ASHE KAINE MIJINA
ASHE KAINE MIJINA - 22
ya bude min nashiga, ina shiga motar ban kara sanin inda nakeba, suma nayimi nayi Allah masani, sai farkawa nayi na ganni a wani makeken gado an saka min ruwa, na bude ido a hankali, na jujjuyasu bansan inane nan ba, nayikokarin tashi amma nakasa tashi kaina yayi nauyi, naduba sai naga ashe ruwa ake qaramin, iya tunanina gidan su sister khadee ne tunda daga chan nafito, my be faduwa nayi aka maidani chan.
Kawai sai na daure fuska dan kuwa banason ganinsu. Banason taimakonsu, banason duk wani abu daya shafesu, ina kwance sai ga wani saurayi gajere fari ya shigo, ina ganinsa, na fara surutai, miyasa kuka maidani gidanku, miya dameku da lafiyata da ciwona, Kuma idani gaidanmu banason ganinku ko kadan, haka nayita surutai ina kokarin cire drop dinda aka sakamin sai naji ya rike hannuna, na daga ido na kalleshi baice min komai ba saima bina da ido da yayi ina balaee na, naso in ci gaba sai kuma na fasa sabida kaina yayi nauyi Sosai ihun da nayi, namaida kaina, na rufe idona, bacci mai nauyi ya kara daukeni banfarka ba sai tsakiyar dare, abin mamaki....?
ASHE KAINE MIJINA - 23
Na dauki ledar na shiga bayi na kulle nayi wanka da yake kaina adaure yake, amma dai gashina anyi sama dashi hakan ya bani damar wanke gashina tsab,nayi wanka kamar ban taba wankaba, ga ruwan da zafi Sosai, duk sanyi da kasalar da suka rage naji sun tafi, nayi brush, amma yunwa ta addabeni, na saka kayan top ne da jeans, nafito kamar baniba, amma zuciyata cike da haushin su sista khadee, ina fitowa naji ana kiran sallah, na tuna inna tace kada inkai maqreeb.....?
ASHE KAINE MIJINA - 24
Kada inkai magareeb, naje na tayarda wannan gajeren yana wani mutsuke ido, mallam ka tashi kaje ka kira sista khade akaini gidan mu ko a budemin kofa inje gida, na fada cike da kadara, wani kallo yakemin, kallon baisan alkiblar maganataba, kallon mi kike nufi, ya tashi zaune, amma kya bari gari ya waye sannan akaiki gida ko, wane gari zan bari ya waye? Yace Bakiji ana sallar asuba bane? Asuba!?? Dama asubace ba maqreeb ba? Kuka ya kubucemini ba tare da nasaniba, miyasa sister khadee tamun hakane? Miyasazata bari ihar in kwana gidansu kuma ta ijiyeni a dakin uncle dinta.
Lallai khadija ba kawar kirki bace, wannan duk araina nakeyi, na dago na kalli mutumin nan, na rasa irin rashin kunyar da zan surfa mai, kawai, nace uncle to sista khadee ta gayawa inna da yaya ina gidansune? sabida inna tace kada in kai magareeb gashi har gari ya kusa wayewa? Yayi kasake yana kallona, kayi magana mana uncle, yaji dadin sunan data kirashi dashi, har yana maimaitawa a fili uncle, amma kuma shi wacce sister khadee ce takefada haka, Lallai idan yagaya mata baisan sister khadee ba wannan rudaddiyar zata daga mishi hankali fiye da na yanzu, amma zai lallabata har gari ya waye sai ya mata bayanin komai, da sanyin murya yace ki zauna in miki bayani, kinji sister na, da jajayen idona na dago na kalleshi jin ya fadi sunan da yaya yake kirana dashi, sai na sami kaina ina maibin umurninsa, nazauna girmn kai ba nawa bane nan.....?
ASHE KAINE MIJINA - 25
Ba wata mafita illa in danne abincina in barwa Allah ko na mutu in tafi ciki da nauyi.
Saida ya kira sau uku ana hudu aka daga, batayi maganaba shi ya fara sallama aka amsa mishi sama sama, yanzu inna take gayam nazia har yanzu batadawoba! Kuma tace gidan ku zataje kamar yanda kika roka na amince ta tafi, tace Nazia kuma? Ai batazo nan ba, What! ......?
ASHE KAINE MIJINA - 26
ASHE KAINE MIJINA - 27
Hakadai wasa wasa har saida Nazia tayi kwana hudu a gidannan bata kara ganin saba, kuma kamar aljani sai tayi bacci yake kawo mata abinci abin yana daure mata kai, yau ta dauki alwashin bata ba barci, har kusan magareeb ba'a kawo mata abinci ba, data gaji da jira sai ta dan gyangyada baccin da tashinta duka minti hudune amma har ya kawo abinci ya fice abnshi, tunani kala kala takeyi, ta fara tunanin ko ta daina cin abinci ne, wata zuciyar tace ki danne abinki ko kin mutu kije da nauyi.
Duk tayi wani iri da ita ammafa bata rameba ko kadan dan kuwa bata wasa da abinci saidai akwai alamar tashin hankali tare da ita, Iyaye anyi sanarwa har an gaji bata ba labarinta, anje gun malamai suna ta addu'a anata sauke qur'an Allah ya bayyanata amma shiru sister khadija kuwa bata ma san cewa har yanzu ba'aga nazia ba, hankalinta kwance tana al amarrunta, ko a skull da andauko zancenta sai tabar gurin batason zancen, bata San zancen batanta akeyiba, su kuma sauran sun dauka haushin rashin kawane yakesa bata zama cikin mutane musamman da ake cewa garin zuwa gidansu ta bata.
Yaudai bazanyi bacci ba sai naga aljanin da ke ijiyemin abinci, baccin kariya nayi ya dauka nayi bacci ko minti uku ba'ayiba naji ana buda kofa a hankali bayan ya bude sai kuma ya tsaya kamar bayan minti daya sai aka turo kofa ina jin ya turo kofa nayi zubur na miqe dama akan dadduma nayi baccin gefen kofane.....?
ASHE KAINE MIJINA - 28
Kofane, yana Shigowa na mikke dan Allah uncle kayi hakuri, da abinda namaka dan Allah ka kaini gida, aranshi yace dama batayi bacci ba.
Miyasa ka ijiye ni anan? Mi kakeso in maka?Baka tsoron Allah ne? Ko kai ba musulmi bane? Baka tananin halinda iyayena zasu shiga? Is ok? ya katseta, da daga mata hannu kansa na kallon kefe, ta dago ta kalleshi, ki natsu kiji mi zan gayamiki!! Na farko Idan na fara magana kada kiyi magana sai na kare, kinajina? Yes naji! Ya juyo ya kalleta tausayinta da yanda ta bashi amsa ya kamashi , lokaci daya sonta da sha'awar kusantarta ya kamashi, ya hade yawun dole, gashi ta wani mishikyau, tufafin sa ne a jikinta top da wando, yayi sauri ya kawar da kai, ya mike tsaye idan har yakuSan ceta bai mata adalciba, dan kuwa yayi niyar keta mata mutunci ladar mari da ta mishi amma kuma tausayinta ya rinjaye shi, ya mike anjima zan miki bayani, zatayi magana, mi nace miki.
Ta tuna yace kada tayi magana, ta kalleshi taga idonsa taga ya kada yayi jaa, sai taji tsoro, ya fita, mamaki ya kamata yanda ya sauya lokaci daya, taci abincin tayi sallar tana nan za une sai gashi ya shigo, abin mamaki bai kalli ko gefenta ya zaune ya juya mata baya....?
ASHE KAINE MIJINA - 29
ASHE KAINE MIJINA - 30
Mun isa unguwar mu da misalin qarfe tara na yamma, na rangada sallama inna tana ganina ta fara salati Sai kawai ta fashe da kuka nima na fashe da kuka, tana kuka ina inayi tayi wa yaya waya ko minti biyar ba'ayiba ya iso, yana zuwa naje na rungumeshi ina kuka, araina nace ni ban rameba su suka rame, duk sai suka qara bani tausayi, nan aka fara tambayar ya akayi? Na koro musu bayani daga farko har karshe, sun tausayamin kuma mamaki ya kama su, suka gayamin rashin mutuncin da sister khadee ta musu, anan dai wanda ya kawoni shima yayi bayani nashi, sai dai yayi karya sabida ce musu yayi sai jiya da dare na farfado kuma yace tsoro yaji ganin lalacewar kasa kada yakaini gurin yan sanda ya janyo wa kanshi wani abin daban, to hakadai a ka jajantawa juna akayi waya kauye aka sanar dasu an ganni iyayen nura sunji dadi Sosai inna tace gobe sai ayi sadaka....?
ASHE KAINE MIJINA - 31
Yaya ya Siyo min siyomin sabuwar wayah da sabon sim, sabon gata da kulawa wajen inna da yaya ba'a magana, kusan kullum sai unle habeeb yazo gidan mu har dai ya shaqu da inna ya zama kamar dan gida tun da inna ta fahimci sona yakeyi kamin ma ya furta take bashi labarin nura kuma ta gaya mishi Lallai wasiyar mahaifinane in auri nura, baiji dadin rasani da yayibahakan kuma baisa mun daina zumunci dashiba, amma ya rasa wani farin cikin sa, yan gidan su sun sammu muma munsansu har zumunci mukeyi.
Saida nayi wata biyu chur a gida sannan aka fara maganar komawata makaranta, yaya habeeb yace a chanzamin skull, haka kuwa akayi aka chanza skull, ban kara jin labarin sister khadee ba, Ranan munje bakin auren kanwar uncle habeeb nida inna muna dawowa a hanya mota tayi tsayinta na kunna na kunna taki tashi munanan tsaye saiga wasu Guys sun wuce sai inna ta musu hannu har sun wuce Sosai sai suka dawo, da yake ina cikin motar ne, ki fito ga wasu yan samari nan na tsayar kinsanba jin maganata zasuyiba, nafito suna zuwa suka fito motar su, sai dayan guys din yace kace kamar kasan matar kuma kace tsohuwace, yes Wallahi kafa San yau tin safe nakejin faduwar gaba, kirjina sai dukan uku, uku yakeyi i don't know you. Yanzu ma Sai naji ya karu, ita tsohuwar fa, Share Ashe ba tsohuwa bace manyan kayace, suka kwashe da dariya, suna kokarin tsallakowa, amma fa daga farko tsohowar dana gani kamar na santa amma na manta inda nasan ta, any how tunda munzo mutaimaka musu kawai, inna dama tana ganin sun dawo ta ta shige mota abinta, abokin deen ya shiga motar yayi danne danne sai kawai motar ta tashi, tunda suka zo naji jikina ya chanza na Kasa dago kai in kalle gefen da nakejin ana kallona, muje ko deen dayan abokin ya fada amma ina deen yayi Nisa, Na dago da kyar na kalle mai maganar nayi godiya zan zaga yace idan ba damuwa ki bamu number ki, murna kamar ta kashe deen, Lallai yayi dacen aboki da yake gane duk wata matsalatashi, na bashi number bada son raina ba dan kawai mutunchin da suka mana ne....?
contact-form
0 Comments