PAGE 57 TO 60
Jikin ta a sanyaye a hankali ta buɗe baki tace,"Yaya kayi haƙuri wallahi ban san ranta zai ɓaci ba harta yanke ɗanyen hukunci haka akan ka, don girman Allah kayi haƙuri ka yafe min".Ta ƙara she maganan da muryan kuka,ji yayi duk ba dadi lokaci ɗaya a zuciyar shi,tayi matuƙar bashi tausayi yanda take maganan. Dukawa yayi yana fuskan tan fuskan ta, sa hannun shi yayi a hankali kan lallausan fuskan ta ya share mata hawayen da suka zubo yana murmushi kamar bashi aka gama kashe da mari ba yace,"ƙanwata karki damu Ummie zata sakko zanje in bata haƙuri.
Yauwa abinda yakamata kayi kenan gadanga,fushin mahaifiya, bala'i ne da masifa akan ɗanta,hatta Allah fushi yake dakai in kasa mahaifiyar ka cikin kunci tashi kaje kabata haƙuri,don gujewa fushin ubangiji. Fadan Iya da take tsaye ta bayan su tun ɗazun da sai yanzun tayi magana. Murmushi yayi yace,"zan bata haƙuri Iya,Ummy ta mai fahimta ce da haƙuri, nasan zata haƙura. "Yauwa tashi kaje. Fadar Iya akaro na biyu. Mikewa yayi yana fasha fuska, tare da riko haɓan ta yamikar da ita.
Cute da gudu ta taho wajan sa ta kan kame shi, dukawa yayi ya dagota ya shillata sama, sukayi hanyar bedroom din Ummy, yana rada mata magana akunne tana gyada kai tana murmushi. Abeeda wai ke bazaki bikin kanwar Najaatu bane a katsina, ki tambaye mijinki, in zai barki. Fadar Aisha da suke zaune wajan shaƙatawa,suna ciye ciye, duk sunci ado kamar bazasu mutu ba. Kam bala'i da yasani da kar ya sani uwar su ɗaya uban su ɗaya, kayan ankon ma na wajan ɗinki, tafiyata zanyi,aini aduk fitata ban jiran umurnin Aliyu inde zan jira umurnin sa to bazani ba, kulle yake min kamar matan mallam,ban ɗauka ba kuma bazan ɗauka ba yasani ,banda lokacin sa.
Taɓa baki Aisha tayi cike da mamaki take kallonta ita ta isa tafita gaba gaɗi batare da sanin Abubakar ba da ta kwana gidan su, bikin nan ma ya tubure yace baiga uban da zataje yi ba biki katsina bikin ƙanwar ƙawan ƙawa cabɗi."Azahiri ko tace,"ai da yaganki sakwa sakwa rainaki zai rinƙa yi,mazan nan in baka nuna musu kaima jan wiya ne kana da taurin kai ai sai sharan gidan ka yafika walwala. Kide bari ƙawata,ni wallahi ko ya mantawa nakeyi ina da ita, don shike mata komi, kwana biyu ma ban ganta ba ko tana gidan uwarsa ne oho, duk inda yakaita shi ya jiyo bani da asara".
Lallai lamarin Abeeda yana matuƙar ba Aisha mamaki itade duniya kawai tasa agaban ta, wani kallo Aisha ta watsa mata a zuciyarta tace yar wahala, kibiye ma matan bariƙi sunan ki bazawara wata rana,bakina ganin yana ƙaunar ki bazai iya turaki gidan ubanki ba,ni naiman haihuwar ma muke ido rufe bamu samu ba keda yake jaka ce kin samu kina wulaƙantawa,azahiri ko haƙori ta washe tace. kawata aikin ki nakyau wallahi, karki yarda ko ƙara haihuwa balle harki tsufa,atara miki yaya ,shikuma yaje ya kara aure.
Kaɗa manyan idanuwan ta Abeeda tayi kamar zasu faɗo ƙasa tace,"aure ai wallahi Aliyu bai isa ya auro wata yar iska ba, yamin alƙawari dagani babu ƙari, ke in taƙai ce miki Aliyu bai iya haɗani da kowa a zuciyar shi balle har yaji shaawan yimin kishiya, haihuwa ko bazan iya buɗe mai ƙafa ba kullum yaci kamar yasamu shinkafa, ke in taƙaice miki ancire min mahaifa,yanda bazan haihu ba kwata kwata,inci duniyata datsinke da kyau,ba wanda yasani sai ke da yau na faɗa miki don kema ƙawar arziki ce baki bani shawaran banza ".
Boye mamakin ta Aisha tayi da yacika zuciyarta lallai Abeeda ba Allah sam a gabanta,sheɗan yayi mugun buga mata gangar mu'azu tayi nisa banta jin kira a zahiri ko tace. Shegiya ƙawata aikin ki na kyau sosai. Dariya suka fashe dashi tare da tafawa. Aisha na mata kallon sakarya. Atika Atika ke Atiƙa tashi ki daukan min tallan kokon nan rana nayi. Faɗan Zarah tsaye kan Abeeda da tayi ɗaiɗaya kan gadon kara kannan tugu-tugu ba kitso, mika tayi ta mike tana gantsaro yan matasan nonon ta da suka ɓullo kamar kan gero, suma azaban taɓawan maza ne yasa suka fito,turo baki tayi tana bin Zarah da wani mugun kallo tace.
Zara kin raina min wayo da yawa,ina bacci zaki wani tasheni akan banzar kunun ki ni bazani ba ki ɗauka da kanki kije ko kijira yar iskan can Sa'ina tazo ta je miki don wallahi bazani ba. Riƙe baki tayi tanabin Atiƙa da ido harta dasa aza tace,"kaji min shegiya yar iska nizaki gayama bazakije min tallan koko ba lallai wiyan ki ya isa yanka. Wallahi Zarah ko shure shuren mutuwa kike bazani ba, zaki zubar min da aji talla Allah ya kiyaye wallahi in zaki jira Jidda ta dawo taci gaba miki ita ce bautantar ki amma bani ba,in kin matsy kije da kanki.
Tana kai aya ta mike ta shige bayi batare da ta ɗauko buta ba. Tura ƙofar suka tura a hankali suka shiga tana zaune bakin gado tayi tagumi lokaci ɗaya ya ɗuƙa guywowin sa a ƙasa ko ɗagowa ba tayi balle ta kalle su, lokaci daya suka.
PAGE 61 TO 65
Tura ƙofar suka tura a hankali suka shiga tana zaune bakin gado tayi tagumi lokaci ɗaya ya ɗuƙa guywowin sa a ƙasa ko ɗagowa ba tayi balle ta kalle su, lokaci ɗaya suka fashe da kuka lokaci ɗaya a tare, don Aliyu yasan tun yana ƙarami Ummy ta tsani kukan shi hankalin ta yanzun zai tashi ta shiga damuwa. Runtsa idon ta tayi tana jin wani abu yazo ya tokare ƙirjin ta sam batason jin sautin kukan Aliyu, lokaci ɗaya ta maida kallonta kan Aliyu da Cute da suke kuka duk sun zuba mata ido.
Ya isa haka Aliyu" ta faɗa da ƙarfi cikin ɗaga murya. Lokaci daya suka haɗe kukan su kamar haɗin baki.
NIKO NACE LALLAI UBA DA ƳAR NAN TASHI ƳAN DRAMA NE, DAMA RAƊAN DAYAI MATA A KUNNE KENAN SUNA DARIYA ASHE DRAMA SUKA HAƊA
Kasan bansan ganin hawayen ka a kasa shine zaka zo ka tasa ni gaba dakai da mai kama da kyanwar MRS BASAKKWACE da baƙaƙen idon ta kamar na ZEERO kuna min kuka, kutashi kuban waje in kuka zakuyi min kuma ka tafi da Yarka can ku ƙarata. Cikin ɗaga murya take maganan.
Cikin marai raicewa murya suka haɗa hannuwa suka ce," sorry UmmY, a taƙaice. Shiru tayi bata kalle su ba, bata kuma basu amsa ba. Cute sauka tayi ajikin Aliyu tasa guywowin ta a ƙasa ta kamo ƙafar Ummy ɗaya da yake ƙasa tace,"Ummy Dadyna bazai ƙara ba wallahi, kiyi haƙuri, kinga Dady ma yayi kuka".
Maganan taso taba Ummy dariya amma ta danne dariya tace,"tashi kiban waje ko inyi ball dake mai bakin tsuntsu kawai, nayafe masa na haƙura haɗa kayan ki kukoma gidan ku, maza tashi kikira Iya ta haɗa miki kayanki don banson takura. Kumburo baki Cute tayi kumatun ta suka ƙara cikowa kamar na LIPTON GIRL tacewa,"ni anan zan zauna Momy ta bata son. Saurin toshe mata baki Aliyu yayi yace,"mata kull yana girgiza kai,kar na ƙara ji yanada nake son ki haka Abeeda kinji. Gyaɗa kanta tayi.
Ummy ko tausayi yar jikan tata ɗaya tunƙwal take bata ace ka haifi ɗa kamar ka haifi ɗan shegw baka iya kula dashi balle kanuna masa so wannan wata irin ballagazan uwa ce. Ummy kinyi haƙuri ko faɗan Cute davata kafeta da ido.
Eh nayi badon halin ki ba da ubanki, tashi kije ki ce Iya ta baku abinci keda Auntyki JIDDA".Tashi tayi cike da farin ciki tai ma Ummy kiss a gefan kumatun ta ta fita da gudu cike da murna. Harara ta galla ma Aliyu da kan shi ke ƙasa tace," wato ka raina ni baka ɗauke ni da mutunci ba ko da matsayi shiyasa zan maka magana kasa takalmi ka shure maganata katafi lafani don baka da kunya kaje kace ma Ibrahim maine yayi haƙuri yabaka JIDDA koko to wallahi sai kabani takaddan sakin ta don ko Ibrahim bai isa ya hanani ansan takaddan sakin JIDDA a hannun kaba, don haka ka gaggauta katashi ka kawo min takaddan sakin yata JIDDA don amana uwarta tabani ita don kawai anfi ƙarfinane na haƙura".
NIKO CIKE DA MAMAKIN MAGANAN UMMIE NAKE DAMA JIDDA MATAN ALIYU NE?, TO TAYA HAKA TAFARU BAI ZAUNA DA ITA BA YA AURE ABEEDA BISA DUKKAN ALAMU ABIDA BATA SAN DA WANNAN JIƘAƘƘAN A ƘASA BA, RANDA TAJI KO AKWAU ƘURA A ƘASA.
Tunda Ummy tafara maganan saki yaji kamar tana buga masa guduma akai a razane yake kallonta yana girgiza kai. Wallahi Aliyu ko mi zai faru sai ka saki JIDDA wato kun haÉ—o baki da matar ka abaka ita kuje ku maidata boyi boyi ku bautar da ita, to bazan yarda ba aci amanar baiwar Allah ba marainiya. Cikin kakkausar murya take maganan tanayi tana murza yan yatsu.
Aliyu ko sam a zuciyar shi bai ji zai iya sakin ta,don zaman da sukayi da ita a asbiti ta shiga ransa,zai lallaɓa Ummie ta barshi da ita ko bazasu tare ba. Sosa ƙeyan shi yayi yace,"Ummy itama ya kamata a samo mata malami da zai rinƙa mata lesson ta iya karatu da rubutu kafin akaita makaranta na boko dana islamiya".
Buɗe baki Ummy tayi lallai Aliyu ya raina ta wato tana gabas yana yamma duk maganan da tayi masa bai ma shiga kunnesa ba, wani magana ya kawo mata, ƙwafa tayi ta tashi ta shiga ban ɗaki, don bama tasan mai zata kuma ce masa ba. Murmushi yayi ya tashi ya fuce. Ba kowa falon sai ƙaran AC da TV ga daining nan alaman anci abinci an tashi. Suna gama cin abinci Cute taja hanun Jidda wai suje ɗakin ta suyi wasa, hakan ko akayi JIDDA tabita bedroom ɗinta ta kwaso kayam wasan da Ummy ta sayo mata ta baje a tsakar ɗakin suka kama wasa JIDDA ko kamar saanta ta biye mata Cute sai farin ciki take.
Har ya shigo basu sani ba hankalin su ya ɗauku wajan wasa,ya jima tsaye yana kallon su yana jin wani nishaɗi daɓa Abeeda ce da bazai taɓa tinanin ƙara zama da wata mace ba. Nima nazo ayi dani faɗan Aliyu,dukkan atre suka ɗago suka zuba masa ido cike.
!
0 Comments