ASHE KAINE MIJINA
Ashe Kaine Mijina - 45
Bacci mai dadi da nauyi cike da mafarkin deen dina, ban farkaba sai guraren 11 na tashi na kimtsa mukayi break fast, deen ya siyo min ticket daga abuja zuwa sokoto, shi kuma yace sai gobe zai dawo, bada son raina na rabu da deen dinaba amma ya zanyi dole in hakura na isa gida cike da murna da farin ciki bana tunanin komai sai deen dina, inna taji dadin yanda ta ganni nayi kiba tubarkalla dani, kirjjina ya cicciko Sosai.
Nima na kula da hakan, musamman lokacinda na zo abuja deen dina yake cewa na kara kyau da ni'ima kirjina ya cicciko dai dai hannunsa, na dauka santina yakeyi ashe da gaskene, munsha hira da inna Sosai, sai guraren magareeb yaya ya dawo muka gaisa dashi yaji dadin ganin yanda nayi kyau, autan inna waje ta karbeki, na kyalkyale da dariya, ai yaya wajeta hadune naijarmu ce sai a hankali! munyi hira sosai dasu, anan nakejin yaya wai zai auri Zainab khalifa, abin mamaki yarinyar da ya tsana kuma ya raina wai itace har yake ce mata honey a waya, Lallai soyayyah soyayyah ce, sai guraren 10 na dare sannan na koma gidana duk na gaji ga kaya niki dana niko, ina zuwa sai bacci ya kwasheni, ban farkaba sai kusan asuba, nayi sallah nashiga aikin gida ko ina na gyara duk yayi kura na aikatu amma kuma gidan sosai yayi kyau gidan na chanza mai fasali, guraren la'asar sms yashigo.
"GOBE KISHIRYA KIYI GIRKI SU YAYA ZASUZO SU MIKI SANNU DA DAWOWA"
mist shi wannan mutumin shirmensa yayi yawa. Na Shirya musu girki kala kala, Cikin kayan da deen dina ya siyo min na fitar musu da tsaraba, sunzo sunji dadin ganina da sukayi na kula da matar yayan nura sai kallona take tana murmushi motsi kadan tace mini sannu, araina nace matar nan tana sona, naji dadin zuwan su, sun tafi sun barni da Kewa.
Ashe Kaine Mijina - 46
Na isa Turkey. Ai nasan kin isa Turkey Ya karanta sms din yayi dariyar mugunta nura kenan Hello deen, Hello, Kanajina kuwa? Yez inajinki! Ya naji kana magana fada fada. Waya tabamun kaine? Kedai ki fadi abin da zaki fada kawai Tayi shock dajin wannan maganar a bakin deen, wanda daidai da rana dayabai taba mata koda gaddama ba bare ya mata bakar magana! Tayi ajiyar zuciya Allah ya baka hakuri, dama maganar cikinnan ne nace ya za'ayi dashi.
Kuma dama inason in gayamaka na karbi takarda sakina. Deen yayi dum jin wannan maganar ta hulwaty, Lallai maisha ta rika tasha ba abinda yafi illa ya fatattaketa ta rabu dashi, amma ya mata adalci kuwa? Anya yiyiwa kanShi da son da yake mata adalci kuwa? Anya zai ma iya rayuwa ba hulwar sa, zaka iya mana dayan zuciyar ta bashi amsa.Takeshi daga dogon tunanin da ya tafi, deen kayi shiru deen! Yanda ta fadi maganar da murya mai Sanyi sai ta kara bashi tausayi. No Inajinki ci gaba.
Ai na fadi duk abinda zan fada! Kai nake jira. Dama ke duk abinda mukeyi dake kinSan bakiyi planing ba? Dan ki zubar min da mutunci yasa kikayi tarayya dani? Akan me zaki bari ciki ya Shiga, Ta yaya zan aureki da ciki? Sam bakiyi tunaniba kuma bakiyi nazariba, ni Muslimine bazan taba yin shirka gurin zubar da cikiba, Sabida haka kisan yanda zakiya da cikin ki, ki nemi mijinki kuyi Sulhu ya rufa miki asiri ba hannuna. Deen kaine kuwa? Ta Katse shi cike da mamakin abinda yake fitowa dagab akin deen mi yake Shirin faruwa da itane abin kamar a mafarki. Ki saurareni ya fada yana mai daqa murya. Daga yau Sai yau kada ki kara nemana. kadama ki kara nuna kinSanni. jahilar banza wacce batada tunanin.
Bansan lokacin da wayar hannuna ta subucemin ba cikina ya fara juyawa na fadi kasa na fara rero kukan nadama. Tabbas na jahilace tana kuka tana surtai,banida ilimi gaskiyan ka deen ni jahilace ina matar aure namaida wani namijin mijina ina zankai hakkin aurene? Kadan daga azabar da Allah zaimin kenan kamin inje kiyama inchi ubana. Chikinta yaci gaba da juyawa, sai ta fara zubar da jini, Ta tabbatar da idan har ciwo yakamata anan sai dai ta mutu ba wanda zaikaita asibiti.
A Turkish naji dadin kasar duk da cewa ita ma akwai tsadar rayuwa amma tafi Cyprus arha, sai da na shalle sati biyu anan, nayi kewar deen fiye da ko wane lokaci, kullum muna waya muna faranta ran juna, danma kar ya ga jarabata tayi yawa ya rainani da tuni nace ya biyoni Turkey, amma dole in kama kai, ko yanzu dai na more, "wawiya "Haka na kare zama Turkey na wuce India ba nura ba labarin sa nayi zat on zamu hadu koda sau daya ne amma ina, a indiya nayi wata daya cur dan kasar tafi su dadi da kuma saukin rayuwa, duk kudina da suka rage a India na karar dasu, a India ne na fara wani zazzabi zazzabi, amma dai ban baiwa zazzabin hadinkai ba dan kada ya rage min jin dadina, har yaren India na koya dan zamanda nayi, na hada tsarabata da wacce deen ya siya mun da wacce na siya na biya kudin kilo na dawo gida, a abuja na sauka, nayi waya gida na gaya musu na iso gida, ina mijin naki nayi dumm,ko baya kusa idan yazo ki gaidashi, nace aah ai sai karshen sati zai Dawo, sukace to Allah ya dawo dashi lafiya, nayi waya da deen dina na gaya mishi ina abuja yace in kama hotel in jirashi yazo, haka kuwa akayi na kama hotel, shima gobe ya iso, aranar kwana mukayi muna abu daya, deen ya nuna min yanda yayi missing dina nima na nuna mar munji dadin juna! Tir daku.
Har deen yake cewa Asia ta karbeki kalli yanda kirjinki ya cicciko, na rufe fuskata na fada kirjinsa, yayi murmushi yana shafani a hankali, tabbas daba deen ban san yanda rayuwata zata kasanceba, banajin ko za'amutu zan baiwa nura kaina a matsayin mata, haka bacci ya daukeni bacci mai dadi da nauyi inata mafarkin deen dina.
Ashe Kaine Mijine - 48
Barni da kewa? A mota matar yayan nuru take ma yayan nuru gulma wai inada ciki, Kaga yaronnan mutumin banza yana nuna ma mutane bai damu da naziah ba Ashe munafukin yana zagawa kaganta har da ciki, murna a gurin abban Fatima kamar me, kamar ma ba'ataba musu haihuwa ba, a hirar har an saka suna yaran da naziah zata haifa, idan macene sunan mamar nura idan kuma namijine sunan marigayi baban naziah, kunji mutane da iyayi.
Dan aikin da nayi na gaji Sosai na kwanta sai bacci, na tashi da wani irin Zazzabi da kasala na kula aikin da nayine ya haifar min dasu tunda da muna gun honey moon bana komai deen dina yake mun, a India ma nayi irin wannan zazzabin Nasha panadol naji sauki. Nura ma ya dawo Sokoto munanan kamar yanda muke ba wani bayani har yau nakai wata uku da Kwana ashirin jikina ya bude, nayi kiba na gara kyau dani sai missing din deen dina nakeyi.
Na dauko waya na kira deen muna hira nake gayamai fa lokaci yayi ya kitsa min abinda zan fada ma mijina ya sakeni nima yace min akwai wani abu da yake jira yana kammala shi zai sallami matar tashi kamin lokacin na kammala idda na sai muyi aure.
Suna kammala waya jikinta na rawa ta dauko dayar wayan da nura ya bani dama dashi take mai SMS. Bata taba kiran saba Shima bai taba kirantaba, Duk abinda deen dinta ya fada taga idan ta fadamai zai rainata my be ma yaki sakinta sai kawai ta chanza shawara ta tsara yanda zata mai haka kuwa akayi ta aika SMS tana jiran reply.
Abin mamaki ba musu ya aminta da buqatar ta na ya saketa amma da sharadin cewa sai nihal ta dawo ta ganta sannan zata tafi gidan su amma yanzu zai bata takarda tayi ran tsawa akan ta yarda.
Ashe Kaine Mijina - 49
Itama ta amince da sharadin sa duk a SMS suke maganar, Nan take nura ya rubuta takardar saki ya ijiye ma naziah a hanyar dakinta, murna kamar ta kasheta yau zata kai ga burinta,ya deen dinta zaiji idan yaji ta karbo takardar saki,murna ba'a magana, kamar ta wuce gida amma sai tace bari dai ta cika alkawari kuma taga wannan nihal da akeji da ita,kowa zancenta yakeyi zata dawo karatu canada, kuma tace gidansu zata sauka.
Naziah na Kwance tana yan tunane tunanenta, yanda aurenta da deen zai Kasan ce tunda yanzu ta zama bazawara, a bikin Su tayi kaza tayi kaza, a wannan tunanin ta gangaro wani tunani. Sai yau nake tuna cewa fa,tunda nayi aure banyi al'adaba ko sau dayaba.
Sai yau nake tuna dan ciwon dane da yawan zazzabin da nakeyi. Yanzu nake fahimtar inajin cikin cikina kamar ana min motsi. Sai yau na tuna duk kwanciyar da nake da deen dina a jikina yake zube min. din bai taba amfani da condom ba! Lokaci daya hankalina ya tashi lallai ni lafiyayyace kuma komai zai iya faruwa dani, Kardai ciki nake dashi? Wai ma idan nayi ciki ya zan kalli inna, gashi na kashe aurena rana ta farko da naziah ta fara nadamar abinda ta aikata gashi ta karbi takardar rabuwada nuraya zatayi.
Ta Shiga kogin tunani Lallai mafita itace taje asibiti Dr ya dubata, ba shiritadauki key Sai wani private hospital, ta fara yima Dr bayani abinda ya kawota, Bayan bincike bincike Dr ya gane cikine da ita Dr yazo yana fada, ke kinsan kinada ciki amma bakizo aka dubaki ba sai yau, to lallai jaririnki yan. Batamaji abinda Dr yace ba ta fadi sumammiya.
Ashe Kaine Mijina - 50
Sumammiya, likitoci sukayo kaina aka samu ta farfado ta fara sun batu, Dr dan Allah kataimakeni Dr ka rufamin asiri ya zanyi da rayuwata, shi Dr yadauka taji abinda ya fada ne na cewa yaron cikinta na cikin matsala kuma cikin zai iya zubewa ko wane lokaci, hakan yasa yake bata hakuri da magana tare da alkawarin kasan cewa Dr ta har ta Sami sauki, ya rubuta maganguna da allurai da kuma abincin da zata rikici. Ta dawo gida cike da zullumi,da tunani, shin zata fara fadama deen labarincikin da take dashi ne ko kuma ta fara da maganar sakin da aka matane, "Nima dai jabo sai kallonta nakeyi" tadai yanke shawaran Sanar dashi zancen cikin before sakin, dama bata tafi phone dinta ba,Ta kira deen dinta, koda tazo ya kira har 8, ta kira He'll hulwatiy ya kike ina kika shiga inata kira baki dauka ba?
Hello ko baki jinane? har zai kashe sai yaji maganarta a hankali, Inajinka deen! Lafiyan ki kuwa? Naje hospital ne. Subhanallahi hulwatiy mi yake damunki,Waye bashi da lafiya? Kimin bayani mana kinyi shiru.
Na fara magaba ka katseni shi yasa nayi shiru. Sorry hulwatiy kinsan Banason abinda zai taba min lafiyar kine ko kadan, kece jina kece ganina, kece duk wani buri na rayuwata! Talk to me please m hulwatiy! Tayi ajiyar numfashi, Dazu Dr y dubani yes inajinki ci gaba, miyake damunki mi Dr yace? Yace wai inada juna biyu? What!
Yes yace ciki nake dashi, haba hulwatiy, Kidaina min irin wannan wasan mana! Kamar ya WasaWallahi deen da gaske nakeyi. Hankalin deen ya tashi matuka, ya Rasa abin cewa, Ok ki bari anjima zan kiraki yanzu inajin maganar wannan shasha shar tana zuwa kada taji mi muke fada! Amma ai yau Monday deen dazu kace min kana office ne, yes ina office inaga tanada bukatar kudine tazo gurina! Amma kace min baka taba ganinta ba ya akayi har kake gane muryarta? Anya deen! No kingane ai.
Sai taji sallamar mace a wayar kuma taji an kashe aranta tace ee naji muryar mace inaga ta biyo shine, sai bata gane komai, kuma bata taba tunanin yaudara a gurin deen ba.
Da farko kuma har taji tsoro, Amma fa ita dole deen yazo a zubar da cikin nan kamin tayi yun kurin barin gidan aurenta, aranta ta rika sake sake har bacci ya dauketa, Abangareen deen kuwa yanata sake aran shi yanda za'ayi da ckin nan, shikam bai San yanda zaiyi da itaba, kuma yasan illar zubar da ciki dan zata iya mutuwa, kuma dole Shi zaikaita hospital kuma shi zaiyi sign Lallai bazai iyaba! idan ta mutufa.
Miye mafita?Mafita dayace kawai ka rabu da matar mutane kaje ka rungumi matarka! Idan nayi haka anya na mata adalci? Lallai nayi kuskure nayi jahilci tarayya da matar aure, Haka ya kare tunanensa karke ya yanke cewa zai rabu da ita kawai ta San yanda ya zatayi da cikin.
Kinji mugu dan iska kadan daga cikin halayen sheguuuu? bata farka ba sai guraren magareeb, tasan ma deen ya kira, a gurguje tayi sallah bata kareba aka kira magareeb tayi magareeb tayi addu'a ta janyo waya. Ta duba wayam ba miss call ko daya abin ya bata mamaki matuqa. Ta daureta kira shi sai na uku ya dauka, Hello deen.
Ashe Kaine Mijina - 52
Ta rarrafa tun tana ganuwa taja mota sai hospital, kamin ta Isa ta jike sharkaf da jini, bayanta kamar ya bude.Takasa karasawa cikin sai kwasarta akayi akayi ciki da ita, Likitoci sukayo kanta, aka mata allurai. Lokacinda ta farka taji ana kara mata ruwa, Dr yazo yana mata sannu, Hajia naziah sai dai kiyi hakuri munyi iya bakin kokarinmu na ganin mun tsayar da zubar cikin amma abin yaci tura, karke ma Sai mukaga idan mukayiwasa zaki iya rasa rayuwar ki, sai kawai muka miki allura cikin ya karasa zubewa.Wata hamdala tayi hadi da jin dadi, lallai Allah ya rufa mata asiri da ya zubar da cikinnan, Dr yace Yanzu zamu baki allurai da yan magunna kuma yakamata ki sanar da mai gidanki halin da ake ciki, kamin mu sallameki, No Dr maigidana baya gari kuma ni ba yar nan bace. Tafada muryanta yana hadewa, Dr ya kalleta yace to shikenan zaki zauna anan har zuwa gobe ko jibi idan kin kara Samun lafiya Sai mu sallameki. Dr kayi hakuri ka sallameni yanzu kaga banzo da phone dina ba kuma nasan mijina da iyayena zasuyi ta nemana hankakin Su zai tashi ataimaka min please Dr.Hajiya bazai yiWu ba, duk da kinada cikakkaiyar lafiya amma ya dace kidan kara samun rest.
Ashe Kaine MIJINA - 53
Samu rest, duk yanda Dr yayi akan naziah ta bari har gobe idan takara jin sauku a sallameta ta tafi gida amma abin yaci tura, ta nace akan tunda tanada lafiyar ta gida zata tafi. Ya rubuta mata magunguna da kuma allurai, kuma yace tana bukatar hutu danatsuwa, yace mata mahaifarta ta sami matsala zata rika zuwa ana dubata har ta Sami lafiya,kuma idan tayi wasa zata iya rasa haihuwa har abada, ya kara bata hakuri akan Kasa war da yayi na ceton yaron dake cikinta kamar yanda ya mata alkawari anan dai ya kara mata bayanin cewa dama cikin zai zube dan ba daidai yakeba, haka ta dawo gida guraren 11 na safe, tana tasake Sake aranta har ta iso gida, Nidai banyi dacen rayuwa ba, na cutar da kaina na cutar da mijin aurena, nakasa kare darajar aurena, karke ga yanda deen dina yamin, Lallai maza ba abin amince wa bane, anya kuwa deen dinane yamin haka? Dayan zuciyar ta ya bata Amsa yes deen dinke mallam naziah.
Any how mun tashi 1__0, tasha alwashin sai ta rama abinda ya mata."Kinji hauka ko ina zata Ganshi ta rama oho "Ta iso gida ba karfin jiki, ta Samu tayi wanka da ruwan dimi ta kasa jikinta Sosai tasha tea ta nemi guri ta kwanta, a baccin ma dai mafarkin deen ta rikayi, tana taShi ta tsine ma baccin da mafarkin gaba daya, guraren karfe hudu na yamma sms ya shigota, taji duuum nurane
"JIBI NIHAL ZATAZO KI GYARA MATA DAKINDA ZATA SAUKA"
Tayi duum ita kadama suzo Suga halinda take ciki su ganota, Hakanan ta lallaba taje dayan banqaren ta dan gyara sama sama, ta koma dakinta, dama naziah akwai zama daki "kamar jabo "Yauce ranar da nihal zata iso guraren 4:pm zata iso, Nura yasa an yo siyayyah abubuwa kala kala duk na tarbar nihal, Naziah aranta taji tana son gani wannan yarinyar da ake azabarbabin zuwanta.
Kamin karfe biyu ta kammala hada komai gida yayi fes dama fes yake girki kala kala ta hada duk na tarbon nihal, itama dai tadanyi wanka duk da yanayin yanda ta kode ta chanza tayi wani iri da ita amma dai tayi kyau abinkada kyakyawan mutum.
Ashe Kaine Mijina - 54
Tana zaune parlour tana kallo har guraren biyar basu isoba, lokacin shan maganinta yayi ta shiga daki kenan taji karar mota haka kirjinta ya rika dukan uku, ko miye haka oho, tanajin maganar Su sama sama, abinda yafi bata mamaki muryar wacce takeji kamar tasan muryar amma ta manta inda tasan muryar, Aunty! Aunty!, Ina kike gamu mun iso, muryar da taji kenan ana gwalla mata kira, Shikam nura yana ijiye nihal ya fita dan kada naziah ta kwafsamai gaban m nihal.
Na'am ina zuwa,naziah ta bada amsa a takaice.Ta fito kamshin da taji Lallai tasan kamshin, amma tasan hancin tane yake yaudararta.Tafito da Walwala abinda take gani gabanta yafi bata mamaki akan komai, ba kowa bace face tsahuwar kawarta da tafi tsana a rayuwar ta itada mugun uncle dinta wacce Sanadiyar su ta bata wato sister khadija, tuni ko wacce ta daure fuska naziah ta kalli she khadjia a wula kance ina nihal take?
Nihal ta kalli naziah cike da mamaki da al'ajabi Lallai wannan naziah ce kuma itace matar uncle dina dama ance mata sunanta naziah! Kuuut yau ake yinta. Ko wacce na kallon yar uwar ta, nihal cike da mamaki tace nicefa nihal din, naziah tace miya kawoki nan gidan, suna cikin magana kawai sai ga nura yashigo. Nihal! Nihal!
Ya Shigo da kayaa niki a hannu yana kwalawa nihal kira. Abinda ya gani shine ya bashi mamaki hade da daure kai, ledodin hannun saduk suka zube, Jikin Sa na rawa hadi da sarke war murya ta tashin hankali hadi da tsori ya kalleta murya na dancing, ke miyaa miyaa kawoku gidana! kinzo dan ki tarwa tsamin iyali na hadi da jin dadina ko, waima uban wa ya baki address din gidana. Naziah ta gama razana jin yace miya kawota gidan sa, idan dai nan gidan sane to Lallai mijintane! Kuma shine uncle din sister khadee da yace mata almajira kuma ya mareta, shine mutun na farko data tsana a tarahin rayuwar ta?
Shine sanadiyar batanta! Kuma shine mutumin da ta kara tsana second time a rayuwarta wanda yayi sanadin shiga tashin hankalinta! Jin tayi an katsata da wata irin tsawa ke hulwa badake nake magana ba?
Nura ya kalli nihal yace ke ina naziah ta shigane? Nihal ta kallu uncle dinta cike da mamaki tace uncle wannan ma ai sunanta kenan fa naziah, WHAT!
Ashe Kaine Mijina - 55
What! Yes uncle itama sunanta nazia, itace kawata da nake baka labari lokacin, kuma itace wacce ta maka rashin kunya lokacin da taje gidan mu, No bashi nake neman saniba nihal, wai itace matar tawa? nihal da mamaki ta kalli uncle dinta, tace kaman ya uncle dama bakasan matar taka ba? yayi shiru yarasa abinda zai fada, ita nihal mamakinta shine wata hudu dayin auren baima tama sanin matar ba to ya akayi akace mata tayi ciki.
Kuma uncle yace mata bai santaba bai ma taba ganintaba amma batayi tunanin abin yakai hakaba! nazia iya tunaninta ta gane cewa lallai wannan nura shine mijinta, kuma shine uncle din sister khadija, kuma shine deen dinda ya yaudareta yaci mata mutunci. Dukansu sunyi churko churko kowa ya rasa abinda zai fada.
Nazia taji tsoro matuka tayi tunanin kada su mata wulakancin dayafi wanda deen ya mata da wanda wannan tsohuwar kawar tata ta mata, tajuya zata koma dakinta ta tattaro kayanta ta wuce gida tunda dama ya saketa, tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki dama batada lafiya cikinta daya zube, tayi taku biyu uku kikajita lau, ta fadi "nima jabo bansan miya sa ta fadiba" duk sukayo kanta nura jikinsa na rawa yake bubbugata amma ko motsi batayiba hankalinsa ya tashi matuka suka yayyafa mata ruwa amma ina shiru da sukaga zasu bata lokaci sai suka dauketsai asibiti, a hanyar asibiti kamin a isa ta farfado taganta a mota tayi yunkurin mikewa zaune taji an dan daneta irin ta kwanta dinnan a jikin wani kamshin da takeji yana dukan hancintane ya tabbatar mata cewa tana tare da deen ne ta dako dagyar tana dubawa taganta ashe jikin deenma take kwance, dukda rashin karfin jikintanba bai hanata tashi a jikinsa da karfiba hadi da dalla mai harara da wani uban tsakiba, ko ajikinsa shidai ta samu lafiya itada dan cikin da ke jikinta! "kunji wawa baima san cikin ya zubeba konijabo da masu karatu munsan cikin ya zube ko baku saniba? kusaukeni anan! ta fada a taqaice dan bata iya magana sosai. deen ya bude baki zaiyi magana.
Nace a saukeni anan! Wannan karo da gadara hadi da isa ta fada tare da tsiwa irin tata, komai ta fanjama fanjam, ta murda marfin motar wallahi idan baku tsaya ba zan sauka, kuma motar tana tafiya ne, deen ya tabbatar da zata aika yacema nihal ta tsaya tafita ta basu wuri, nazia tamai kallon banza, dawa za'abarka....?
0 Comments