, na miqe kenan kawai sai jiri ya kwasheni na fadi a gurin sumammiya, kaina ya kara bugun gate din gidan,kikaji gwall, maigadi ya fito ya ganni a hakan ya shiga ya kira matar sa aka taimaka masa ya shigo dani daga ciki, shida matarshisuka taimakamin har na farfado na dawo hayyacina, amma bana gane komai kuma ban san inda nake ba, matar ta ciremin kayan kwata ta daurayemin jikina ta saka min wasu tsummakaronta,ta bani dan paracetamol da panadol na kora, bayan kamar awa biyu na fara farfadowa, na gane inda nake, suka tambaya ayeni sunana da komai na musu bayani, muna cikin magana najiyo muryar sister da wani namiji a waje.










Uncle wallahi tun kamin afara ruwa tacemin ta fito, gida, kuma batasan nan gidan ba, na kira wayanta yafi sau dubu baya shiga, kataimakeni dan allahuncle, kinsan Allah, wallahi ba inda zani gwanda ma ki haqura ki kama kanki ke idan ma kika qara min maganar wata anan sai na babbalaki.

Tabbas muryar nihal ce kuma ni take nema, nace ma matar maigadi, gurin waccan yarinyar nazo, tanajin haka tayi wuf ta tashi, ta qwala mata kira, sister khadija.! Sister khade!! Ko ta waigo ta wuce abinta, sista khadi kizo ga nazia anan, ba shiri ta waigo ba shiri ina take rabi....?

ASHE KAINE MIJINA - 20

Ina take rabi, Gatachan dakina, mi takeyi a dakin ki kuma da gudu ta qarasa, tana ganinata rungumeni, duk da warin kwatar bai saki gashinaba, amma haka ta rungum eni tana kuka,kin bani wahala naziah, ta janyo hannuna muka shiga daga cikin gidansu, dagyar nake tafiya, ga sanyin da nakeji, mun shiga gidan kenan, bamu kai parlour ba naji murya daga baya ke ina kika samo wannan almajirar.

Sis khade dai kam ko waigowa batayiba bare ta bashi amsa,! Yaci gaba da magane, ke badake nakeba, wallahi idan nazo gurinnan sai na babballaki, habauncle ba girmankabane wannan abin da kakeyi, da talaka da mai kudi duk Allah yayisu,kuma ai wannan naziah dina ce fa.!! Kece naxoon taki almajirace amma kuma akwai diri, dayake duk kayan sun manne min a jiki shape dina ya fito, najuyo na kallashe, fitsarar ta motsa na kalleshi daga sama har kasa na zubar, na hada da tsaki, sis khadee ta kalleni, haba nazia, kanin abbanmunefa, na fuske ko qanin abbankune ai baisan darajar mutaneba, koma miye ai uncle dinane, kamin ta rufe baki tuni naji saukar mari a fuskarta kamin in ga waye nima ya kwasheni da nawa marin guda biyu lafiyayyu, saida na gigice, cowon kai ya karu na bude ido naganshi gabana tsaye, kuuuut idanna barshi Lallai ya daki banza, nima nasa hannu na kwasheshi da irin nashi marin guda biyu lafiyayyu.....?

ASHE KAINE MIJINA - 21

Mamaki ya kama sista khade, taga yanda na mari ganin mahaifinta, wanda yake ji da ita, kuma a gabanta a gidansu! Lallai koda uncle ne bahida gaskiya dole ta nuna ma naziah kuskurenta dan gaba...!! Sistet khade ta kalli nazia tace, ke dama yar akuyace, Wacce batasan darajar na gaba da itaba, Wallahi da nasan ke butuluce da bazan taba qawance da yar qauye irinkiba, Mamakin duniya ya cika nazia dama haka sista khade take mara mutunci to ba gyaleta zanyiba, wata zuciyar tace ki gyaleta gidansu kikazo, sista khadaji sai masifa takeyi, inda take shiga ba nan take fitaba, zuciya ta rufeba uncle yayi Sokoko yana saka Wulakancin da zai mata, ni kuma ga mugun jirin da ya qara tasomin ga sanyi inaji ga yunwa, na dunqule hannu nakaiwa sista khadee wani wawan nushi, kuma na kamata da duka baki, sai jini, unle yana tsaye riqe da kumatu yana dada kallon wai almajirace zata mishi wannan wulakanci yana chi gaba da saka sharrin da zai mata kuma yasaa ma danginta wulaqanci, sai ganin yayi ana kokowa, tuni ya hanbare ni aw urgar dani gefe, ina miqewa na kama hanyar dana ga na biyo mun shogo nasamu na fita gidan nakama hanyar titi kamar mahaukaciya, ga warin kwata gashi ina layi kamar yar maye, gashi banida ko kwandala na shiga tazi, ina tsaye idona sun fara rufewa naji qarar mota gabana, sai jin nayi yace ina zuwa na fada mishi unguwarmu tuni ya bude min nashiga.....?

contact-form


Post a Comment

0 Comments