f Aunty Rumaisa Kashi Nabiyu_2

Aunty Rumaisa Kashi Nabiyu_2


Aunty Rumaisa Kashi Nabiyu_2


         Aunty Rumaisa Kashina Biyu

Da Hamza” ina ga fa ita ce yarinyar da ya kira ni kafin su taso ya ce yayi matar aure”Ammi ta ce” Wow masha Allah yarinya mai hankali kalli taki zauwa gun mu dan kunya amma shi idanunsa ya rufe ya bita” dariya suka sayi atare suna binsu da kallo su ga iya gudun Shaheed din.

Rumaisa da sassafe ta isa gunsu tayi jifa da jakar ta fada jikin innani ta rungumeta gam tana dariya innani ta ce” ke karki karasa ni mana, sannu da zuwa” kiss Rumaisa tama innani ta saketa ta rungume Mamie ta ce” i miss you Mamie” dariya Mamie tayi ta ce me too dota ya gajiya” Na’ima ta ce”Anty nifa” sakin mamie Rumaisa tayi ta rungume N’aima.






Al’ameen ya ce” Rumaisa ni me na kashe miki wai” sakin Na’ima Rumaisa tayi ta nufo gun Al’ameen ta shagwabe fuska tana bubbuga kafa ta fada saman kirjinsa ta rungumesa gam, ta shagwabe masa ta ce” my brother kayi hakuri kaji wallhahi nayi missing dinka sosai fiye ma da tunanin ka” murmushi Al’ameen yayi ya kara manne ta jikinsa yana buga bayanta.

Shaheed ko wani gululun bakin cikine da kishi ya tokare shi duk da ya ga yayanta ne, haka ya iso ya musu sallama, Rumaisa da sauri ta saki Al’ameen ta kalli Shaheed shiko ko kallonta bai ba, ya gaishe dasu innani suka amsa cikin fara'a Na’ima ko idanu ta kura masa. Al’ameen ya bashi hannu Shaheed ya amsa sukayi musabaha, ya musu sallama ya tafi gun yan gidan su. Rumaisa ta bisa da kallon mamaki ko me ta masa yayi banza da ita duk Sai bata ji dadi ba.

Al’ameen ya ce”ai sai muje gida ko kanwar ki ce mun kusa shan biki dan naga wani abu”bBaki Rumaisa ta zumburo ta sunkuya ta dauki jakar ta karama Al’ameen ya Ja babbar Rumaisa ta kama hannu Innani suka nufi gun mota. Shaheed ya na isa gun iyayan sa ya rungume Daddy Ammi ta ce” wai mun zata can gidan nasu zaka bita” dariya yayi ya ce”Ammi muje gida akwai hira Allah kuwa” dariya suka masa Hamza ya Ja akwatin sa suka nufi gurin mota.

Lokacin da su Rumaisa suka isa gida takwas da rabi, na dare, Al’ameen ya na parking Rumaisa ta bude mota ta fito aguje tayi cikin gida tana kiran Abbie. Parlow ta fado aguje, Abbie na zaune cikin keken sa ya ware mata hannunsa, da gudu ta karasa ta fada jikinsa tana murna ta rungumesa tsam ta ce” My Abbie i miss you ya karfin jiki.” Ta fada tana d’agowa ta na kallon sa. Dariya Abbie yayi ya ce”My love Alhamdulilah ya gajiya ya yan uwanki da fatan kowa ya na lafiya.






Rumaisa ta ware hancin jin kamshin Abdallah na ziyar tar hancin ta, ta ce da Abbie”Alhamdulillah Abbie duk suna gaishe ka” ta fada tana sakin sa ta mike tsaye tana raraba idanu, karaf idanunsu ya sarke da juna ita da Abdallah ya kame saman wata lumtsumemiyar kujera ya dora kafa daya kan daya, kansa ya kauda fuskasa kicin-kicin ya shiga latsa waya, Rumaisa ta saki murmushi ta kalli Abbie ta ce”Abbie yaron nan ya raiwa kansa hankali ya na kallo na shine bazai mun sannu da zuwa ba” ta fada tana nufar gurin Abdallah tana murmushi ta ce” Baby kanina waye ya taba min kai agarin Abuja” ai Abdallah bai bari ta iso ba ya mike tsam ya kara waya a kunnasa ya na takunsa na isassun maza sabon jini ya nufi kofar fita. Baki da hanci Rumaisa ta saki tana kallon sa har ya fice sai taji ta tozar ta dan ta tsani a disga ta har kwalla ta taru idanunta ta iso gaban Abbie ta sunkuya ta rike kafar keken, Abbie muryata na rawa ta ce”Abbiena wa ya bata ma Baby Baffa rai, kalli ko kulani bai ba ace wata daya bamu hadu ba amma ya ganin ya mai dani banza” dai-dai lokacin su Al’ameen suka shigo da sallama.

Abbie ya amsa musu ya kalli Rumaisa ya ce “My love Baffa ke kika ta boshi ya kira yafi sau dari ba ki dauka ba ya ce ya fita daga harakar ki” abin dariya ya ba Rumaisa ta saki ranta ta ce” au a kan wannan ne wlh tafi nono fari can ya karata nima na huta”ta fada tana dariya ta nufi bedroom d’inta. Dariya Na’ima tayi taja akwatin Rumaisa ta bita ta na cewa” Wa zai shiga tsananin harshe da hakuri” dariya su Mamie suka yi Mamie ta kira Larai da karima masu aiki suka shimfida babbar leda nan saman tafkeken carpet din parlon suka kawo kulolin abunci a ka jera dan mafi yawa haka suke dinner din dare.







Rumaisa bayan ta shiga hadaddan bedroom dinta ta cire kayan jikinta ta daura towel ta shige bathroom tayi wanka bathroom din kadai abin kallon ya hadu mutika,Ta jima sosai, kafin ta fito dan saida ta gasa jikinta sosai da ruwan gumi, tayi wanka ta fito. Na’ima tana zaune Rumaisa ta ta fito ta ce”to me kuma kike jira baki fita ba” Na'ima ta ce”Anty kiran ki ake tayi a waya shine na daga muryar kamar ta wanda muka ganku tare a Airport” Rumaisa ta na goge jikinta da towel ta ce” Ok naji tashi ki fice na shirya jikina”Na’ima ta mike tsam ta fice.

Agagauce Rumaisa ta shirya cikin riga da siket yan kanti milk colour wanda suka dan kamata hips dinta duk ya fito rigar ta dan matse ta kirjinta da yake cike dam kamar zasu fasa rigar su fito kayan sunyi mata kyau sosai ta kame jelar kitson ta daure su da ribbon suka koma tsakiyar gadon bayanta batai kwaliya ba turaran ta mai sanyin dadi ta fesa ta dauki wayarta wacce take ta ruri, irin ta Abdallah har kalar ma iri daya ne, bata yi picking ba ganin number ba suna ta nufo parlo.

Yan gidan sun jeru a saman carpet suna zazaune suna jiran Rumaisa sai gata,kusan Abbi ta zauna tana murmushi ta riko hannunsa ta ce”Abbie ni zan baka abaki”dariya yay ya ce”My love ki bari kici nima zan ci da kaina”innani ta ce”Rumaisa tashi ki kirawo k’aninki ya fa ki zauwa ya ce baya cin abuncin kinga har marin Na’ima yayi dan ta je kiransa” Rumaisa ta kalli Na’ima tana matsar kwalla kumcinta har yayi Ja abin ka da farin mutum.Rumaisa ranta ab’ace ta ce”ri bar ya ci mana amma meye na dukanta a kan me zai duki mareniyar Allah ko ya manta Amana take a wajansa”ai Na’ima najin Rumaisa ta daure mata gindi ta b’are baki ta fashe da kuka tana cewa wayyo wuyana Yayana ya murde mun wuya bayan marin da ya zuba mun”Rumaisa ranta a mugun b’ace ta mike ta na cewa”wallahi ran Baffa sai ya baci yau ta “fada tana nufar kofar parlo.

Mamie da Abbie da Al’meen suna kiranta ta rabu dashi kar fa suyi rikici dan a sama ya ke ta ce”wallahi Abbie sai na wanwanka masa mari yaji idan da dadi ai shima ai ya na da gaba dashi”ta fada tana ficewa daga parlon.Kai tsaye Rumaisa part d’insu Abdallah ta nufa ko ina na jikinta motsi ya ke, tamkar tarwada sai sauri ta ke ta je ta rama ma Na’imah dukan ta.

Post a Comment

0 Comments