NAMIJI BAYA KA'DAN
Page 4
Manna mata cup din yayi a bakinta, Sanyin cup din ya ratsata cikin jin sanyin ta dan kada mai ido allamar zan shanye fa ka rasa, Shi kuwa ido ya tsurawa fuskarta tare da kafesu kan pink lips din ta idonshi yana ganin yadda take motsasu alamar zata shadin.
Ido ya lumshe tare da sauke ayijar hrt ya daga mata giransa daya cikin alamun kisha, aiko ta kara manne lips dinta kan Cup din shiko ya dan tura mata yana mai kashe mata ido d'aya, gaba daya ya mace da kallonta shiyasa har baisan sanda ya tura mata shi har ya haura sanan lips din ta na saman cup din Da sauri ta janye kanta cikin Sa hannu ta ture nashi hannun ido ta zare mai cikin hade fuska tace "Jifa zaka tura min har cikin hanci dan mugunta ai kai ka nuna bai dameka ba".
Tsaki yaja tare da binta a baya yana tsurawa kugunta ido ganin yadda yake rausaya kamar da gangan take mai abin ma yake gani, a parlour Anty cikin kauda kai yace" kije ki kwanta ki huta dan dare yayi"hara ta cilla mai tare da cewa to Hamma Mahmoud ai dole kai guda ai dole na kwanta ko banjin bacci"Karisa shigawa yayi yana shafa sajen fuskarsa da dan cika izza yace "Ai na kaine dan girma ne dai Allah ya bani tunda yayini NAMIJI".
Tabe fuska tayi tare da cewa "Hmmm ni ina da abin yi Dan wonka nake son yima"Juyawa yayi ya fita tare da cewa "Toh sai kin gama kimin flashing akwai magana"yana tafiya dakin su Abincin ya danci sannan ya watsa ruwa ya dawo parlour ya kwanta kan three stirs shiru yana jiran yaji kiranta amma shiru har zuwa kusan 9 sannan ya kirata yana mai tunanin ko wani mayenne ya tsareta da surutu, aiko yana kira bata daga ba har saida ya kuma na 3 sannan ta daga yana jinta rai a bace yace "Dawa kike magana tun dazu? Kuma me yake gaya miki?Sannan ba nace in kin gama kimin flashing ba"? tsaki ta ja sannan tace " Dan Allah mallam kar ka kara min zafi kan zafi"shiru yayi cikin hade fuska yace "zafin me kuma.
A sanyaye tace"Ni banson zancen wani aurema yanzu wallahi ya Auwal ne ke son jaza min". Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa" Khadija ki dena cewa bakya son Auren shin kin manta shi Aurennan sunnace baba shin bakya fatan ki zama uwa ta gari ga yaranki Ke a zaton ki a shekara run kin nan za'a barki bakiyi Aure bane Sannan ai ke da kankima muddin kina da lafiya yes dole zaki bukaci Aired Ko so kike ai ta zagin iyayenmu ace sun zuba miki ido"?
Shiru tayi cikin sanyi jin zantu kanshi Na ratsata Dan ta tabbar gaskiya yake gaya mata. A haka yai ta mata jirwaye mai kama da wonka Wanda itako bata gane ba Har dai ta fara jin bacci cikin jin baccin da raunin murya tace."Mahmoudu bacci nakeji fa" dariya ya danyi cikin jin dadi Yace " Yau kuma Mahmoudu na zama ne Nana"? "Yes mana ba ka fiye son girma ba" a'a fa bani ke son girma ba Allah ne ya bani girman"Mika tayi cikin sanyi tayi hamma allamun baccin sosai, Shima mik'ar yayi tare da cewa.
"Kiyi Addu,a to"."Toh" tace tare da katse kiran Shiko gaba daya daran ranan ya kasa samun nitsuwa tunani yake da gaske fa ya Auwal gani yake bazan iya Aureba ko kuma mugunta ce shi yana can da matarsa Niko yana hada min zafi. A haka ya tashi ya sake watsa ruwa tare dayin alwalla yazo yai nafila tare da Addu'ar Neman zabin Allah Daga nan kuma yayi ta karatu kur'ani A haka bai samu yayi baccin kirkiba saida akayi sallan Asuba sannan ya dawo ya konta yasamu ya fara baccin.
Shiko yana fita parlour ya wuce yana shiga tare da salam bai ko kalli inda Nazir yakeba yace "Wallahi yunwa nakeji kuma gashi ina son shiga school"Nazir dinne yace "Mahmoud kana gida kenan"? Yes yace ba tare daya kalleshi ba sannan ya juya gunta yana kizo ki ban in yaso ki dawo cikin girma Nazir yace "a'a Mahmoud kaje dai ka jira".
Tuka rinnan ya fada a ranshi tare da murtuke fuska ya juya zai mgn kenan ya Auwal ya shigo Wanda dama yana Parlon Anty ne suna tattaunawa kan Nazir din cikin hade fuska yace " kai Mahmoud me kakeyi a nan kaje Mami Na nemanka. Fuska ya kara murtukewa sannan ya fice yana to! yana fita gidan Goggo Zahra ya wuce yana zuwa ko yayi sa'a malam Abubakar nanan mijin Goggo Zahra kuma abokin Abbanshi suna gaisawa da Gaggo Zahra yace Goggo gun baba fa nazo.
To tace dashi tare da cewa "to tashi muje tun kan bakin su fara ta ruwa"Suna shiga parlon shi yaje gaban shi cinkin girmamawa ya gaidashi Ya amsa cikin son yaron dan yana da nitsuwa da cikar haiba cikin halin girma yace "Mahmoudu ya karatu ya su Abban ka"Kai ya dan sunkuyar tare da cewa "Alhamdulillah"Daga nan kuma sai yayi shiru tare da sunkuyar da kai Lokaci d'aya shiko mlm ya gane da magana a tare dashi Shiyasa cikin kula yace"Mahmoudu meke tafe da kaine ka gaya min kar kaji komai kaji ko" shiko cikin jin karfin guiwa yace."Baba dama......?
Page 5
S
" Abubakar yanzu kai me ka fahimta a zancen Yaron nan, Yanzu ina Mahmoud ina Aure? yanzu anyama Mahmoud yasan me ake cewa Aure? Abubakar Yanzu nefa Mahmoud d'in ya jona University anya yaro nan yasan me ake cewa Aure ai ko yayunshi mata ban taba Aurar dasuba har sai sun gama secondary sun fara zuwa F,C,E kafin suke Aure"Tunda ya fara maganar Mallam Abubakar ke binshi da ido har saida yazo k'arshe sannan yace.
"Amman nayi mmkin jin zantu kan nan daga bakinka shin A shari'a ace akece sai yaro yayi digiri zaiyi Aure? Shin Wanne matsayin da sharad'u musulunci ya gindayar in NAMIJI ko mace sun kai za'a basu damar suyi Auren.
Shi kuwa mlm cikin sanyi yace."Toh matukar dai ba so kake muyi sanadin yaduwar barna da fasadiba to ayi mishi abinda yake bukatar dan wlh illace baba iyaye su kafe kan yayansu bazasu yi Aureba har sai sunkai wani mataki a karatu boko hakan Na jawo yawan barna da fasadi ".
A hankali Baba yace."Yana da kyau Abban ka yaji buka tarka daga bakinka"Kai ya kuma shafawa sannan a hankali yace."Abba dama eh ni dama Abba ni Aure nake sonyi kuma Khadija ce nake so sannan mun gama mgn da ita ni nafi son ayi Auren nan kusa".Abba kam tunda ya fara maganar ya bude baki da mmk yana binshi da ido shi har tsoro Yaron ya bashi (wai Aure nake so)Mallam Abubakar ne yace."Toh Ibrahim kaji ko"?
Yes yace cikin sanyi sannan ya kalleshi cikin kura mai ido yace." Mahmoud Aure kake so ko"? Kai ya gyad'a tare da cewa "yes"Abin yanzu dariya ya bawa Abba shiyasa cikin sanyi yace."Wato kun gama shirya zancenku kai da Khadijan. ita Khadijan ta yarda da Auren"?Kai Mahmoud ya isa dan duniyar domain ta kar karewa yayi ya rinka tsara zance yadda abin zai tafin mai dai dai Gyara zama yayi cikin sanyi yace."Yauwa Abba daman mun gama maganar da ita ita tace duk abinda za'ayi kar a kirata Dan kunya yakeji ta kuma amince dani shiyasa ma tak'i komawa gidan Sulaiman"Ido Abban ya tsura mai cikin son gane gaskayar zance sai kuma yace "Khadijan ko ta amince"?
Yes yace cikin k'arfin hali Baba ne ya kalleshi cikin sanyi yace." toh tashi ka tafi" toh yace tare da mik'ewa ya fice abin shi.
Mallam Abubakar ya juyo gunshi cikin mgn irin ta manya yace."Toh ka ga da idon ka dai tunda sun dai daita Kansu to kar a shiga hakinsu Maganar. Khadija kuwa ni inaga kunya takeji ace ita bazawara zata Auri saurayi kuma k'aninta dan haka kar a tuntubeta da zancen In inna samu zama zama nanda kwana 4 zanje gun Alhaji Sani muyi mgnar zanzo mu tafi da kai dinKuma ko iyayensu mata a bari sai mun gama komai a gaya musu kasan zasu iya yin k'ananan mgn ganu a kai.
A haka suka Ajiye shawara shiko Mahmoud duk abinda ake ciki mallam kan kirashi ya gaya mai. sannan sunje sun samu Baba Sani Shi ba Abin da yace sai sanya Alkhairi. Sannan sun tsaida zance za'a daura Auren randa za,ayi na Amira. Shi kuwa Mahmoud yana sane da komai Amman baiyi gigin gayawa Khadijan da itako bata san komai ba akan zancen.
Ran jumman kuma akayi walima mai kaya tarwa. Da daddere bayan sallan insha allah Khadija ne cikin sauri ta nufi dakin su Mahmoud d'in cikin dan hade fuska ta leka parlon hankoshi tayi yana kwance kan 3 str daga shi sai three quarter a jikinshi, ganin shi hakan sai taji wani irin nauyi ya rufeta da sauri ta juya tana.
Dan Allah ka fito kazo ka kaini Target zan karbo dinku nanmu gun Yazid yace yana jirana".Cikin kasala ya mike tare da rataye rigarsa a kafada ya fito ya tsaya a gabanta da sauri ta kuma juyawa dan wallahi bata son ganin shi hakan Shi kuwa rigar yasa cikin kasala yace.
"Muje ko".Ita kam tuni tayi gaba cikin mota ko cikin sanyi ya dan rink'a mata hira har sukaje suka karbo dinkunan suka juyo suna dawowa. tukin yake cikin sanyi da k'orewa tafiya yake a hankali sun mik'e kan titin da zai maidasu cikin Yola a hankali kamar maiyin rada cikin kasala da wani yanayi ya juyo yana mata wani irin kallo yace. Khady gobe fa...
0 Comments