ASHE KAINE MIJIMA
HE KAINE MIJINA - 56
Y a kalleta ya marairaice haba, ta katseshi da she! yimin shiru munafuki banza mayaudari lokaci daya ta kirashi da sunayen ta bude marfin motar da karfi ta fita abinta, yafito yabita a baya har zata shiga taxi yaja ya tsaya yabita da kallo hadi da kallon cikinta lokaci daya Allah ya sakamar qaunar cikinta fiye da yanda yake tunani, nihal nason tayi magana amma kuma yanda taga ya daure fuska ya wani chanza sai tayi shiru.
Chan kuma sun kama hanya tace uncle nifa bangane wannan abunba nakuba naga, bakuma zaki ganeba, ya bata amsa a taqaice, ta kalleshi ta gefe, har zata kara magana ya katseta, kuma banason inji wannan abinda ya faru gurin kowa! nihal taci gaba da driving dinta, uncle ina zamu tafi yanzu, gidana, nanma amsar a takaice ya bata.
To ai, to ai me? look nihal kindameni da magana kibarni inji abinda nakeje please har suka isa bata kara mai maganaba, nazia direct gidan su ta wuce tana zuwa ta fada jikin innarta tana kuka, inna tana tambayarta abinda ya faru dagyar ta iya bude baki tace nurane ya sakeni.
Inna tasaka salati..! sakifa kikace yes! wallahi inna ya sakeni! inna tana ganin abin kamar bada gaskeba ko kuma mafarki, to Ina takarda, nazia tadan takaita kukan nata tace takarda tana gida namanta da ita, hankalin inna inyayi dubu ya tashi, inna ta kalleta rai a bace kinga yanda kika dawo lokaci daya kamar mai jego? Kirjin nazia ya kara bugawa, waima miya hadaku ne da har ya sakeki? naci gaba da kukana ban bata amsaba inajinta tayi waya da yaya ta gaya mar abinda yake faruwa.
Bansan abinda yace mataba kawai sai naji tace to sai ka iso ta kashe wayar, tazo tazauna kusa dani, tayi tagumi chan kuma tace, Allah dai ya saukeki lafiya amma wallahi yaronan baiyi halin iyayensaba, amma dai bari muji miya hadaku kamin ince wani abu! Wani rasss naji dama inna tasan inada ciki kenan? to ya akayi suka gane inada ciki.
yanzu idan ma nace baitaba kusantanaba ba yarda zasuyiba lallai da sake.
ASHE KAINE MIJINA - 57
Lallai da sake dole insan yanda zan bulloma lamarin "zancen zuci takeyi" Allah nagode ma da ka zubar da cikinnan, na tashi zan shiga dakin inna kenan, sai sallamar yaya mukaji yashigi kamar an turo shi yayi jaaa kamar kauta? sai huci yake kamar wani kasa, wallahi inna tun farko nasan za'ayi haka! nur bayason nazia itama bata sonsa amma muka rufe ido muka ce sai anyi auren nan kuma na gaya miki haka tun farko yanzu ga wulakancin da yayi mana nan yasokota dan ma cikarshi dan iska baitashi sakintaba saida ya mata ciki yanzu dan Allah inna abinda yayi ya kyauta kenan? Ya mata adalci kenan? yanzu ki.
Inna ta katseshi kai wai wane irin mutunne kai bakasan miye ya hadasuba kawai zakazo kana ma mutane rigimar banza, Ai ka bari ta mana bayanin miye ya hadasu har ya saketa sannan ka fara rigama rigimamme kawai! dan tazo tace yasaketa haka kawai ba fada ba komai zai saketa? dukansu basason juna to katabbata akwai laifin kowanne su aciki kabari tayi bayani da bakinta, ta kuma nuna takardar sakin sai aji yanda za'abullowa abin, yaya yayi ajiyar zuciya ya nemi guri ya zauna, amma fuskar nan har yanzu aturnuke, ya kalleni cike da tausayi kiyi haquri nazia kidaina kuka Allah zai saka miki idan ya yaudareki ina takardar sakin naki, Nazia ta bude baki dagyar muryanta duk ya dushe, yana gidan! miyasa bakizo dashiba, mantawa nayi dashi.
Gobe zamuje ki dauko kayanki da kuma takardar Allah ya sakamiki! ana cewa ya natsu ashe da sauransa, ni da ganin idinsa nasan baida kirki mutum banza ay dama nasan zaiyi fiye da haka! Inna ta kalleshi rai a bace waikai lafiyanka? waya gayamaka ana shiga tsakajin mata da miji, wallahi zasu baka kunya daga baya ana ma magana kamaida ni mutuniyar banza, ai inna duk ke kika janyo tun farko ni banso auren nan ba amma kika nace sai anyi sannan yanzu ga wullakancinda yayi mata kina cewa abari sai anga takarda, kawai inna kisa mana ido dan ba kara bari zamuyi mu maimaita kuskuren farkoba dole in nemawa kanwata yanci dan anga bamuda uba.
Karo na farko da yaya yaki sauraren inna idan tana magana, haka idan tanamagana ya maida mata amsa, mamakin duniya yacika inna tasaki baki sululu tana kallonsa, Lallai baitaba mata hakaba, kawai bari ta barshi har ya sauko sannan su fahimci juna.
ASHE KAINE MIJINA - 58
har ya sauko sannan suyi magana su fahimci juna, ya tashi fauuuu, har yakai kofar fita ya juyo ke nazia zo muje, na kalli inna naga ta dauke mana kai na fuske abina nabi yaya ina dan dingishina.
part din yaya muka wuce da yake an gyarashi tunda yaya ya kusa aure da zainb khalifa, mukaje sashensa muka zauna a parlour yaya yaso yamin magana amma ganin fulmar yanda na harkitse yasa yaja bakinsa ya dinke, amma ransa a bace, ki shiga dakina ki kwanta ni zan kwana anan kamin gobe muga yanda za'ayi, ba musu na amince dan bayana kamar ya bude dan zafi gashi na jike sharaf dajini, ina bukatar zagayawa in kimtsa jikina, na tashi naje dakinsa, direct bayi na wuce dan in gyara jikina saidai kuma ba pad sai da tissue nayia mfani na watsa ruwa na fito, ina fitowa na nemi guri na baje. Abinka da mara lafiya ga gajiya nandanan bacci yayi awon gaba dani.
A bangarennura ko kuma muce deen, yagama rudewa ya zare kamar wani dan gwaya, dama hulwarsace matarsa? dama itace a gidansa bai saniba? yanzu tana dauke da cikinsa! waima ya zaman cikin yake shege ko mai uba? dana ba shege bane! dana dan halal ne koda bada sanin junan mu muka sameshiba, dayan bangaren zuciyarshi ya bashi amsa, ina kaunar dana fiye da raina! lokaci daya kirjinsa yayi wani mummunan bugawa daya tuna cewa ya saketa! ya tuna wullakancin da yamata, anya zata yafemin kuwa? bangaren zuciyarshi ya bashi amsa da zata yafe masa tunda tana sonsa! amma yana tunanin bazata taba yafe marba.
Yafi yarda da cewa bazata yafemar ba, kuka ya saki kamar karamin yaro ya durkushe kasa lallai na yaudari kaina na yaudari soyayyar da hulwaty ta nunamin.
ASHE KAINE MIJINA - 59
ta nunamin, ya rasa yanda zai yi da rayuwarsa, zuciyansa kamar ta fito dan bakin ciki da damuwa babban burinsa ta isa gida lafiya! waima da wane ido zai kalli iyayenta dama nashi iyaye iyayenta sun mai karamci tun tana jinjira ya nemi a bashi ita kuma aka bashi aka ijiyemasa ita tun lokacin har ta isa aure lallai ya zalunceta, koda baya sonta baidace ya mata abinda ya mataba, kodan karamcin da iyayen ta suka mai, mizaicewa iyayensa idan sukaji cewa ya saketa? yanzu yake tuna maman nihal ta taba cemar nazia nada ciki yana kallonsu wani iri har yake ce musu shi ko ganinta yayi bazai ganeta, ashe da gaske hulwarsa tana dauke da cikinsa.
Lallai ya tsuke tunaninsa ya akayi bai ganetaba? ya akayi bai gane sunantaba. Ta taba gayamin sunanta nazia amma tace babanta yana kiranta da hulwa, so tafison sunan shi yasa bai gane sunanta na asali ba, ya tuna lokacinda zai siyamata ticket daga abuja zuwa sokoto yaga sunanta Nazia muhammad amma baiganetaba, duk tunanin daya dauko baya kaiwa karshensa, yaga ba yanda za'ayi ya ganeta, amma hadda jahilci yayi mai yawa, yanzu yatuna ya kirata hulwarsa da jahila ashe nine jahilin nine dakikin nine azzalumin yaci gaba da kuka hadda gunji kamar karamin yaro.
Nihal tana parlour tayi jigum tajiyo kamar ana kuka ta lekoo taga lallai uncle dintane yake kuka! itakam ta rasa gane komai duk tunaninta bata samun amsa, lokacinda zata iso Mamanta tace kada ta rika barin antin nata da aiki dan tanada juna biyi (ciki) lokacin da tazo uncle da aunty nazia sun nuna basu ma san juna ba. Duk tunanin ta bata sami amsaba, taja ta tsaya kofar dakinsa. tana tsoron ta shiga dakin ya balbaleta da masifa gashi ya gargadeta, ganin kukan da yake ya tsananta da wani gunji da yake yasa bata tsaya wata wataba ta fada dakin taje gunsa cikin tsoro, uncle meyake faruwa.
Kamar baijitabata kara maimaita tambayar har saida ta tabashi da jarfi sannan ya dago ya kalleta yanda taga ya chanza ya hargitse lokaci daya abin ya bata mamaki da tsoro, kodai yanada aljanune? ta kalleshi uncle mi yake faruwa? ya kasa magana amma dai ya daina kukan da yakeyi, ya dago ya kalleta abin tausayi dashi " koda ni jabo bancika jin tausayin mazaba dan basuda kirki amma yadan bani tausayi kadan? " ya bude baki nihal zaki timakeni.
Yesuncle zan taimakeki kinyi alkawari! Yes nayi, Duk wahala? Yes! nihal talk tome ina cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali kimin alkawari idan kowa ya gujeni ke zaki tsaya tare dani zaki rufamin asiri.
Uncle na maka alkawari duk wuya duk wahala zan kasance tare dakai har karshen rayuwata, kuyi hakuri kun jini shiru wallahi nayi busy ne da yawa wannan ma a train na rubuto mukushi idan na dawo zan kammala.
ASHE KAINE MIJINA - 60
Har karshen rayuwata, Yaji dadin alkawarin da nihal ta daukar masa yasan kuma akwai ta da jajircewa akan abinda takeso idan har ba wulakanci a ciki, ta yarda dashi saidai tunaninsa daya ya zasu bullowa abin? Dolene ya gayawa nihal gaskiyar abinda ya faru anya zai iya kuwa? tabbas bazai iyaba zai tonawa kansu asirine kawai wannab sirrine tsakaninsu baidace kowa yajiba. zaidai san yanda zai bullowa abin. Nihal dai tana zaune tana kallon uncle dinta duk da ya daina kuka amma yana wani gunguni gunguni dukkan alamu dai ya zautu ta kira sunansa uncle ya dago ya kalleta, au kinanan? AiKina iya tafiya, tace to, ta tashi ta tafi cike da sake sake a ranta haka yaci gaba da tunane tunanensa yana kuka har barci yayi awon gaba dashi.
Bai farka ba sai guraren asuba ya tashi idonsa sunyi hulu ba kyan gani. Maimakon yayi sallah sai ya wuce dakin hulwarsa yana shiga ya dauki turarenta yana shinshinawa hadi da hugging din kwalbar turaren yana kwalla kamar wani zararre ya tashi yana yan tabe tabe tabensa har yakai gun wayarta battery low ta mutu ya jona chaji komi yake nema oho ya dauko hand bag tinda yana lakube anan yayi karo da takardar sakinta da magungunab! Bai duba maganin kona miye ba tunda yasan tanada ciki zai zama maganin masu cikine. Aranshi Wato bata tafi da takardar ba "yama manta da cewa suma tayi a hanyar hospital ta farfado tace a kaita gida" lokaci daya bakin cikinsa ya dawo farin ciki yayi wani murmushi bada bata lokaciba ya shiga ba yinta ya yayyaga takardar yayi zuba a bayi yayi bayan gida akai? ya korarowa yayo alwula yaje yayi sallah.
Allah kadai yasan abinda yake sakawa a ranshi har gari ya waye yana lazimi akan Allah yasa ta yafe masa su dawo normal.
Yazo ya sami nihal ta hada mai break fast bai iya ci sosai ba yadan taba dai kawai duk dahaka nihal tayi mamakin sakewar da yayi akan jiya. Nan zarginta ya kara tabbata akan uncle dinta yanada jinnu dan su suke haka one time kuma kamar ba'ayiba.Taso suyi magana sai kuma ta basar tunda jinnu ne bazai tuna komai ba. Nazia bata farka ba sai guraren 8 na safe duk jikinta ya kara ciwo sabida batasamu tasha maganiba, ta rarrafo tazo palo ta sami yayan ta bayanan tasanba gurin aiki yaje ba dan sai 10 yake tafiya aiki, tayi tunanin bari taje kitchen ta hada tea ta kora tana zuwa taga yayanta tana fere dankali abin ya bata dariya dan bata taba ganin yaya a kitchen ba, duk ya zubar da rabigarin ferewar aranta tace lallai zainab khalifa zatayi fama ko irin mata bataji dadiba miji ya tayata girki da dan ayuka yaya kam ba abinda zai tabuka.
Ta kalleshi ta gaidashi ya amsa cike da fara'arsa hadi da tausayin yar marainiyar kanwarsa! kin tashi tace yes! Ka kawo In karasa yace aah ki barshi zan karasa kina bakuwar tawa sukayi dariya. Ai yaya a wannan duk ka zubar da rabin dankalin yayi murmushi ina practice ne kamin maaadam tazo dariya ta kamani amma na fuske wato zainb khalifa ce maaadam. lallai rayuwa mai juyi da yanda yaya ya tsani zainb khalifa amma yanzu itace wacce yake burin ta zama uwar yayansa.
Kije ki shirya muje gidan wancan yaro ki dauko takardar sakinki da kayan bukatarki.
No yaya muje a haka kayana duk suna chan gidan. Kije ki duba wardrobe dina zaki ga kaya ki zabi daya ki saka Naje dakin abin ya bani mamaki ganin kayan mata kamar wani karamin store ta dauki wani dogon riga baki ta saka duk da ta rame amma kayan su. Karbeta sosai.
Koda ta fito harya kare hada musu break fast ta zauna suka ci lallai taji yunwa rabonta da abinci tun jiya da safee! Suka fito sukaje sashen inna suka gaisheta ta amsa ba yabo ba fallasa suka gaya mata zasuje gida nura in dauko takardar sakinna da kayana har sunkai bakin kofa inna tace ban yarda kuyi chin mutunci da kowaba yaya ya amsa da insha Allah. Suka isa unguwar tunda suka isa unguwar kirjinta yake dukan uku uku har suka isa gidan suka iske gidan a bude suka shiga nihal "sister khadija" sukayi karo da ita a pallow tana chatting fuskarta cike da fara'a da gani ita da ammar suke soyewa koda bansan still suna tareba.
Tana ganin mu tayi shock zunbur ta miqe ta gaidamu cike da fargaba yaya ya amsa mata rai a sake direct dakina na wuce abu na farko danayi karo dashi yasa nasan an mini bincike dakin cike da kamshin turarena kamar anyi wanka dashi hand bag dina komai an juye a saman gado waya a chagi haka daita tattare kayanta na bukata amma ta nemi takardar sama da kasa bata ba labatinta, wayarta ma dagyar ta ganta dan a chaji take ta fito a sanyaye tacewa yaya bataga letter dinba da kuma yanda ta sami dakin anan suka gane yayi bincike ne kuma shi yadauke takardar ran yaya ya baci matuka ya kalli sister khadija ke ina nura? Bakinta na rawa tace Yaje office ya dauko wasu takardu har suka gama zaman jira bai dawoba an kira wayar a kashe suka tafi gida sunje sun ma inna bayani tayi tagumi batace komai ba.
Anan aka zauna ake tambayata da wane dalili ya sakeni yaya yake cewa kodaida nihal kuka sami sabani nace aah na rasa abinda zan fada.
ASHE KAINE MIJINA - 61
Na rasa abinda zan fada na sake fashewa da kuka, shikam yaya ya rasa abin fada sai kawai ya tashi ya fita abinshi nayi kukana, inna dai taga kukan bamai karewa bane tazo tana rarrashina har nayi shiru.Guraren magareeb yaya ya dawo ya sameni nadan saki jikina baicemin komaiba har zai fita inna ta kirashi ta tashi ta shige daki ya bita baya bansan mi suka tattaunaba naga sun fito abinsu.
Ya kara wuta inna bata min magana nima bance musu komai ba har nayi Kwana biyu a gida. Ina duba wayata da yake na dan saki jikina kadan kuma na warware rashin lafiyarda nayi dan inashan magani akan kari. Ina karanta wani hausa novel a group din hauwa m jabo sai wata tace amata sending din wani picture ina dubawa kawai naci karo da hoton takardar sakina dana dauka zan nunawa deen lokacin dan inason inyi surprise dinsa, sai yacimin mutunci yace bani bashi "dama na nuna mai tun lokacin zai gane tunda rubutunsane" sai naji maganar yaya da inna da guduna na fito na na nunawa yaya hoton takardar sakina yana dubawa baice komai ba ya ma inna bayanin takardar inna tace saina fadi dalilin sakina naga dai boye boye ba nawa bane saikawai na bayyane musu komai na gaya musu bai taba kusanta naba yaya ya kalli inna inna ta kalli yaya cike da mamakin maganata sai inna tayi karfin hali ke dan mijin ki ya sakeki kada ki maida mu mutanen banza, kinason kice cikin da kike dashi ina kika sameshi? Ko kin dauka dan baki gaya mana kinada cikiba mu ba zamu ganeba ki chanza wata karyar ba wannan ba.
Inna ta karkade zaninta ta kara gaba ta barmu da yaya ya juyo ya kalleni yazo kusa dani ya zauna.Ya dafa kafadata nazia kiyi magana ki fadi gaskiyar abinda ya hadaki da mijinki wani ki mai sharri ko qire ko kage duk bai taso ba ki fadamin gaskiyaa kinji autar inna! Na fara rantse rantse akan ba abinda ya taba shiga tsakanin mu dashi iya abinda na fada shikenan ba wani ciki da nake dashi kawai dai nayi jikine hatta honey moon da mukaje kowa da ban ya tafi abinsha haka dai nayita tona asirin zaman mu amma ban fadi yanda muke dashiba.
Yaya kam ya gamsu dan bai sanni da karya ba dama shi baiga ciki ba inna tabashi labarin cikin wacce akace tanada tace ba haka bane miye nasu na karya tawa.
Ya shiga sukayi magana da inna ya fito ana maimaita maganar cike da jimami. Zamu jirasu zuwa karshen sati idan har danginsa basuce mana komai ba zamuje mu kwaso kayanki dan ba komawa zakiyi gidannan ba, nura da nihal sun rasa yanda zasu bullowa lamarin nura daikam ya dawo kamar wani almajiri sai tarin kasun ba dayatara duk wanda yaganshi ada yaganshi yanzu yasan yana cikin wani hali, su kitsa su warware duk yanda zasu bijirowa iyayen zancen saki ba tare da tonon asirinsa ba a maida nazia sun kasa samun mafita nura ya rasa yanda zaiyi, ba wata mafita da yake da ita idan yace baitaba kusantar ba to cikin na uban waye waye.
Ga son duniya ya dauka ya gwallafawa cikin nan hawaye ne suke gangaro mai na nadamar abinda ya aikata nihal har ta saba da ganin kuka uncle dinta tuntana mai kallon mai jinnu har ta gane tsabar son da yake yiwa nazia ne da damuwar da yake ciki. A karshe sun yanke shawarar kada su gayawa iyayensu ita nihal karshen wannan satin zataje gidansu nazia suyi magana."kaji wauta irinta yara wai nihal zataje biko"Nazia dai kam inna ta yarda ba tada ciki tunda bataga cikin ba yanzu kuma alamomi sun nuna haka tunda lokacin kullum idan sunyi waya da nura daga yace baya gida sai yace yana kan hanya sai yace tana bacci ko tana sallah hakadai bai taba baiwa nazia sun gaisaba kullum kwana kwana yake mata shimayaya ya yarda dan shima kusan haka ta faru ya kira nazia ina nura tace baya gida ya kira nura ya nazia yace tayi bacci bayan daidai likacin suka kare waya yayi tunanin wani abu saidai bainkawo komai a ransa ba haka dai kowa ya rika fadin albarkacin bakinsa.
Nazia bakin cikin wulaqancin da deen ya mata yana damunta amma ba halin fada dan ita ta janyowa kanta sonsa ya rufe mata ido yanxu ga abinda ya mata tasha alwashin duk ya kuskura yazo gidansu sai tamai kaca kaca.Yau suka shirya kwaso kayanta da la'asar guraren biyu saI ga nihal a gidan inna dai kam bata ganeta ba tace gun nazia tazo. Inna ta kira mata nazia ta shige dakinta. Nazia ta fito da fara'a wa zata gani makiyarta sista khadee. Nazia Ta wani daure fuska tasha magani ta zauna akan hannun kujera ta dora kafa daya akan daya tana girgizawa tana shan sweet, sister khade ta gaisheta ta amsa da lafiya a takaice.
Gunki nazo, aunty nazia idan zaiyiwu mu shiga daga ciki, No. Nan ma is ok nazia ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba.Ta hadiye yawu tayi kasa qasa da murya. Dama aunty akan maganar.Ta dakatar da ita da hannu. Don't ever called me your aunty, am not & i will never be the one. I can hear you go ahead. Ta kara kawar da kanta gefe. Ninhal Tayi ajiyar zuciya dama akan maganar uncle ne nazo dan Allah, nanma ta kara katseta.
Shot your mouth up! you thinkless, do to most disgraced embrassemented matter you already done to me & your inrespective your mannerless, uncle do! But your came with another ovios alonatic thinking? to let me tell you, kije ki fada ashawon uncle dinki idan ya isa yazo da kanshi ke banida lokacinki wawaye kawai, ran sister khadija ya bala'en baci taji maganar har cikin ranta tasosu kuma taji haushin maganganun nazia amma ba yanda ta iya tazo gyara tayi barna.
Ta dago ta kalli nazia taga yanda ta daure fuska tasha jinin jikinta ta rasa abin fada chan nazia ta juyo. Get out of this abode.! before I disgraced your personality now! Think less, stupid people haved to go and find an approach of manners & valuable of any mankind has wasing to you. Oya ga hanya ta nuna kofa get out. Ta fada da tsawa.
Sister khade ta gama kulewa tasan idan har taci gaba da zama faruwa naci ba nata bane mutuncinta yafi mata komai ta dauki jakarta ta fita kamin ta fita tajiyo tsakin nazia think less kawai. Nazia tasani sarai sister khade batason tsaki tasha fada da mutane a secondary school akan tsaki dan kuwa da kamata tsaki gara ka waska mata mari, har ta tsaya sai kawai ta wuce rai a bace.
Ta fada mota taja dakarfi tana fotowa gidan taja ta tsaya tana kwalla, lallai nazia taci mata mutunci da yake tasan weak point dinta shi yasa ta mata haka anya zata iya cika alqawarin da tayiwa uncle dinta kuwa da wuya dan bata daukar raini gun kowa wallahi, ta share kwallarta taci gaba da driving kamar zuciyarta ta fito dan baqin ciki ita zata cire hannunta dan tasan nazia da bala'en tsiwa komai zata iyayi.
Idan kuma ta juyawa uncle dinta baya wazai taimakeshi. Dayan zuciyarta tace wanda yasa ya saketa ya taimaketa....?
0 Comments