f Mijin Babata Ne 66 To 80

Mijin Babata Ne 66 To 80


Mijin Babata Ne 66 To 80



PAGE 66 TO 70

Nima  nazo ayi dani faɗan Aliyu, dukkan su a tare suka ɗago suka zuba masa ido, cike da mamakin yaushe ya shigo sam basuji takowar sa balan tana buɗe ƙofar sa. Idon shi cakkkkk akan JEEDAH da itama shi take kallo ido cikin ido kallon kallo suke mai juna,a hankali ta jaye idanuwan ta don lokaci ɗaya taga wasu kibiyoyi daga ƙwayan idanuwan shi suna fitowa suna shiga nata. Murmushi Cute ta sake tare da haɗa  hannayen ta tafa su waje ɗaya tace,"perfect match, Dady ka ɗauke ta mukoma gidan mu wallahi kunyi matuƙar dacewa.






Ɗan sosa ƙeyan shi yayi yana murmushi ya sa guywowin sa  ƙasa yana shafa lallausan gashin kanta yace,"Cute kin cika magana babu wani perfect match, kuci gaba da wasan ku, bari inje gida in dawo. Dady Momy  fa, kace  mata nayi missing ɗinta over one billion. Shafo kanta yayi lokacin ɗaya takaici da haushin Abeeda ya sauka a zuciyar shi, ɗan gajeran tsaki yaja can ƙasan maƙoshin sa yace," zan faɗa mata, ki kula da kanki. Ummy dai ta kula dani, ni mai zan iya ɓa kaina. Ta faɗa tana wani ƙyafta manyan idanuwan ta.

Murmushi yayi tare da sake mata peak kiss a goshi, tare da miƙewa yana satan kallon  JEDDATOU da kanta ke ƙasa kamar ruwa ya shanye ta tawutsiyar ido ya ke kallonta har yafice, sai da ya tabbatar ya fice ya kulle ƙofar ya wani jingina da jikin ƙofar ya sauke wani nauyayyan ajiyar zuciya yana runtsa idon kallon ta yake cikin ido da ɗazun suke kallon juna, murmushi ya sauke harsai da kumatun shi suka lotsa a zahiri ya furta "gaskiyan kine CUTE mun dace sosai. Jin motsi kamar wani na fitowa yasa yai saurin bin hanyar waje.







Da mamaki Ummy take kallon bayan shi dama bai fita ba, mi ya tsaya yi,lallai sai ta tsaya tsayin daka akan Aliyu game da Jiddatou sai tayi bake-bake taga yanda zai ganta har ya hure mata kunne ta soshi. Zai shiga kenan tana danno hancin motor ta waje, da baya yaja motor sa ya buga tagumi yana bin motor ta da kallo  har ta ɓace ma unguwan kafin ya samu daman shigewa da tashi motor. Halin Abeeda yadena bashi mamaki tsoro kawai yake bashi ta rikiɗe ta sauya  kamar ba Abeedan da suka soyayya ba kamar zasu lashe junan su,ko kaɗan a da bata son ɓacin ransa yanzun ko saide ya mutu ba ruwan ta da damuwar shi. Cike da tinani kala kala yai packing ya shiga ciki.

 Ɓangaran Abeeda koda tagan shi ko ɗarrr bata ji ba don bala'in haushi Aliyu ke bata,duk yabi ya  takura ma rayuwar ta, gwamma da tabi  shawaran AISHA  da yanzun kanta yayi murfi yabarta a baƙauyiya bagida jiya,dayanzun ya ɗinkira mata ciki ya barta dareno, thank God da tacire mahaifan gaba ɗaya ta huta da ɗaukan ciki,in yaso in tama son wani haihuwar  taje asa mata wani.

NI MATAR DATTIJO WACCE MIKI ANA CIRE MAHAIFA A MAYAR,LALLAI KINA RUWA GAKI GA KADA

Yauwa yar halak irin albarka yayar da aka haifa tsiya na bacci, zo ki ɗau min tallan ku! Sa'ina da yanzun shigowan ta ɗauke da jaka a kafaɗa, da alaman kwanan waje tayi,tawani katse Zarah da ganin ta yasa ta washe jajayen haƙoranta take mata maganan ɗauka talla. Kambala'i injiwa Zahra ɗaukan talla,ko kaɗan ba ajina bane, ke kika jama kanki da yanzun Jiddah na nan da ita zatayi miki, wa a birnin ma a ina take, kiyi yanda zakiyi ta dawo kici gaba da ɗaura  mata tallan, amma ga dubu uku ki raba ma almajirai, amma wallahi bazan ɗau talla ba. 








Tana magana tana girgiza jiki tana ya mutsa fuska. Sa hannu tayi a acikin jaka ta ɗebo dubu uku ta watsa ma Zarah dake tsaye buɗe da baki.

Zarah a hasale tace,"kaji min yan jaka da lalainta yaya, tallan ce bakuyi min kun gwammace kuyi ta yawo  kwararo, lungu lungu,amma dai zanyi manaji, duƙawa tayi ta kwashe kuɗin ta kalmashe shi tasa a lalita, ɗaukan roban kunun tayi ta ɗaura akai tafita.

NIKO NACE YAFI MIKI,GA RANAN JIDDA DE KIN GANI,ƳAƳAN DA KIKA HAIFA SUN GAGARE YI MIKI WACCE KIKAI MA RIƘON SAKAINAN KASHI TAFI MIKI AMFANI DASU

ASALIN LABARI

Malam Muhammad mai gemu,shine asalin kakan su Jiddatou,haifaffan ƙauyen!

PAGE 71 TO 75

ASALIN LABARI

Mallam Ibrahim Muhammad mai Gemu shine sunan cikakken sunan mahaifin su JIDDATOU, su biyune awajan iyayen su, shida wan shi Abdullahi, sun taso wajan maƙwafcin su Mallam Ibrahim, kasancewar tun suna ƙanana. Allah ya ɗauki ran iyayen su ta sanadiyan gobaran wutan da baa san dalilin tashin sa ba, kasan cewar maƙwaftakan da, da amin takan da, tafi na yanzun, ada maƙwafcin ka zaiyi yanda ya gadama da YaYanka,saɓanin wannan lokaci da kowa nashi ɗan yasani.

TO WANNAN KENAN

Mallam Ibrahim yana da mata ɗaya Zarah wacce take ɗiya ga ƙanwar mahaifiyar sa,auren ladan noma akai musu,watou na jeka ga ɗakin ka. Shekaran su shabiyar basu taɓa koda ɓatan wata ba, hakan yasa shi zuwa maƙwaftan garin su ya auro wata yarinya mai suna Aisha.








Zarah tayi bala'i tayi bore ba, amma hakan bai hana Ibrahim aure ba. Aisha tasha tsagwama da kyara a wajan Zarah, bata da sakewa sai in Ibrahim na gida, inko bayanan bautan duk duniyan nan sai tayi shi. Shekaran ta guda, sai ga ciki ya bayyana a jikinta. Zarah kamar tai hauka, ta kasa zaune ta kasa tsaye, alokacin ta fantama zuwa gidan bokaye,duk inda taje saide aci mata kuɗi ace cikin zai zube, amma shiru, maye yaci shirwa.

Wahalan duniyan nan ta ɗauko ta ɗaura mata. Inda ko ɓangaran  Ibrahim kawai takesha kamar ƙwai acikin cokali,komi yasamo Aisha,komi Aisha, ran Zarah ɓaci yakeyi kamar zata mutu,tai ta zage zage  da habaice habaice. Bayan wata tara ta haifo ɗiyarta mace, mai kama da ita, buɗan bakin Zarah ko cewa tayi taga haihuwa zataga yanda yarinya zata rayu a doran ƙasa. Aisha ko addua kawai take ma ƴarta Allah ya tsareta, Ibrahim ko komi lodowa yakeyi, jikin sa na rawa, da wanda zaiyi amfani da wanda bazaiyi amfani ba siyowa yakeyi.

Ranan suna yarinya taci sunan mahaifiyar su Hauwa'u, suke kiranta da JIDDATOU, kulawan duniya Ibrahim ya ɗowa ma wannan ya, har matan ɗan uwan shi sunzo daga birni da ɗan uwan nashi da ɗansu ɗaya Aliyu mai shekara goma, Aliyu ko yarinyar nan wuni take awajan sa, har Aisha kece masa kana son ta nabaka  ita,sai yace to Ummy na zamu tafi da ita ko. 






Ummy ta gyaɗa kai suyita dariyan yarintar sa. Zarah ko kamar ta kashe su don haushi da takaici, ta tsani matan Abdullahi, basa zama inuwa guda.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya da daɗi ba daɗi, Aisha nata rainon yarta cikin kulawa haka mahaifinta ta,bata fito da yarta tsakar gida matuƙar Zarah na nan,don cin zalinta take da gan gan. Sai da Jiddatou tashekara biyu da rabi lokacin Aisha ta yayeta, tana yawo ko ina, sai ga Zarah tafara laulayin ciki. Murna wajan Aisha kamar itace keda cikin,Ibrahim yanuna farin cikin sa, amma ba kamar cikin Jidda ba. Zarah ko andena sa riga sai ɗaurin ƙirji, tun kafin ciki yafito ake turo ciki,tsurfa kala kala, iriiri,kitifi ba wanda batayi.







Watan ta tara da kwanaki ta haifo yarta mace itama mai kama da ita, Ibrahim yayi hidima amma bakamar haihuwar Jidda ba, hakan ya ƙulal da Zarah, a tsakanin ne Aisha ta fara sabon laulayin ciki,ran Zarah yayi matuƙar baƙi. Tunda Aisha ta ɗau cikin nan yau lafiya gobe ciwo, ba mai kula da ita gashi ƴarta batavda wayon yin abubuwa haka take cijewa ta daure tayi ayukan gida harda na Zarah. Watarana ciki dare naƙuda ya taso mata, gashi Ibrahim baa ɗakinta yake ba, gashi bata isa ta je ta buga musu ba tasha zagi, tayi matuƙar galaibaita tafita hayyacinta. Jidda ko baccinta kawai take batasan maike faruwa ba. Tun Aisha na iya motsi har tazo bata iyawa.

Ko da safe tayi Zarah sai ƙwala mata kira takeyi tajita shiru ban kaɗo ƙofar da zatayi ta iske ta kwance male male cikin jini ga ɗa yafito babu mai motsi cikin su, ga Jidda nacan na bacci. Wani mugun ƙara ta sake wanda yai sanadiyan tada Jidda daga bacci a firgice, Ibrahim ya fito daga make wayi ya yarda buta yana   tambaya lafiya. Zarah ko komawa tayi ta zauna daɓas tana kurma ihu, kan kuce mi gida ya cika sa mutane. 









Hankalin Ibrahim yayi ƙololuwar tashi, take aka kaita asbiti aka tabbatar musu da rai yayi halin sa. Dawowa akayi da ita  aka kai mata sutura aka kaita gidan ta na gaskiya, bayan share zaman bakwai ƙanwar Aisha taso ta ɗauketa Ibrahim ya hana, haka Ummy taso ta ɗauketa Ibrahim da suke kira da Abba ya hana, alokacin ne suka yanke shawara da ɗan uwan shi Abdullahi da matan shi Ummy na haɗa auran Jidda da Aliyu, basu ko bar garin nan ba saida aka ɗaura aure,bada sanin Zarah ba, daga dangin Aisha sai Abba a ɗan shagon ƙofar gida sukayi cikin sirri. Ummy taso ta tafi da ita tasata makaranta amma ina Abba ya hana,yace sai in zata tare  yasata anan gaba,ai bokoko a wuta ne,miye amfanin bokon mace. Ahaka suka tafi suka barta, bada son ran Ummy ba, lokacin Aliyu yana india yana karantun shi, bai san wani wainar ake toyawa ba. Haka rayuwa taci gaba da tafiya ba daɗi ɓangaran Jidda don tun tana ƙarama ta ke amsan gasashiyar gyaɗa a hannun Zarah, bayab haihuwar Atiƙa zarah ta ƙara haihuwar Sa'ina. Ta sangarta su sosai bata son mai zai taɓa su,gashi sun rainata tun suna ƙanana suke zaginta, basa ganin girman kowa.







Ko wuni takeyi yawon talla na safe daban na rana daban na yamma daban.

Uƙuban rayuwa ba wanda bata ganshi ba. Lokacin da takai minzilin girma, ana ta tururuwan nema auran ta, amma zarah ta hana,tace ita da aure sai bayan ranta, rayuwar JIDDATU a tallatan zai ƙare. Kwatsam aka kira Abba aka sanar dashi mutuwan ɗan uwan shi tunƙwal guda ɗaya, sanadiyar haɗarin motor zuwa kaduna, wajan ɗaurin auran ɗan abokin sa, ya shiga tashin hankali, sosai na rashin ɗan uwan sa, da ƙyar ya dawo hayyacin sa, don Hajiya Asma'u tafishi jarumta da take,haka aka share zaman bakwai. Lokacin Aliyu har yagama bautan ƙasan sa yasamu aikin bank UBA, kuma sun haɗu da wata yarinya Abeeda ɗiyar ɗan babban kasuwa Manmadu Sharif mai goro, suna soyayya sosai da son junan su kamar su lashe junan su sabida ƙauna.

Ko kaɗan  bata son ɓacin ran Aliyu. Dayazo ma Ummy da buƙatan auran Abeeda, tatuna  masa da yana da wani aure fa a ƙauye in ya matanta ya tuna. Aliyu shafa ma idon shi toka yayi yanuna  baisan da wannan labarin ba,kamar sa ace yazauna da ƴar ƙauye, shi yama Abida alƙawarin bazai  mata kishiya ba,kuma bai son ɓacin ran ta. Ummy taji matuƙar baƙin cikin maganan Aliyu, amma ta danne zuciyarta tanuna mai ba komi, taje ta samu Ibrahim a ƙauye,yaji takaici, amma sanin halin ɗan yau yasa ya daure ma zuciyar sa,shiyaje yanemo ma Aliyu auran Abeeda kuma ya amso masa  auranta.








Ko sati baayi ba suka fara samun matsala da Abeeda. Abeeda kwalliyan wajene amma bata iya komi ba,bata iya ladabin kula da miji ba, shigo shigo ba zurfi tayi masa sam bai gane waye ita ba sai bayan aure, satin su uku tafara laulayin ciki, ta tada rashin mutunci sai de acire ita haihuwa ba yanzun ba,bata son ta tsufa da wuri, ga Aliyu nason haihuwa da siɗin goshi ya shawo kanta ta bar ciki, da tatashi haihuwa ko aiki ta sa akayi mata, wai ita batason wahalan naƙuda ta mutu bata gama cin duniyarta da tsinke ba ba, anko ciro mata ya mace, in Aliyu farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha, haka Ummy ranan suna taci sunan Ummy watao Nanah Asma'u, Nany aka ɗauka don kula da Nanah wanda Aliyu ke kiranta da Cute, bata samun kulawa sam wajan mahaifiya, ko arzikin nono bata samu abata saide tasha madaran yara,Nany ko sabida wulaƙancin Abeeda basa ko daɗewa suke guduwa kawo wasu da haka har Cutie ta girma tayi wayo yakaita school sam bata samun kulawa wajan Abeeda.

Abubuwan Abeeda kullum ƙara yawa yakeyi, Aliyu ganin ta yakeyi kamar mai aljanu wani lokaci,sam bata waiwayen bayanta. Tun daga lokacin da Aliyu ko yayi aure Abba yasa maka sa damuwa harta kai shi da rasa ɓarin jikin sa, jinin sa kullum hawa yakeyi, gashi babu mai temakon sa ZARAH ce ta zama mijin inko Jidda batayi talla ba baza suci ita da baban taba saide su zauna da yunwa,ZARAH da yayanta ba mai zuwa duba Abba Jidda ke hidima dashi.






Ƴayanta ko ba wanda yanzun ba'a kawo kayan nagani ina son shiba,duk da suna yawo ba ma maza  haɗin kai acikin gonaki ba komi bane a wajan su, basa ganin mutuncin kowa harda na uwar tasu, bata isa tasa a ayi ba kuma bata  ta hana ba su hanu ba.

WANNAN KENAN,ATAƘAICE,A GURGUJE

Ɓangaran Abeeda shirin zuwa katsina biki kawai akeyi.

PAGE 76 TO 80

Ɓangaran Abeeda shirin zuwa katsina biki kawai takeyi yayinda Aisha zugata kawai take tana cewa itama zataje. Bata damu da ta gaya ma Aliyu ba, ko ta kan shi bata bi, in sun haɗu a get ne zai fita zata shigo ko zai shigo zata fita. Ɓangaran Abba yana samun kulawa sosai daga wajan likitoci da Aliyu, alhamdulillahi sauƙi na samuwa, jikin shi na motsawa ta dalilin gashin ƙashin da yake samu daga ƙwararrun likitoci. Jidda zaki iya gane asbitin da Ibrahim ke kwance.






Faɗan UmmY da take zaune kan kujeru falon ta. Tana sanye cikin riga da zani mai launin purple da pink ɗinkin dogon riga ta kashe ɗaurin Aisha baban gida, wani abun sai wanda ya gani. Cute na zaune gefeta ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana sanye da wando jeans blue da riga yellow an gyara mata gashin  kanta. Jidda na zaune daga ƙasa can gefe daga ƙasa,Ummy tayi tayi ta hau saman kujera taƙiya. Girgiza kai tayi alaman aa,kafin tace,"aa Ummy so ɗaya mukaje".

Ummie ɗaukan wayarta tayi  dake gefe,don rabon Aliyu da gidan watou fushi yake da ita daga mai faɗa.Lalubo number shi tayi ta buga masa kira,ringing biyu ya ɗaga,bata amsa sallaman da yake mata illa cewa datayi kazo gida yanzun nan ina son ganin ka. Bata jira mai zaice ba ta datse wayar. Ajiyan zuciya Aliyu ya sauke mai nauyi,gaban shi na faɗi, yana tunanin mai kuma yayi. Gama haɗa takaddun dake gaban shi yayi yasa laptop ɗinshi acikin brife case ɗin shi  ya kulle ya kwashi wayar shi  da key ɗin motor shi ya fito yana rataye breif case ɗin a kafaɗan shi.

Biyawa yayi gidan abinci yasaya yanufi asibiti yakai ma Abba  yasamu jikin nasa saide ace alhamdulillah. Gaisawa sukai Abba yana ta shi masa albarka  yana amsawa  cikin jin daɗi. Ali, ina ƙanwar Jidda kace mata ina kewar ta. Faɗan Abba dake zaune tsakiyan gado ya jingina da bango.









Wani nauyi da kunya Aliyu yaji ya rufe shi,yakamata  ko ya kawo JIDDA gidan ma bai samu zuwa ba sabida abubuwa yayi mai yawa. Murmushi yayi a zahiri yace,"Abba suna gaisheka ifa da Ummy da Cutie, yau ma Ummy tace zan kawo su. Yagaya masa haka ne don bai sanmai zaice  mata.

Allah sarki ina amsa faɗan Abba. Murmushi yayi Aliyu yamiƙe yai masa sallama  yace zasu zo anjima. Kai tsaye gidan Ummy ya nufa ,a pallow ya iske su suna kallo a tashan zeeworld. Bayan yayi sallama sun amsa, ya gaida Ummy, Cute ta gaida shi kafin Jidda ta gaida shi, ya amsa cikin kulawa. Zama yayi agefe  Cute yana riƙo hannun ta, amma hankalin shi yana wajan Jidda yana wani satan kallon ta. Ummy kula da tayi da haka yasa ta tawani haɗa rai tace,"Jidda ,Cute ku tashi ku shiga ciki mangariba ta ƙarato. Bako musu tatashi jikinta asanyaye ta matso inda suke zaune ta sa hannu zata Cute na zare hannun ta jikin Aliyu  ta miƙa ma Jidda hannun ta.

Riƙe mata hannu tayi suka nufi hanyar bedroom ɗin su. Zazzare ido Aliyu yaketayi kamar yayi ƙarya. Sannu Aliyu nikake fushi dani, don nayi ma faɗa. Faɗan Ummy da take kallon sa. Murmushi yayi ya kwanto kan kafaɗan ta cikin shagwaɓa yace,"Ummy ba haka bane, ayyuka suka min yawa, wa ƴanda kwana biyu banyi ba a office, wallahi kuna raina. kwafa tayi kafin tace,"ni ɗaga ni karka karya ni, yarka ta haumin jiki kaima kazo duk so kuke ku karya ni. Murmushi yayi tare da ƙara shigewa cikin jikin ta yana kyalkyale dariya.









Ran kwashi ta buga masa akai, da sauri ya saketa yana sosa inda ta buga masa ran kwashin. Wani asibiti Ibrahim yake. Ta tambaye shi tana kafe shi da ido. Ummy yake fa. Shine baka ji zaka iya gayamin ba. Ummy dama zan kaiku anjima ku shirya. To Allah yakai mu, kaima Allah yama albarka".

In banda wulakanci taya bayan shekara goma da kuka kawo tsiyan auran ku zaku dawo kuce abaku abinku, gaskiya bazai saɓu ba bindiga a ruwa.


Post a Comment

0 Comments