PAGE 21 TO 25
A ƙasan zuciyar shi yake wannan maganan. Miƙewa Ummie tayi tana ƙoƙarin shigewa cikin gida,yai saurin ruƙo saleɓen zanin ta,tsayawa tayi cak batare da ta kalle shi ba. "Ummie pls forgive me. "Aliyu ka kiyayeni, kabani takaddan saki kawai,kaje ka zauna da wacce ka zaɓi farin cikin ta fiye da nawa".
Cikin fushi take maganan. Gaban shi tsananta bugu yake,yaune rana na uku da ya taɓa ganin mugun ɓacin rai fuskan mahaifiyar shi,gaskiya na tafka babban kuskure ya faɗa a ƙasan zuciyar shi. Azahiri ƙara marairaice murya yayi yace,"Ummie na kiyi haƙuri. To Aliyu ɓace min daga gani inka ƙara zuwa min da maganan nan ranka sai yayi mugun ɓaci". "Tou Ummie insha Allahu. Miƙewa yayi jiki a saɓule yai mata sallama,ya tafi yana tunanin mafita, lokaci ɗaya kuma yayi murmushi.
Dady wai ina zamuje ne. Cutie take magana ta nade hannuwan ta cikin riga da wando yellow purple ɗin ɗan ƙaramin hijjab yasa mata da takalmi purple,akwatin ta yake sa mata kaya.
Weekend zamuje,ran sunday zamu dawo sabida school. Ya faɗa batare da ya kalle ta ba yaci gaba da sa mata kayan a ɗan akwatinta. Tsalle tayi da murna,ta hau bayan shi tana dariya. Dariya yayi shima daidai lokacin yana rufe akwatin. Dauka yayi suka fito riƙe da hannun juna. Daidai lokacin tafito taci uban ado kamar bazata mutu ba,kallon kallo sukai ma juna,yawani murtuke fusa, yayin da ita harare ta galla masa. Good morning momy".
Faɗan Cutie da ta tsare Abeeda da ido. Batare da ta kalle inda take ba taja dogon tsaki ta wuce ta fita ba tare da ta ko gaisheshi ba. Murmushin takai ci yayi tare da shafa kan Cutie. Cutie ko jikin ta duk yayi sanyi. Koda suka fito harta banka ma motor ta wuta ta wuce. Aliyu ko matuƙar mamakin halin Abeedah yake.
ALIYU INA ZUWA HAKA.
SHIN WANI HALI JIDDA TAKE,TA MUTU KO TANA RAYE.
WANI HALI ZARAH TAKE.
DAMA ASHE ALIYU BA AURAN ABEEDA KAWAI YAKE DASHI BA.
PAGE 26 TO 30
Zarah ko nacan police station tana amsan azaba kala kala, duk marasa imanin police ɗinnan sun gama ƙara canja mata kama gaba ɗaya. Saida likitochi suka kwashe awa uku akan ta kafin sukayi nasaran dawo da numfashin ta, don dogon suma tayi lokacin da Zarah ta buga mata sandan. Don ko su kansu likitocin har suncire rai da zata shi,duk da akwai alaman rai atattare da ita. Hansai ko hankalin su duk a tashe yake tunda sukaji shiru ba wanda yafito balle suji tana raye ko ta mutu. Tafiyan awa biyu da rabi yayi daga shi sai yarshi komi ta gani a hanya sai tace Dady saya min, ko kuma ta tambaya miye wannan,wani yabata amsa wani yai murmushi yaja mata hanci,hartai bacci ta tashi tace,"Dady bamu iso ba. Murmushi yayi ya shafo kanta da ɗanyan hannun shi yace,"mun zo mana yanzun zamu ƙarasa". Gyaɗa kai tayi ta kwanta taci gaba da wasa da yatsun ta kamar wata babban mace.
Cute kenan akwai manyan ce kamar wata ruƙon tsofaffi. Parking yayi a dai dai killan gidan su mahaifin shi ba kowa a a wajan sai bisashe da suke ta kiwo, yara ne daga can nesa suke wasan su, kulle motor dayayi ta hanyar danna key yasa motor tai kuka, take yaran hankalin su ya dawo kan su. Zuba musu ido sukayi, shiko ɗaukan Cute yayi suka fara tafiya,yaran ko zuba musu ido sukai kamar sunga tv. Assalamualaiku",sallama ya rinƙa kwaɗawa,amma ba kowa shiru,har ya juya zai fita,ya lura da Sa'ina dake zaune ƙarƙashin dalbejiya tana damɓara kwalliya kamar wata jaka yasa ran shi ya ɓaci.
Ranshi ɓace yake maganan. Shiru tayi tai muƙus don tasan shi da rashin imani yanzun sai ya nema ya karyata, gashi tana shirin zuwa wajan saurayin ta. Dogon tsaki yaja ya nufi ɗakin Abba, kwance yake jikin sa ne kaɗai ke rawa gashi yai fitsari da kashi ɗakin duk ya ɗume da wari, ga yunwa naci cikin sa. Har Aliyu ya tusa kai yai saurin dawowa baya yana toshe hanci. Ke da mutum a ɗakinnan? ya tambayeta cikin tsawa. Jiki na rawa tace "yes baida lafiya ne Jiddah ne ke kula dashi. Ina Jiddah take da bata gyara shiba?,maike damun shi. Lokaci ɗaya ya jero mata wa ƴannan tambayoyin. Jidda an tafi da ita asbiti tun jiya baa dawo ba. "Miya faru da ita.
Dama-dama tawani fara kame-kame. Zaki min magana ko sai na taka ki mai suffan burai. Dama Zarah ne, nan ta kwashe abinda ya faru ta gaya masa,ransa yai mugun ɓaci sai huci yake kamar ya daki babu. Ke to uban miye amfanin ki da bazaki dubashi ba banza ballagaza wanda tasha a mama, dalla tashi kije ki gyara shi tas.Yanda yake ihu yake tada jijiyoyin wiya ba ƙaramin razana tayi ba,jiki na rawa ta miƙe ta nufi ɗakin Abba yaune rana ta farko kenan da tunda ya fara ciwo shekara huɗu kenan bata ko leƙa shiba ta ga yayake. Azuciyar ta kuwa tsine ma Aliyu kawai take, toshe hanci tayi tana tsoron ta fita ya kileta,gashi saida tayi wanka taci kwalliya zaisa ta aikin kashi tou ita ta yaya ma zata fara. Ƙwafa yayi ya samu turmi ya zauna ya ɗaura Cutie kan cinyarshi da tuntuni tawani ƙanƙame shi, a zuciyar shi ko ganin rashin kyautawan shi yayi da har ƙanin mahaifin sa ɗaya tilo da ya rage masa a duniya yana ciwo bai san ma yanayi ba, gashi yana da halin temakon sa, rabon sa dashi tun ɗaurin auran sa da Abeeda ko ban gajiya bai samu zuwa yayi masa ba, sabida kunyar da abinda yai masa.
Cuty tsura masa ido tayi na seconds kafin ta kai duban ta kan Aliyu tace,"Dady waye shi. Cutie Baba nane, sunan shi Abba, ke kuma Kakan ki ne. Yana juya motor yana mata magana. Cikin mintina ƙalilan ya harba motor kan titi sai cikin gari.
NAGODE SOSAI DA COMMENTS ƊINKU ALLAH YABAR ZUMUNCI
PAGE26 TO 35
Cikin mintina ƙalilan ya harba motor kan titi sai cikin gari, asbitin daji yakai shi wajan wani abokin shi Dr Munir inda aka anshe shi aka shiga dashi don bashi temakon gaggawa. Ɓanagaran Jidda ko likitoci bayan sunyi nasaran cetou rayuwarta suka fito inda suka kira Hansai da Tani sukayi masu bayanin ta farfaɗo,amma basu san lafiyan kanta tana cikin hayyacin ta ko ta samu taɓin ƙwaƙwalwa sai ta farka daga bacci tukunan zasu iya gane haka, da ta farka su tabbatar da sunzo sun gayama likita,don a ƙara dubata, su ci gaba da addu'a, godiya sukayi suka tashi suka nufi ɗakin da aka kwantar da ita. Zarah ata ko ina jin jiki takeyi, tun balle da akace yar kishiyan ta ta kashe,hatta wa yanda aka haɗa su cell ɗaya gana mata azaba sukeyi.
Zo cinye ni, tunda ninayi miki magana baki ban amsa ba kin shigo kamar wata aljana wai Ummy yunwa. "Dadyne fa ya kawo ni,yace ince miki banci abinci ba. "Ina Aliyun, "Ya wuce. "Tashi kije kitchen kice Sadiya tabaki abinci. Tashi tayi da gudu ta nufi hanyar kitchen. Aliyu ko bazama yayi police station neman Zarah tanan ne zai iya gane inda yarinyar take. Saida yaje police station uku ana huɗu ne ya samu nasaran ganinta. Sanda aka fito da ita zuwa bayan kanta inda zasuyi magana. Zarah ƙasa tayi da idonta tana hawaye dama can shakkan Aliyu take don baida mutunci ko kaɗan tsaye tsaye yake mata magana babu ko kara.
Gwaggo nazo ja miki kunne ne wallahi,matuƙar yarinyan nan ta mutu ko wani abu ya sameta wallahi tallahi billahillazi ko duka arzikina zai ƙare, sai na ƙarar don inga an hukunta ki,baruwana da ke yar kakana ne, sannan mijinki kawunane mafi soyuwa a gareni zan rufe ido a wulaƙanta min ke,police kuci gaba da hukuntata. Cikin kakkausar murya yake mata maganan yanayi yana murza yatsun sa suna ƙara,iya abinda ya faɗan kenan ya ciro rafar ɗari biyar ya aje musu akan tebur ya juya yabar wajan. Duk wani dake tsaye a wajan saida yayi mamakin maganganun shi, sannan ya aje uban kuɗi ya tafi. Zarah ko duk ta rikice tasan halin Aliyu saide bai furta ba sai ya aikata,tayaya asirin da tayi mai na bazai ƙara waiwayan ƙauye ba ya karye har yazo, dole takoma wajan mallam,don maganin ɗan iskan yaron nan.
Mai akace damuwar ta, Yatambaya akaro na biyu. Nan Hansai tamai bayani,bai wani gamsu ba, yafita ya nemi likita ya ƙara yi masa bayani, kafin ya fito yaje chicken republic yayo take away yakai musu, har lokacin bata farka ba. Inda Abba yake ya koma, lokacin har an gama dubashi an kwantar dashi shima sai bacci yakeyi, wajan likita yaje yamai bayanin hawan jinine yai sanadiyar kawo mai mutuwar jiki, rashin kulawa da zuwa asbiti yasa jikin sa ya mutu gaba ɗaya. Dr Munir yabashi tabbacin zai iya tashi, inde aka dage masa da gashi. Sallama sukayi ma juna bayan an samu mai kula da Abba namiji, zai biyashi.
0 Comments