f Ashe Kaine Mijina - 62 to 69

Ashe Kaine Mijina - 62 to 69

 

Ashe Kaine Mijina - 62 to 69


            ASHE KAINE MIJINA


ASHE KAINE MIJINA - 62

S ister khadija Tana tafe tana tunani yanda zatayi, karshe ta yanke shawarar zame hannunta daga lamarin baki daya, ko banza batasan abinda ya hadasu, ga rainin irin na nazia da bazata daukeshiba tayi tayi uncle ya fada mata abinda ya hadasu, saidai yace just help me nihal! a hakan zatayi helping dinsa batasan abinda ya hadasuba? kawai zan koma gidane bana ganinsa  ma bare ya bani tausayi! Da wannan tunanin ya isa gidansa koda taje ta tarar baya gidan ta tattara kayanta tayi gidan su, mamanta na ganinta taji tsoro kardai kun saida hali da matar uncle din naki? Da yake ke nihal bakida hali ga zuciya kamar ta kasheki naga fuska duk a turbune.

Sister khadija tayi murmushi ta nemi guri ta zauna to umma yau baki chankaba, ta kwashe duk abinda idonta ya gano mata ta fada musu kuma lallai alamu sun nuna baima taba ganinta ba itama haka. Maman nihal tayi dariya! kefa har yanzu yarinyace wata kila sabani ya hadasu amma mace hadda ciki kice basu taba ganin junaba. Nihal dai tayi kokarin yiwa umna bayani har saida umma ta gamsu da dalilan da ta kawo mata dan kuwa taji har ya saketa da kuma ta fada mata da bakinsa ya fadi ya saketa din, amma kuma nihal din tace abinsa harda aljanu kam. Amma bari baban fati "abbansu nihal kenan" ya dawo muji yanda abin yake.

Ran nazia yayi fari sol ko banza ta gaya mata magana kuma tasan ranta zai sosu, taso taqi fita ta hadata da karen gidansu amma sai ta tafi. Ta shiga daki cike da farin ciki tasha maganinta ta shirya tana jiran yayanta. Bada jimawaba yazo suka je gidan mai gadi ya bude musu gidan suka tattara duk wani abu da sukasan nasune suka kara kaba.









Bayan isha saiga nura yazo gidan yana neman nihal yaga gida wayam!Ba nihal ba kayan nazia abin ya bashi mamaki wato ya tura nihal gyara ta maibarna ko? Zai kuwa chi ubanta! ( kaji wawa) yaje gun maigadi a firgice yana tambayarshi ya haka maigadi yamai bayani daga zuwan nihal har zuwan su nazia yana karewa nura ya wankeshi da mari kaji tas! kuma yace sai ya dawo da kayan da suka diba dan bai bashi umurnin barin kowa ya dauki komai a gidan ba! (kaji hauka ina ruwan maigadi ai sai yace sai ya dawo mai da matarsa bawai kayan matarsaba)

Magadi yayi tsuru tsuru ya riqe kumce yana bada hakuri nura ko saurarensabaiyiba yace yabar mai gidansa ya sallameshi ya wuce cikin gida a fusace, Dama su nura an iya kuka ya zauna tsakiyar pallow ya fara kuka ba mai rarrashinsa cikin kuka ya jiyo magana sama sama koda ya duba sai yaga abbannihal tsaye yazo gabansa yaja ya tsaya yamai kallon banza ganin gidan bakayan nazia ya kara tabbatar mai da cewa lallai ya saketa, Bai tausayawahalinda yaje cikiba ya haushi da masifa. 

Karshe yace yadauka yazama mutum ashe har yanzu da sauransa! Sabida haka ya tattara kayansa ya bar wannan gidan dama albarkar nazia aka bashi wannan gidan nura ya tsananta kukansa basu barshi da bakin ciki rabuwa da mataraaba suna kara mai wani bakin ciki.
Yayan nura yayi waya gida ya fadawa mamansu da babansu abinda yaronsu yayi itadai kam maman nura da taji abin kasa magana tayi dan tsananin bacin rai, nura baiyi halacciba sai kallo kallon suke itada mai gari "baban nura" maman nura tace a kira inna amma mai gari yace wannan mugun abin ya wuce waya saidai su tafi. da kanmu har gidan, tun da asuba iyayen nura suka baro kauye sukazo birnin sokoto. Bayan sun dan huta suka kwashi jiki sukaje gidansu nazia bawai biko sukaje sunje bada hakurine.




Koda Inna batasan zuwansuba ta musu tarba cikin mutunci da sakin fuska kamar ma ba abinda ya faru amma maman nura ta kasa koda hada ido da ita. Inna kam Sai neman ayi hirar bayan rabo takeyi amma duk sun kasa kunyar abinda dansu yayi ya ishesu. Chan dai maman nura ta fashe da kuka ta rungume inna tana bata haquri. Nura vai kyautaba! Baiyi halacciba! Yaci amanarnazia, hakadai tayi ta sunbatu. inna nafadin babu komai har dai itama tafashe! dan abin ya dade yana cinta inna kuka maman nura kuka dagyar dai mai gari ya samu ya rarrashesu sukayi shiru cike da kunya shima.

ASHE KAINE MIJINA - 63

Mai gari (mahaifin nura) yaci gaba da maga. dukan mu bamusan abinda ya faruba jiya ake gaya mana abinda ya faru, dan Allah kuyi hakuri yaron ne basu da hankali kwata kwata, basu san halacci ba da nura yasan halacci da nura ko bayason nazia ai dan darajar halaccin da kuka masa yaci ace ya zauna da yarinyar nan, maigari dai yayi maganganu na ban hakuri karshe yake tambayar lafiyar nazia da lafiyar cikin ta. Inna ta musu bayanin da nazia tayi na cewa basu taba hada shinfidaba mamaki ya kama kowa ganin yanda ake fadar tanada ciki duk dangi sun sani amma yanzu ace ba ciki. Basu isa su karyataba.

Ana nan mai gari yaci gaba da cewa yanzu sai ayi hakuri a maida auren inna batace komaiba sukayi ta bata baki har tace Allah yasa hakan yafi zama alhairi ana haka saiga yaya hafez ya shigo shida zainab khalifa su zainb ana wani iyayi an sami saurayi dan gayu , suna zuwa suka gabaki a gidan sama sama suka gaisa zainab ta wuce gun nazia, yaya ya zauna ayi dashi anan mai gari ya fadawa yaya bukatar su ta da amincewar inna akan maida auren. zunbur ya mike. Bazata yiwuba! Akan me kuke playing dinmu? Ko dan kunga mahaifin mu ya rasu? to nine gatan nazia kuma nice mahaifinta! idan har kukaga ta koma gidan wannan yaron to ita ta bukaci hakan. amma baza'a kara wulakantamin yar uwaba ya buga rigarsa zai fita.











Inna ta mike zata cimai mutunci akan rashin kunyar da take ganin yayi. mai gari ya takatar da ita yaje ya janyo hannun yaya hafez ya zaunar dashi. Hafizu bazamu taba tursasa nazai akan ta koma gidan nuru ba abinda kawai mukeso shine kada wannan zumunci namu ya lalace. idan har basu shirya kansuba zan turo Dr mustafa yaron kanina watakila su daidaita kansu banason abinda zaisa zumuncin mu ya bace , maman nura bataji dadin hadin da mai gari yake shirin yiba tace insha Allah ma zasu daidaita kansu haka daizaman ya kasance har guraren azzahar.

Suka kwashi jiki sai gidan su sister khadee mai gari yasa aka kirawo masa  nura bai bata lakociba yazo ganin yanda ya zama lokaci daya abin ya basu mamaki da tausayi! Jikinsu yayi la'asar maman nura ta kalli autanta tama manta da aika aikar da yayi ta taso ta rikeshi tana tambayar lafitar shi. Ran yayan nura ya baciganin yanda mamansu ta rude ganin halinda danta yake ciki ya daka mai tsawa hadi da cemai munafuki wallahi mama kuk kuke kulashi iskancine kawai.

ama ta dalla ma abban nihal harara ta zaunar da shi, Pallow yadau shiru chanmai gari ya fara yiwa nura bayanin abinda suka sani hankalin nura yayi mugun tashin dajin cewa tace basu taba hada shinfidaba, kuma batada ciki kenan ta zubar mai da ciki? Cikin da ya daura ma son duniya! Cikin da yake tunanin shine zai taimaka masa su gyara auren su, Ya saki wata irin kara saidakowa ya firgita a gurin yace...?

SHE KAINE MIJINA - 64

wallahi ni ban saki nazai ba! kuma karyane tace bamu hada shinfidaba har cikina tana dashi wallahi! kenan ta zubar mun da ciki? Kowa yayi tsit! sai kukan nura ke tashi a pallow jikinsu yayi sanyi yayan nura yace dama nihal tace aljannu ne suka shafeka, inaga yafi kyau a bari sai yaji sauki sannan ayi maganar, nura ya dallama yayan sa wata muguwar harara idonsa cike da hawaye sunyi jaa cike da fushi yace kaine mai aljannu baniba damaka tsaneni baka sona daaga yau kai ba yayana bane, Duk pallow saida kowa ya yayi dariya da maganar mallam nura autan mamanshi, suka kara tabbatar da cewa yanada rashin lafiyar jinnu. dan kuwa ko musu bai taba hadasu da yayan saba kuma yana tsoronsa fiye da yanda yake tsoron iyayensa.

Amma yana mai irin wayannan maganganu. kowa sai ya gasganta maganar abban nihal. Ya taso yazo ya rungume kaninsa yana rarrashi cike da tausayi shi kuwa sai wani kace jikinsa yakeyi! Haka dai zaman ya kare ba wata natija.










Da dare maman nura ta bi nura dakinsa suna magana ya kara jadda dama abinda ya fada farko cewa bai saki nazia ba idan ya saketa kuma ina takardar saki? Nan fa duk da cewa tana mai kallon mara lafiya ta gasganta maganarsa. Bayan ta fito ta samesu a pallow suna tattauna maganar akan a nemowa nura magani anan maman nura tace idan har da gaske ya saki nazia ina takardar sakin take? yaka mata fa idan za'ayi abinnan ayi adalci bai yuwa ace autana ne kawai bashida gaskiyaitama da laifinta. Sukayi shiru lallau yakamata ace ga takardar saki bawai kamar yan da inna ta musu bayaniba wai sakin a waya ne. Haka dai aka kareakan za'a nema mishi magani idan yaji sauki sai a hadasu su biyu a aji gaskiyar maganar.

Haka kuwa akayi an kai nura gun mai ruquya aka danna mai maganguna da hayaki kala kala. kamar gaske bayan kwana uku yadan da normal amma fa bai daina hararan yayansaba kuma baya gaidashi ba yace duk ya hadu da nihal sai ya kakkaryata dan gani yake zuwanta gidan su nazia yasa komai ya kara lalacewa bayan tace zata taima keshi.....?

ASHE KAINE MIJINA - 65

An shirya zama kowa yazo Haddad su nihal an hallara. Aka fara maganar kowa ya fadi albarkacin bakinsa amma nura yaki saukowa akan cewa ya saketa. Akayi sama akayi kasa amma yaki yarda yace idan har da gaskene to ta kawo shaida a rubuce dan ba zasu yarda da waya ba, wannanzamanin komai ana iyayi. Karshe nazia taga ba nasara a gunta ta mike taje daki ta dauko qur'ani tazo gabansa ta tsuguna ta miqa mai qur'anin tace idan har yayi rantsuwa da wannan qur'anin akan cewa bai saketa ba, zata koma gidansa yau dinnan.

Nura ya rasa yanda zaiyi sai zufa ke keto masa! Chan dabara ta fado masa ya karbi qur'ani yace zaiyi rantsuwa amma itama tayi alkawarin cewa zatayi rantsuwa akan cewa basu taba hada shinfidaba kuma bata dauki cikinsa wata huduba, Qakakara kaka.
Suka fara kallon kallo tsakaninsu pallow yayi tsit ana sauraren wannan lamari nasu! Nazia ta karbi qur'ani jiki a sanyaye tace kamin ka rantse ni zan rantse. ta rike qur'ani hannu bibbiyu ta rufe ido tana hawaye.









Tace Ni nazia muhammad na rantse da darajar wannan qur'anin! A matsayinana matar nura ta sunna bai taba kusantana da sunan raya wannan sunnar aure ba daidai da second daya saidai ya, tuni nura ya taso yarufe mata baki ganin zata fallasa sa dayan mugun aikin da suka aikata, wanda baya fatar hakan ta kasance har karshen rayuwarsa! Bayason Iyayensa susan halinda ake ciki. Tausayin nazia ya kama kowa yayan nura ya haushi da fada akan me zaka hanata fadar gaskiya? Ta tabbata kenan bakada gaskiya! kamaida mutane sha sha shai. Yayan nura yazo gaban nazia yace mata nazia ci gaba saidaime? Nura baisan lokacinda ya juye bakiba da harshen farisanci da suka koya tare da nazia tun kamin suyi aureba yace mata (( nazia turo khuda asrari moro pakhsh nakun na bi khatiri man bi khatiri khuda)  tadago ta kalleshi harga Allah ya bata tausayiba yanda ya hargitse da kuma yanayjn sautinsa ko banza tana sonsa ta kalli yayan nura tace mai ba komai.

Nura yayi ajiyan zuciya yayansa ya kalleshi ya rasa bakin magana tunda baisan mi yace mataba, (( nima hauwa jabo saida na tambaya aka fassaramin abinda yace kuma bazan fassara mukuba) nihal ta taso tazo ta karbi qur'ani itama tayi rantsuwa akan cewa lokacinda tana gidan uncle ya fada mata da bakinsa ya saki nazia yakai sau 50. 

Ta fadi yana yawan maimaita cew a ya yaudari nazia ta taimaka masa. Mai gari yace kada ku maida qur'ani abin wasanku mana. Ya karbi qur'ani hannunun nihal ya koma ya zauna kowa yayi shiru ana jiran gogan naku nura mayaudari yayi magana amma kamar ruwa yacishi yayi tset.

ASHE KAINE MIJINA - 66

Nura mayaudari yaki magana kamar ruwa ya cishi yayi tset Pallow ya dauki shiru kusan minti uku ba wanda yayi magana ana sauraren nura mayaudari.

Chan ya dago kai ya kalli hulwarsa yaga yanda take zaune a natse amma da gani a kwai damuwa tattare da ita tausayinta hadi da wani kaunarta da yakeji ya kara kamashi, ya tuna maganganunda ya fada mata lokacinda tace tana da ciki wato zafin maganar ne suka sakata ta zubar da cikinsa kenan? miye laifinta ma tunda shi yace ta zubar ba ruwansa! Idonsa sun cika da kwalla ya sunkuyar da kai yace.









Baba lallai na saki nazia saki daya! Lokacinda na saketa bansan cewa itace matar tawaba! Kuma ni dauke takardar sakin dana mata na yaga dana fahimci itace matar tawa, dan wallahi inason nazia baba fiye da yanda nakeson raina bazan iya ruyuwa ba itaba yana magana murya na sarkewa.

Maigari yace alhamdulillahi dama munason muji gaskiyar magana, kuma gashi kun fada da bakinku. amma cikin maganganunku akwai abubuwan da ban ganeba.

Kace lokacinda ka saketa bakasan itace matarkaba! Kenan kasanta tun farko kenan?Itama tace baku taba saduwa da sunan aureba saidai, sai ka hanata karasa magana wanda yake nuna kamar kunsan juna kamin aure ko makamancin haka.

Sai maganar ciki da kakeyi wanda kowa ya shaidi tanada ciki kuma akazo aka rasa cikin yanzu. Ka nuna baka taba saninta ba baka ma taba ganinta ba ya akayi kasan tanada ciki? Hakan ya nuna akwai wani boyayyen lamari da mu bamu saniba Lanada kyau muma a mana bayani.

Lokaci daya nazia da nura suka kalli juna kamar hadin baki sukace wallahibaba! sai dukansu sukayi shiru, babu kom, nan ma hada baki sukayisuka kara yin shiru nura ya karasa maganar da cewa baba ba komai tsakaninmu baba! Maigari dai bai gamsu ba sauran mutane ma tambayar maigari ta sakasu cikin tunani yanda suka hada baki ma ya nuna rashin gaskiyarsu a bayyane, yaya nura yace tunda dai munji haqiqan abin shikenan wani bincike bai tasobababa koma miye wannan tsakaninsu ne rashin kyautawa ne dai nura ya riga yayi muna dada bada hakuri. inaga shikenan kawai. anan dai akayita bada hakuri akan kara abinda nura yayi aka shigo da maganar komawar nazia, yaya nazia yace abarta ta huta daga baya ayi wannan zancen, nazia da karfin hali tace ni na bazan koma gidansa ba na amince idan na kare idda zan zamu daidaita da Dr mustafa idan mun shiryasai muyi aure.

Ke hulwaty! Kinada hankali kuwa? Kinsan abinda kike fada? Da aurenki kina tunanin wani namiji ko? Ta dalla mai harara da murguda baki aure kuma? Ai yanzuu hulwa ta mai raboce haka suka fara musanyar magana sun ma manta akwai mutane tare dasu kowanne cike da kishi da bakin cikin rabuwa da dan uwansa.









Harga Allah nazia dan ta bata masa rai tace zata aminta da Dr mustafa bawai dan tanasonsaba. Dukansu abin ya basu dariya yayan nura yace shikenan ya isa! Nura ya kalli yayansa cikin kwalla yace yaya kanajin abinda take cewa ko? Nura yama manta da baya ma yayan nashi magana! Tausayin kaninsa ya kamashi yace kayi hakuri ta bari zamuyi magana daga baya! Haka dai abu ya qare, zaman baiwa nura dadiba idan ya tafi ina zai kara ganin hulwarsa. Kowa ya watse aka kara kaba.

Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah yau wata shida abubuwa sun faru na baKin ciki da farin ciki nura ya zautu kamar bashiba ya dawo ustaz baya magana sosai abinci kadan yakeci ba wanda yake ganin walwalarshi yayi yayi akan hulwarsa ta haqura ammabina taki hakura. 

Yayi kamun kafa gun yayanta sai yace ya nemeta su daidaita ta chanza layi baya samunta. Jin dadinsa daya kin yuwar aurendu da Dr mustafa yanaga da mutuwa kawai zaiyi. Nazo tun kan ta kare idda yayanta ya samo mata admtn a dan fodiyo ta fara karatun ta amma soyayyar mijinta tana mata yawo akai ta tabbata har abada ba zaata daina son deen ba saidai tana barwa cikintane tunda ba yanda zatayi, Kaji sona gaskiya.

ASHE KAINE MIJINA - 67

Yau nazia ta fito lecture tare da sabuwar kawarta da tayi mai hankali da natsuwa Aysha ameen sokoto wacce haifaffiyar sokoto ce yarinyar nimw kaina jabo nakiyaba da natsuwarta amma najma ake kiranta dashi yarinyar akwaiilimi kamar ana mata wahayi ga natsuwa da hankali, abinda yasa tasu tazo daya da nazia kenan duk da nazia akwai tsiwa amma tadan natsu yanzu.

Suna tafe suna tadi har suka kawo gurin cin abinci sunyi letti ba sakwara gashi ita sukeson ci sai sukace to su fita wajen makarantar su siyo a motar najma ameen aka tafi motar sukaje Dady smart anan suka yada zango sunyi sa'a akwai sakwara a gun suna ci suna tadi anan nazia take cewa taji kamshin wani turare mai tayar mata da hankali yanayinta yadan chanza amma ta f uske kada najma uwar wayo ta ganota. sunci sun koshi, suna dati sama sama daga sama taji muryar da ko cikin bacci ko mutuwa tayi ta dawo taji muryar zata ganeta rabonda ta ji muryar wata shida kenan.

Muryar deen dinta ne yake kiranta hulwaty! zunbur Ta mike cike da mamaki ta kalleshi ya chanza gaba daya. ya tara suma a fuska sai kuma ya mata kyau! chan ta tuna da chin mutuncin da ya mata ta daure fuska Malam lafiya? Kawani zo ka tsayawa mutane akai? Najima kinsan shine? Gurinki yazone? Najma ta kurba malt ta kada kai alamar aah. Ta watsamai kallo da dara daran idonta masu rudar dashi tace to malam sai anjimako. Yaja ya tsaya yana kallon ikon Allah hulwa ce take nuna cewa bata sanshiba! Da taga ya kafe kamar an dasa ice sai ta zargu tacewa najima suje.










Suna kan hanya najma tana driving tace waye wannan mutumin na dazu? Nima bansanshiba ta bata amsa a tsanake, Najma ta murmusa dama akwai wayo najma ko hanjin mutum tana gani! Amma acting dinki ya bayar dake nazo, alamu sun nuna kunsan juna! kuma kunyi kewar juna! kuma kunason juna! kuma kun tsani juna! kuma. Is ok phycologist! @ ke haka kike kullum da fassara ni ko mai kama dashi ban taba ganiba sai yau najma ta kara murmusawa naxoo ki gaymin mana duk maganar da najma take bata kalli nazia ba tuqinta take hankali kwance, amma hajiya nazia hadda zufa dan kuwa tarude tasan najma smart girl ce amma batayi zaton zata gane haka da sauriba. Sai ta basar da maganar. kai yaufa zamu shiga hannun Dr shu'aib kinsan bamuyi assignment dinsaba ko? Najma ta ganota sai ta shareta itama ta murmusa tace yes yanzu muje muyi kamin mushiga lectr. ahaka har suka isa makaranta.

Nazia kam duk ta rude ganin deen tsohon abu ya dawo mata sabo, ta samu dakyar aka tashi ranar batayi bacci ba dan tunani.

Nura kuwa binsu yayi a hankali har yaga inda suka shiga.Tun daga ranar dan fodiyyo ta zamo mishi gida har ya gano department dinsu hulwarsa. Ranar nazia ta fito shago ta siyo musu malt najma na hall tana jiranta sai kawai tayi kichibic da nura. Tsoro ya cikata. Haba hulwa miye duniya karki manta deen dinkine masoyinki mijinki.Ta katseshi da daga hannu.

That was then, but now lost substances value & no regard before me.You are completely out of my mind, you are neither trusted nor reliable. Please find your way live me alone.

Bata jira amsarshiba ta kara gaba abinta malt dinda batasha ba kenan zuciyanta tana kuna amma taji dadin maganganun da ta danna mai ko banza tasan ya yaji haushi.. Najma ta kasa gane kan nazia karshe nazia tasa kuka dagyarnajma ta rarrasheta.

ASHE KAINE MIJINA - 68

Bayan tayi shiru ne take tambayarta abinda ya faru anan nazia ta baiwa najma labarin komai amma bata fadi mugun aikin da suka aikataba. Najma ta murmusa I know that! Na fahimci akwai wani abu tsakaninki da wannan guy din tun ranar, na barkine kawai dan naga bakyason maganar.









Amma miye aibi tunda yayi regret ku daida kanku mana? Kinasonsa yana sonki mistake ba wanda ya wuce yinsa inaga kawai ki hakura nazooo ku maida aurenku. Ashe kin taba aure bansaniba, shine idan ana zancen banana kike fuskewa kinuna mana irin u don't now everything. Kai nazoo kin burgeni u are so smart more than me wallahi nazoo tadan dara batace komaiba.

Haka najma tayita rarrashinta tana bata hakuri har tadan saki rai suka rabu akan zatayi tunanin akan shawar da najma ta bata, koda ta aminta saita walfanura.

Nura kam yasha wulakanci kala kala a gun nazia wanda sam baya damuwa burinsa ta amintace masa su maida aurensu. Tunda yakara sakata a ido ya kasa sukuni da walwala kullum yana dan fodiyyo (nidai jabo nace kawai ya nemi admtn makarantar ya fiye masa yawon hanya).

Wannan karon ma nura ya tare nazia tare take da najma ya mata magana kamar yanda ya saba itama ta bashi amsa kamar kullum, ta nunashi da yatsa waike wane irin mutum ne? And I won you not get to any of my bussineesany more. It also look like you don't have human conscious & moral values. Leaves for your own interest. Ta murguda baki ta wuce abinta.

Ran najma ya bace ba kadan ba, kuma tasan duk randa nazo taga nura tamai cin mutunci sai tayi kuka tana dana sani abinda ta aikata Najma ta kalli nuraya bala'en bata tausayi sai ta wuce su dukansu tabar nazai ita kadai tayi kukanta har ta kare ba mai rarrashi.
Ran nazia ya bace wato najma laifinta ma take gani abinda takema nurako duk zata raba jaha dasu. Gobe sai taki zuwa makaranta wasa wasa nazia saida tayi sati daya batazo skull ba ba nuraba hatta najma hankalin su ya tashi nura yaga najma ya daure ya tambayeta tamai bayanin rashin zuwanta ya batahakuri akan kada tayi fushi da aminiyarta akanshi. yakamata ta kira taji lafiyarta tunda bata saba fashin zuwa makatantaba. ya karbi number najma akan zata sanar dashi lafiyar nazoo idan sunyi waya.











Nazai kuwa ta sharawa inna karya da yake inna ba yar boko bace tace sun sami dan hutune. Inna tahau ta zauna. Bayan tafiyar nura najma ta kira nazia amma taki dauka takira yafi sau biyar amma shiru ba labari, bayan lecture ta wuce gidan su nazoo. A pallow ta sameta nazia ta daure fuska najma ta kwashe da dariya taja hannunta tana kwacewa har dai suka shiga daki.

Ta ijiye jaka taje ta gaida inna ta dawo ta bud e fridge ta samu malt daya ta bude zatasha nazoo ta kwace daga bakinta ta harareta tace: dan uwanki nura bai siyo mikiba! Maganar ta baiwa najma dariya tace ya siyomin gata a jaka ba sanyine ta bude jaka ta fito da malt tabude zatashi nazia takara kwace wai baza'asha abin nura a gidansuba. Najma kam dariya Abin yake bata dagyar ta samu nazo ta dan saki jiki sukayi nagana ta fahimtar juna.









Ta bata shawara har cikin ranta taji dadin maganar suka shirya suka dawo kamar basune suke rigima ba nazia har tana tambayar najma da gaske shi ya siya mata malt tace wasa takeyi wallahi ita miye hadinta dashi a hanya ta siya suka tafa ta tafi, najma ta kira nura tamai bayani nazia lafitanta lau da sauran bayanai kuma tace zata taimaka masa. amma bata nuna mai cewa nazia ta hakuraba tadaice yaci gaba da addu'a kuma yaci gaba da mata magana.

Kamar kullum sun fito lecture tace a bari ta samo musu dan cake da malt susha da yake nazia mayyar malt ce ta hadu da wani course mate dinta da yake mutuwar sonta mai suna ahmad. ahmad Allah ya jarabceshi da son nazoo amma daidai da rana daya bata taba bashi fuskaba sama sama duke gaisawa yauma sun dai gaisa sai suka jera tare har shagon suka dawo. A kan hanya ya bata labarin ban dariya ta kyalkyale da daria dago kanta da zatayisai taga deen gabansu ya daure fuska kamar ance maigari ya mutu. Ke waye wannan? Ashe bakida hankali bansaniba? Kina da aurena akanki kike tsayawa tare da samari.

Kin manta, shot your mouth up. Don't ever called me matarka. Am not & I will never be the one! So yafi kyau kasan inda dare ya maka! Ta watsamai harara. ahmad yace malam an rasa hanyar da za'a bullone sai aka fake da cewa matanace so sai a nemi wata hanya bawannan ba. Nazo ba tasan lokacinda ta kamo hannun ahmad ba tace muje ko baby na. Tuni idon nura sun rufe ya wanke nazia da wani wawan mari. Ahmad ya daga hannu zai rama mata nura ya rike mai hannu. Boy! Don't make the mistake of bullying me. And for your information, you made a great mistake the other time because she's married to me, any time I sight you talking with her, you'll rest behind the bars.Ya sakeshi da karfi.

A SHE KAINE MIJINA - 69

Ya sake mai hannu da karfi & ka bace min da gani! ahmad yaji tsoro, ya matsa baya sai na hadaka da security wallahi ya wuce yan surutai ya juyo gun nazia. kada kiga ina nibiyarki ki nemi wulakantani gaban mutane! Ke harkin isa ki rike hannun namiji a gabana wannan ya.

Ta kalleshi ido cike da hawaye murya na rawa ta rasa abin fada mai yaji haush i, duk fasaha ta bace mata. I definitely loved you before I know your dirty hidden color. Learn your lessons as appropriate. I really hate you deen.Ta bi ta gefensa ta wuce ya rasa abin fada waima shi da yake neman sulhu mizai kaishi marinta? Ya dungule hannu ya daki iska ya wuce abinshi. Abin mamaki nazia sai bata fadawa najma abinda ya faruba tunda tasan batada gaskiya kuma ta mata alkawarin zata daina wulakanta nura.










Tana zuwa tace miya tsayar dake haka tace fada na tsaya kallo security sukazo garin gudu aka bigemin fuska. ayyah sannu.

Tun daga ranar nura bai kara zuwa makarantarsuba harkwana hudu. Nazia tadamu tana kallon cewa abinda ta masa ne yasa yaki dawowa gashi ba halin magana,

Nazo zamuje gidan uncle dina na karbo saqon umma please tunda bamuda lecture sai 4, nazo ta aminta sukaje, a hanya najma sai danne dannen waya take a mata sms itama tayi har suka isa gidan ba kowa maigadi ya gaidasu ya basu key suka shiga najma tace ta zauna ta kawo mata lemu. Ta kawo mata lemu ta shiga wani daki ta dauko wasu ledoji ta fita tace mata idan kunshirya ki mini waya inzo mu koma skull. Nazia ta mike tsaye banganeba malama mi, ta budebaki da mamaki miya kawo nura nan gidan? Yasa key ya kulle kofar ya maida key aljihu ya matso kusa da ita tsoro da mamaki suka kamata wato set up ne suka mata ko.

Ta rasa bakin Magana sai ta nemi guri ta zauna. Nura ya matso kusa da ita ya tsuguna yana fuskantarta kamshin turarensa ya daga mata hankali amma tafuske, nura ya fara bata haquri akan marin da ya mata a skull gaban saurayinta, nifaba saurayina bane! Ok. Koma miye kiyi hakuri ta kawar dakai. Nura ya shiga aikin rarrashin nazai yana magana yana kuka alamu sun nuna yayi dan dana sanin abinda ya aikata. Ita dama tuni ta yafemai kodan ganin halin da ya shiga, ( kaji mace idan dai tanason namiji tsakani da Allah wallahi komai ya mata zata hakure) batace dashi komaiba ganin ya tsananta kukanshi ne sai taga rashin dacewar haka yana namiji yazo yana mata kuka tace shikenan ya wuce! Ya dago jajayen idinsa ya kalleta nazai kice kin yafemin mana! karo nafarko da ya taba kiranta da nazai saidai hulwaty....?


Post a Comment

0 Comments