International Blaise Diagne. Da yake a Kasar Senegal capital Babban birninsu (Dakar) da mislin karfe Biyar na yamma, Ko ina ka waiga dandazon jama’a ne, matafiya cikin Airport din kowa na jiran lokacin tashin jirginsu yayi. A tsaitsaye suke suna jimamin rabuwa da ita.
Matashiyar budurwa ce kyakyawa lumba one tana da wani irin sihirtaccen kyau duk da ita ba fara ba ce amma tana da mutikar, kyaudoguwa ce sam ba ta layin fararen mata haka zalika bata layin bakake, wato chocolate colour kenan sanye take da wani yadi na mata irin na Senegal green colour dinki doguwar riga wanda ya kamata ya mata cif cif surar jikinta mai kyau ta baiyana tana sanye da wani takalmi shima green ne mai tsayi gaske yana da igiyoyi, sai jakarta da take makale a kafadarta ita ma green colour, ta sha kitso mai masifar kyau wani mai wata irin kwana-kwana ta zubo jelar kitson gaba, sauran gaba sauran baya, daga kitson za ka san tana da gashi, ta dan yane kanta da karamin mayafi shi ma green colour, a gaskiya a wannan lokacin duk namiji mai lfy ya ga Rumaisa zai ji yana son ya mallaketa amatsayin matarsa ta sunnah.
Tsaye suke kasancewar an fara sanarwar matafiya Nigeria su shirya, yan uwanta sun baibaye ta, suna kukan rabuwar su da ita dan har yau sun kasa sabawa in dai Rumaisa zata zo Séenegal to idan za ta koma Nigeria cikin kuka su ke rabuwa da dangin mamarta suna koke-koke. Wata dattijuwa ce mai kimanin 60 year, rungume da Rumaisa tana kukan rashin ta da za ta yi na Rumaisa din.
Rumaisa ta manne ajikin tsohuwar tana murmushi tana shafa bayan tsohuwar dan Rumaisa ba ta fiye kuka ba, ga shi idan ta ce za ta yi yanzu tsohuwar rikicewa za ta yi. A hankali Rumaisa ta yi magana, da yaran Senegal, cikin zazzakar muryata, ta ce” grand-mere ki yi hakuri zan dawo shekara mai zuwa in sha Allahu, ki bar kukan, ta kalli Bibata da Umari ta ce” Ku lallaba mun grand mere ai zan dawo, in ko na sami miji sai ku zo biki ko grand mere" Ta karasa fadar maganar tana ma grand mere chakulkuli.
Sai ga ta tana dariya tana dukan Rumaisa, daket ta kwace ta fara gudu grand mere ta bita suna zagaya dan filin da suke tsaye, su Bibata suna musu dariya, jama’a sai kallonsu suke cike da sha’awa, barin Rumaisa yadda jikinta yake motsawa.
Saboda akwai ta diri mai kyau da daukan hankali, jigidarta da ta ke daure a k’ungata mai dauke da sinadarai sai cakas-cakas suke, a kugunta, Rumaisa doguwa ce chocolate colour dirara mai kirar Coca-Cola akwaita mazauna, masu mutikar daukan hankalin maza, samanta a tsuke kasanta a bude yake, ba ta da kiba kuma ba ta da rama sosai akwaita da hips na daukar hankali, ga ta da manyan-manyan boobs a tsaye suke cur tandam-tandam, ma su tafiyar da imanin duk wani lafiyayan namiji.
Rumaisa tana da doguwar fuska mai dan fada, tana da dogon hanci da manyan idanu farare tas lumsassun idan tana kallonka za ka zaci kallon raini take ma ko kuma tana jin bacci gashin idanunta gazar-gazar ne haka gashin girarta mai kyau ne, sai dai tana da fadin lips sosai irin na yan Senegal, amma cikin ikon Allah sai ya yi mata kyau mutika lips dinta pink ne, tana da dimple a gefen kumcinta na dama wanda ko magana take lobawa yake bare ta yi dariya, Rumaisa tana da fara’a da son mutane ba ta da raina mutane sai dai ta fiye sanyin hali kuma ba ta cika surutu ba mutum daya yake bata ciwon kai shi ne ya koya mata surutu da masifa.
Shekarunta na haihuwa 26 year amma wallahi ba za ka taba cewa Rumaisa tayi 20 year, ba saboda Allah yayi mata kyawun diri da kyan fuska ko ta fadi shekarunta na haihuwa mutane ba sa yarda sai su ce karya take ba za ta yi ashirin ba ma dole take kyalesu saboda ko a makaranta haka ta yi ta fama da kawayanta da malamai kafin su kammala karatunsu na karshe wato law school, wallahi har sai da ta fara musu yar masifar da Abdallah ya fara koya mata tukun ta samu kansu, suka rabu da ita suna cewa an kara mata shekaru ne ai.
Dole Rumaisa sai dai ta yi dariya ta ce ta ji har suka gama karatun su. Sosai Rumaisa suke zagaya filin suna dariya ita da grand mere, umari sai ya fara hawaye ya tuno da mahaifiyar Rumaisa da ta mutu. Mubarak ne ya isa gurin Rumaisa ya kamota ransa a bace ya ce “wai me yasa kike haka ko baki ga yarda jarababbun maza ba suka zuba miki idanu ko baki san abin na bata mun rai ba wallahi dole zan zo Nigeria cikin satinan tunda karatu ya kare Abbie ya bani auranki na dauko abuna mu taho haba ina dalilin jaraba sai kace Rumaisa ce kadai mace.” Ya karasa yana huci.
Rumaisa ta kwace jikinta, ta kura masa idanu dan sam ba ta san da zuwan sa ba, cikin sanyin murya ta ce”wai Moubarak me yasa kake da kishi yaushe muka yi da kai zan aure ka wallahi har yanzu ban sami kalar namijin da nake so ba in da ina son ire-iren ka da tuntuni ina cikin karatu na yi aure please ka barni mana mu tsaya zumunci ba wai soyayya tsakanin mu, da wani idanu zan kalli Aliya matarka haba dan Allah.”ta fada tana ja baya.
Mubarak kallonta yake cike da mamaki ya ce” wallahi a kanki ko sakinta ya kama zan yi wallahi idan kika ga ban aure ki ba sai dai wani ikon Allah” grand mere ta fara masa fada ta rungume Rumaisa tace”ki rabu da sakare.”dariya Rumaisa ta yi.
Za ta yi magana aka fara neman matafiya sai lokacin idanun Rumaisa suka ciko da ruwa ta rungume grand mère suna kuka. Sai da Bibata ta banbare, Rumaisa daga jikin grand mere. Rumaisa ta rungume yan uwan mamarta maza da mata daya bayan daya, Bibata ta ja hannunta ta rakata bakin inda za ta shiga har gun jirgi Mubarak na biye da su hannu ta daga masa dan a rabu lafiya.
Haka Rumaisa ta shiga cikin jirgi tana kewar yan uwanta. Tunda Rumaisa ta shiga jirgi ta jingina kanta da kujera ta lumshe idanunta tana safke numfashi tana jin wayarta na ringin ta ki bude idanunta ma bare taga mai kiran, dan ta san bai wace, Abdallah.
A can kuwa Nigeria garin Abuja unguwar Games village a dai-dai wannan lokacin wani matashin saurayi ne ya fito cike da takun isa da kasaita yake takunsa, yana kalkada makullan mota,yana ciza lips dinsa ya nufi rumfar ajiye motoci da take cikin wannan tamfatsetsan gidan tsarare wanda aka kerasa da kayan zami tamkar a kasar larabawa babu abin da babu a gidan tsayawa fadar tsarin gidan ɓata lokaci ne, amma ya hadu ta ko ina dan gidan kallo daya zaka masa ka san ya hadu ba karya me shi ya ci ya tada kai da nera.
Abdallah yana isa rumfar motocin ya yi tsaye jikin wata jibgegiyar Jeep fara kal fuskarsa ba walwala yana latsa zabgegiyar wayarsa iPhone 11 yana jan tsaki da ciza baki. yana sanye da wasu kananun kaya riga da wando masu masifar kyau Ash colour sun yi masifar masa kyau sai zuba uban kamshi yake kayan sun fito da girman kirjinsa saboda yadda kayan suka kamashi, da gan-gan yake zazago wando yayi kasa amma hakan baya hana kaya su masa kyau, gashin kansa mai tarin suma baka sudik sai walkiya yake iska na kada gashin tamkar na indiyawa harda tilar kunne daya gare shi wacce yasa mata barimar zallar gold sai sheki yake gashin kansa sai walkiya yake saboda bai fiye aski ba shiyasa zaka ga gashin tamkar na wata macan, Abdallah dan kimanin 23 year dogo mai murdaddan jiki mai zubin karfafa yana da faffadan kirji samansa a bude yake yayin da kasansa yake a tsuke, fari ne tas kyakyawa ajin karshe a kyau yana da manyan idanu dara-dara da gashin idanu da na gyara masu kyau yana da dogon hanci bakinsa dan karami, jajur da shi tamkar na jarirai wanda hakan ya kara masa kyau ba kadan yana da simple har biyu, ko magana yake lobawa suke uwa uba idan ya yi dariya, abin da ya ke tafiya da Antynsa Rumaisa kenan tayi ta saka sa dariya tana saka yatsarta ramin tana tabawa.
Abdallah ga shi da shegen kwarjini duk girmanka idan kuna magana da Abdallah ya tsareka da wannan shanyayyun idanun nasa masu wani sinadari a cikin su na baiwa da ba kowa Allah ya ke ba irin ta ba dole ka ji shakkarsa shiyasa zaka ga har wanda suka girme masa suna shakun sa saboda shi yaro ne jarumin gaske ta ko wane fanni namiji gaske ne shiyasa ko a makaranta abokansa da malamai suke kiransa da Baffa Abdallah babban mutum.
Shi ko uban son girma sai ya fara bubbude hancin ala dole shi babba ne, Abdallah duk abin nan nasa amma sai ya maida kansa sakare mara wayo a gurin Antynsa Rumaisa ita ko take biye masa tana renonsa tamkar jariri duk da watarana idan ya shakata ta ga iskancinsa yayi yawa fada suke sosai ta yi masa fushi, dan labari dai sai a nan gaba.
Kai komo Abdallah ya fara saboda kiran da yake ba’a dauka, ransa a bace ya bude motar ya shiga, cikin daddadan muryasa a yangace can k’asan makoshi ya furta” Wallahi My Aunty Rumaisa sai na bata miki rai fiye da yadda kika bata mun yau nine zaki dauka dan iska dan ina miki biyayya wallahi sai na saki kuka kamar yadda kika sani sai na daga miki hankali gobe na san maganin ki” ya karasa maganar yana ciza jajayan lips dinsa yama motar key ya fizgeta da karfin gaske ya nufi tamkameman get din gidan yana zuba uban horn, me gadi na sanye da uniforme a guje ya nufi get sanin halin Abdallah yanzu zai bashi hutu,yana wangame masa get ya fice a guje kamar zai tashi sama.
Bangaran Rumaisa jin an daina kiran ta ja tsaki ta ciro wayar a jaka wani kiran ya shigo ganin Abbie ne ta zaro idanu ta dafe goshi cikin siririyar muryata mai dadin, gaske ta furta ” oh My God my Abbie dama kaine kake kirana tun dazu” ta fada tana tsinke kiran, ta ce “Abbie bari na kira ka na zata wannan fitinanan Baby kanina ne shiyasa naki duba wayar” ta fada tana dailing number Abbie.
Bugu daya ya daga da sallama murya dattijo mai cike da kamala. Rumaisa ta ce”my Abbie barka da yamma ina yini ya karfin jiki ya mamie, ka yi hakuri na zata Baffa Abdallah ne shiyasa naki picking” daga can bangaran Abbie ya saki murmushi ya ya ce” My love Allah ya shirya ku ke da Baffa abin ya Kai ya kira kiki dauka kanin ki ne fa abokin shawara ki, na ko ga yanzu ya fita cikin fushi yana jan tsaki” murmushi Rumaisa ta yi, ta basar da zancan ta ce” Abbie gamu cikin jirgi zamu taso a mana Addu’a i love u Abbie Allah ya kara ma lafiya sai na iso please Abbie yaya Al’ameen zai je daukata bana son Abdallah ya je.
Zaman da na ji anyi dab da ni wani daddadan kamshine ya daki hancina shi ya saka na katse maganata nan take ba tare da na sani ba na tsinke kiran dan na tsani takura ga shi ba halin na ce ya tashi tunda jirgin ba na gidanmu ba ne.
Cikin cool voice na ji ya mun sallama muryashi mai dadi, ban san lokacin da na dago ba, karaf idanunmu suka sarke da na juna yana sakar mun murmushi take na ji gabana ya fadi nayi saurin kawar da kaina na sadda k’asa, ina mamakin kyawunsa duk da bai kai Baby kanina kyau ba, baki ne kyakyawa isasashan namiji na nunawa sa’a zai kai kimanin 32 ma’abucin fara’a.
Amsa sallamar nayi daga shi ban sake ko kwakwaran motsin, wayata na kashe baki daya na maida jaka na darma belt na takure a guri gudu na lumshe idanuna. Har jirgin mu ya tashi ban dago ba, murya sa na kuma tsintowa yana cewa” La beauté sannu kin amma ke haifafiyar Nigeria ce ko.Ya fada yana leken fuska ta.
Ban masa magana ba, saboda kusancin mu ya yi yawa ga kamshin sa ya cika ni, ban taba tunanin ana samun namiji mai kwarjini da dadin murya wanda ya hadu ga sansan yan kamshin bayan Baby Baffa kanina ba. Tunanin ya katsemun ta hanyar ce mun “please mai kyau ki mun magana wallahi tunda na ganki a waje kuna wasan tsere da kakar ki Allah ya jarabe ni da sonki kai tsaye wallahi gaskiya nake fada miki.
Ya kara maganar yana dafe kansa idanunsa sunyi jajur kwalla ta taru. Kallonsa na yi na ga kwalla yake,cikin sanyi murya cike da tausayin sa nace”please kar ka yi kuka ina da rauni ba na son ganin na sanya wani damuwa, ko Baby kanina ba na bari yayi duk yadda zai bata mun rai shi da yake yaro bare kai babba” ta karasa maganar tana sadda kanta dan bata jure kallonsa gabanta faduwa yake sai ta rika jin wani irin yanayi.
Murmushi farin ciki ya saki yace “Alhamdulilah na ji logon ki zan dinga miki kuka da zaran kin ki saurara ta, so da farko ni sunana Shaheed Ghali imam Sara muna Abuja zaune tare da iyayena, da yan uwana sauran labarina sai mun kebe, please ki bani gurbi a zuciyar ki wallahi yau daya na yarda da ake cewa daga kallo daya ana kamuwa da soyayya.” Ya fada yana sakin murmushi yana leken fuskar Rumaisa wacce take wasa da zoben gold guda biyu, hannunta.
Shiru ya mata yana mai jin dadin samun irin macen da ya jima yana nema kamila mai kamun kai ba irinsu Labibah ba kamar tai masa fyade. Haka jirgin su yake lula gudu asararin samaniya, cikin hikima da dubara Shaheed ya saka Rumaisa ta dan saki jikinta da shi har ta fada masa sunanta da unguwar su a Abuja ya mata wayo har da numberta saida ya amsa.
A haka har bacci ya dauke ta ganin ta takure ya gyara zamansa ya dora kanta saman kafadarsa ya tallabe ta da hannunsa yadda za ta ji dadin bacci, duk da ya k’age amma bai damu ba, haka jirginsu ke tsula gudu zuwa Abuja, sai muce Allah ya sauke ku lafiya."Nigeria" Baffa yana fita a guje ya harba motar saman titi gudu yake sosai, yana ciza lips dinsa na k’asa har ya yi wani irin ja ko me ya tuna da karfi ya take burki ya juya kan motar zuwa gida yana sharara gudu.
Tun daga nesa ya fara zuba honr, megadi ya bude masa get, tun kafin ya iso. Yana isowa ya shige gidan a guje, ya nufi parking space. Yana shiga ya yi parking ya kashe motar ya fito ko motar bai tsaya kashewa ba ya fara takun sa mai cike izza da karfi yake takawa ya nufi tsakiyar rumfar, kallo daya za ka masa ka san ransa a ɓace yake.
Yana zuwa ya bude wata rigar rufe mota wani hadaddan mashin babba mai kyan gaske ya baiyyana green colour ne ajiye rigar yayi ya hau abinsa saboda baya da kura wani bakin glass ne sarke gaban mashin din Abdallah ya cire farin glass din fuskarsa ya saka bakin ya wa mashin din key ya tayar da shi, wani irin kara yake zu me dadi ya fito daga rumfar Al’ameen da ya gama parking ya fito daga cikin motarsa ya kalli Abdallah yace” Baffa kai dawo nan” banza Abdallah ya masa ya ma mashin din wuta ya nufi get a guje. Al’ameen ya buga masa tsawa ko a jikinsa tun daga nesa yake honr aka bude masa get ya fice daga gidan a guje. Al’ameen da ransa ya gama baci ya nufi cikin gida gun Abbie yana masifa sai sauri yake kamar zai kifa dan iskancin Baffa ya fara isar sa.
0 Comments